‘Ku Riƙa Yin Wannan’ Tunawa da mutuwar Yesu da Za A Yi Ranar 5 ga Afrilu
1. Me ya sa Tunawa da mutuwar Yesu yake da muhimmanci?
1 “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Luk 22:19) Da waɗannan kalmomi ne Yesu ya umurci almajiransa su riƙa tunawa da mutuwarsa da ta fanshi mutane. Domin amfanin da ake samu daga fansar, Kiristoci sun ɗauki ranar Tunawa da mutuwar Yesu da muhimmanci fiye da kowace rana. Yayin da ranar tuna mutuwar Yesu da za a yi ranar 5 ga Afrilu tana gabatowa, yaya za mu nuna godiya ga Jehobah?—Kol. 3:15.
2. Ta yaya yin nazari da bimbini a lokacin Tunawa da mutuwar Yesu zai nuna cewa muna nuna godiya?
2 Ku Yi Shiri: Muna yin shiri idan muna da wani abu mai muhimmanci da za mu yi. Ta wurin nazarin abubuwan da suka auku a ƙarshen rayuwar Yesu a duniya da kuma yin bimbini a kansu a matsayin iyali, za mu iya shirya zukatanmu don Tunawa da mutuwar Yesu. (Ezra 7:10) Za a samu wasu jerin nassin da suka tattauna hakan a cikin kalanda da kuma Examining the Scriptures Daily.
3. Ta yaya ƙara fita wa’azi sosai za ta nuna godiyarmu ga Tunawa da mutuwar Yesu?
3 Yin Wa’azi: Za mu kuma iya nuna godiyarmu ta wajen fita yin wa’azi sosai. (Luk 6:45) Daga ranar Asabar, 17 ga Maris, za mu fita kamfen a faɗin duniya don mu gayyaci mutane su zo su Tuna mutuwar Yesu tare da mu. Zai yiwu ka daidaita ayyukanka don ka fita yin wa’azi sosai, wataƙila ma ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci? Me zai hana ku tattauna hakan a Bauta ta Iyali da yamma na gaba?
4. Waɗanne amfani ne za mu iya samu daga Tuna Mutuwar Yesu?
4 Muna amfana sosai idan muka halarci taron Tunawa da mutuwar Yesu a kowace shekara! Farin cikinmu da ƙaunar da muke yi wa Allah tana ƙaruwa sa’ad da muka yi tunani a kan karimcin da Jehobah ya nuna sa’ad da ya ba da Ɗansa makaɗaici a matsayin fansa. (Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:9, 10) Hakan zai sa kada mu yi rayuwa domin kanmu. (2 Kor. 5:14, 15) Yana kuma ƙarfafa mu mu yi yabon Jehobah a fili. (Zab. 102:19-21) Hakika, mu bayin Jehobah da muke yi masa godiya muna sa ran zuwan wannan zarafin da za mu samu na yin “shelar mutuwar Ubangiji” a lokacin Tuna mutuwar Yesu da za a yi a ranar 5 ga Afrilu.—1 Kor. 11:26.