Kuna Yin Shiri don Ranar Tuna da Mutuwar Yesu?
A ranar 13 ga watan Nisan na shekara ta 33, Yesu ya san cewa yini guda ne kawai ya rage kafin a kashe shi. Ya shirya zai yi Idin Ƙetarewa da abokansa, sa’an nan ya kafa wani sabon idi wato, Jibin Maraice na Ubangiji. Babu shakka, irin wannan Idin na bukatar shiri sosai. Saboda haka ya aiki Bitrus da Yohanna su yi shirye-shiryen. (Luk. 22:7-13) Tun daga lokacin, ya zama wajibi a kowace shekara Kiristoci da suke son su tuna da mutuwar Yesu su yi shirye-shirye don ranar. (Luk. 22:19) Waɗanne shirye-shirye ne ya kamata mu yi don taron Tunawa da Mutuwar Yesu da za a yi a ranar 3 ga Afrilu?
Shirin da Ya Kamata Masu Shela Su Yi:
Ku yi shiri don ku ma ku yi kamfen ɗin rarraba wa mutane takardun gayyata.
Ku rubuta jerin sunayen mutanen da za ku gayyata, kamar waɗanda kuke nazari da su da danginku da abokan makarantarku da abokan aikinku da kuma maƙwabtanku.
Ku yi karatun ayoyin Littafi Mai Tsarki da aka zaɓa don Tuna da mutuwar Yesu kuma ku yi bimbini a kansu.
Ku zo taron da wuri don ku marabci baƙi.