Ku Shirya don Ku Tuna Mutuwar Yesu da Farin Ciki
1. Lokacin Tuna da mutuwar Yesu zai ba mu wace dama ta musamman?
1 Taron Tuna da mutuwar Yesu da za a yi a ranar Talata, 26 ga watan Maris, zai ba mu damar yin farin ciki saboda abin da Allah ya yi domin mu sami ceto. (Isha. 61:10) Kasancewa da farin ciki kafin wannan ranar zai taimaka mana mu shirya da kyau. Ta yaya?
2. Mene ne yake motsa mu mu yi shiri domin lokacin Tuna da mutuwar Yesu?
2 Yin Shiri don Ranar: Jibin Maraice na Ubangiji abu mai muhimmanci ne sosai, amma yana da sauƙin yi. Duk da haka, ana bukatar shiri sosai don kada a manta da yin wasu abubuwa masu muhimmanci. (Mis. 21:5) Zai yi kyau a zaɓi lokaci da kuma wurin da ya dace don wannan taron. Ana kuma bukata a samo gurasa da ruwan anab da suka dace da za a yi amfani da su. Ana bukatar a tsabtace da kuma shirya wurin da za a yi taron. Wanda zai ba da jawabin yana bukatar ya shirya jawabinsa sosai, kuma ya kamata a bayyana wa ’yan atenda da waɗanda za su rarraba gurasa da ruwan anab aikin da za su yi. Babu shakka a yanzu, an riga an yi yawancin waɗannan shirye-shiryen. Muna yin shiri sosai a wannan lokaci na musamman don nuna godiya ga Allah saboda tanadin fansa da ya yi don mu sami ceto.—1 Bit. 1:8, 9.
3. Ta yaya za mu shirya zuciyarmu don Jibin Maraice na Ubangiji?
3 Ku Shirya Zuciyarku: Yana da kyau mu shirya zuciyarmu domin mu fahimci muhimmancin tunawa da mutuwar Yesu. (Ezra 7:10) Saboda wannan ya kamata mu keɓe lokaci domin yin karatun Littafi Mai Tsarki da aka shirya musamman don lokacin Tuna da mutuwar Yesu, sa’an nan mu yi bimbini a kan abubuwan da suka faru sa’ad da Yesu yake gab da mutuwa. Yin tunani sosai a kan yadda Yesu ya kasance da halin sadaukarwa zai sa mu yi koyi da shi.—Gal. 2:20.
4. Wanne ne cikin abubuwan da fansar Yesu ta cim ma ta fi sa ka farin ciki?
4 Mutuwar Kristi ya nuna cewa sarautar Jehobah ne ya dace da ’yan Adam. Ya ’yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. (1 Yoh. 2:2) Ya buɗe wa ’yan Adam hanyar ƙulla dangantaka mai kyau da Allah da kuma samun rai na har abada. (Kol. 1:21, 22) Yana kuma taimaka mana mu ƙarfafa ƙudurinmu na cika alkawarin da muka yi cewa za mu bauta wa Jehobah kuma za mu ci gaba da zama almajiran Kristi. (Mat. 16:24) Muna fata farin cikinku zai ƙaru yayin da kuke yin shiri don lokacin Tuna da mutuwar Yesu da ke tafe kuma kuka halarci taron!