Nuna Godiya Domin Kyauta Mafi Girma da Allah Ya Ba Mu
1. Me ya sa muke godiya sosai ga Jehobah?
1 A cikin “kyauta” da yawa masu kyau da Jehobah ya ba da, hadayar da Ɗansa ƙaunatacce ya yi tanadinta ita ce mafi girma. (Yaƙ. 1:17) Ta buɗe hanyar samun albarka da yawa, har da gafarta mana zunubanmu. (Afi. 1:7) Muna godiya a kowane lokaci saboda wannan. A lokacin Tuna Mutuwar Yesu, ya kamata mu ɗauki lokaci musamman don yin bimbini a kan wannan kyauta mai tamani.
2. Ta yaya za mu iya gina godiya ga fansa a cikin iyalinmu da kanmu?
2 Ka Gina Godiya: Domin ka gina godiyar iyalinka, a cikin makonnin da suka gabaci Tuna Mutuwar Yesu a ranar 30 ga Maris, zai dace ka yi amfani da lokacin Bauta ta Iyali da yamma don sake bincika batun fansa. Kuma ku karanta Littafi Mai Tsarki na musamman na Tuna Mutuwar Yesu a kowace rana a matsayin iyali. Kowannenku ya yi tunani a kan yadda fansar ta amfane shi kuma ta shafi ra’ayinsa game da Jehobah, kanka, wasu, da kuma nan gaba. Zai dace idan kuka soma koyan waƙoƙi da za a yi amfani da su a Tuna Mutuwar Yesu.—Za. 77:12.
3. Ta yaya za mu iya nuna godiyarmu?
3 Nuna Godiya: Godiya domin fansar tana motsa mu mu gaya wa wasu game da Jehobah da kuma ƙaunarsa mai girma ta wajen aiko Ɗansa. (Za. 145:2-7) A watannin Maris, Afrilu, da Mayu, wasu iyalai suna nuna godiyarsu ta wajen sa aƙalla mutum ɗaya daga cikin iyalin ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci. Idan hakan ba zai yiwu ba, za ku iya “rifta zarafi” don saka hannu sosai a hidima? (Afi. 5:16) Godiya za ta motsa mu mu taimaka wa wasu su halarci Tuna Mutuwar Yesu tare da mu. (R. Yoh. 22:17) Ku soma rubuta sunayen waɗanda kuke komawa ziyara wajensu, ɗalibanku na Littafi Mai Tsarki, danginku, abokan aiki, da kuma maƙwabta da za ku gayyata, kuma ku saka hannu sosai a kamfen na musamman na gayyatar mutane zuwa Tuna Mutuwar Yesu.
4. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin amfani da lokacin Tuna Mutuwar Yesu yadda ya dace?
4 Lokacin Tuna Mutuwar Yesu yana ba mu sababbin zarafi na nuna wa Jehobah yadda muka ɗauki kyautarsa ga ’yan Adam da tamani. Bari mu yi amfani da wannan lokacin don gina da kuma nuna godiyarmu domin fansa da kuma dukan “wadatar Kristi.”—Afi. 3:8.