Bari Mu Nuna Godiyarmu Za a Tuna Mutuwar Yesu a Ranar 17 ga Afrilu
1. Wane ra’ayi na marubucin zabura ne ya dace musamman a lokacin Tuna Mutuwar Yesu?
1 Domin yana godiya ga ayyukan Jehobah da yawa na jin ƙai da ceto, marubucin wannan zabura ya yi tambaya: “Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?” (Zab. 116:12) Bayin Allah a yau suna da ƙarin dalili na yin godiya. Ƙarnuka da yawa bayan an rubuta waɗannan hurarrun kalmomi, Jehobah ya ba da fansa, wadda ita ce kyauta mafi girma da ya ba wa ’yan Adam. Muna da dalili mai kyau na nuna godiya yayin da muke shirin tuna mutuwar Kristi a ranar 17 ga Afrilu.—Kol. 3:15.
2. Waɗanne dalilai muke da su na nuna godiya ga fansa?
2 Albarkar Fansa: Ana ‘gafarta zunubanmu’ ta wurin fansa. (Kol. 1:13, 14) Hakan yana taimaka mana mu bauta wa Jehobah da lamiri mai tsabta. (Ibran. 9:13, 14) Sa’ad da muke addu’a ga Jehobah, za mu ji daɗin yin magana a sake da shi. (Ibran. 4:14-16) Waɗanda suka ba da gaskiya ga fansa suna da begen rai madawwami!—Yoh. 3:16.
3. Ta yaya za mu iya nuna godiya ga Jehobah don fansa?
3 Yadda Muke Nuna Godiya: Hanya ɗaya da za mu nuna godiya sosai ita ce ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki don Tuna Mutuwar Yesu a kowacce rana da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta. Don a taimaka mana mu yi hakan, an shirya talifin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu na Turanci mai jigo “Are You Prepared for the Most Important Day of the Year?” [“Ka Yi Shiri don Rana Mafi Muhimmanci a Wannan Shekarar?”] Ta wurin yin addu’a da dukan zuciyarmu, muna iya gaya wa Jehobah cewa muna ɗaukan fansa da tamani. (1 Tas. 5:17, 18) Yin biyayya ga umurnin Yesu ta wurin halartar Tuna Mutuwar Yesu ya nuna cewa muna godiya. (1 Kor. 11:24, 25) Bugu da ƙari, za mu iya yin koyi da yadda Jehobah yake ƙaunar kowa ta gayyatar mutane da yawa yadda zai yiwu su halarta tare da mu.—Isha. 55:1-3.
4. Mene ne ya kamata ya zama ƙudurinmu?
4 Bayin Jehobah masu nuna godiya ba za su ɗauki Tuna Mutuwar Yesu a matsayin wani taro kawai ba. Taro ne da ya fi muhimmanci a shekara! Yayin da Tuna Mutuwar Yesu yake kusatowa, bari ƙudurinmu ya zama kamar na marubucin wannan zabura da ya rubuta: “Ka albarkaci Ubangiji, ya raina, Kada ka manta da dukan alheransa.”—Zab. 103:2.