Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 3/14 p. 2
  • Za Ku Bar Wannan Damar Ta Wuce Ku?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ku Bar Wannan Damar Ta Wuce Ku?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Nuna Godiya Domin Kyauta Mafi Girma da Allah Ya Ba Mu
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Bari Mu Nuna Godiyarmu Za a Tuna Mutuwar Yesu a Ranar 17 ga Afrilu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • ‘Ku Riƙa Yin Wannan’ Tunawa da mutuwar Yesu da Za A Yi Ranar 5 ga Afrilu
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • ‘Ƙaunar Almasihu Tana Bi da Mu’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 3/14 p. 2

Za Ku Bar Wannan Damar Ta Wuce Ku?

Lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu Zai Ba Mu Damar Nuna Godiya

1. Wace dama ta musamman ce taron Tuna da Mutuwar Yesu zai ba mu?

1 Taron Tuna da Mutuwar Yesu da za a yi a ranar 14 ga Afrilu zai ba mu dama ta musamman na nuna godiya ga Jehobah domin alherinsa. Labarin da ke littafin Luka 17:11-18 ya nuna cewa a gaban Jehobah da Yesu, nuna godiya yana da muhimmanci sosai. Abin baƙin ciki ne cewa a cikin waɗannan kutare goma, guda ɗaya ne kawai ya dawo ya yi godiya. Ta dalilin hadayar fansa, za a kawo ƙarshen dukan cututtuka kuma za mu rayu har abada. Hakika a lokacin za mu riƙa godiya ga Jehobah kowace rana domin waɗannan albarkatan. Amma, ta yaya za mu nuna cewa muna masu godiya sosai a makonnin gaba?

2. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da godiya don fansar Yesu?

2 Ku Koyi Kasancewa da Godiya: Yin tunani sosai a kan abin da aka yi mana zai motsa mu mu nuna godiya. Domin a taimaka mana mu kasance da godiya don fansar, an yi wani tsari na musamman na karatun Littafi Mai Tsarki don lokacin tuna da mutuwar Yesu. Za mu iya samun wannan tsarin a cikin Kalandar Shaidun Jehobah da kuma littafin nan Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana. Zai dace ku bi wannan tsarin wajen tattaunawa da iyalinku. Yin hakan zai sa mu daɗa kasancewa da godiya don fansar Yesu, kuma wannan zai sa mu yi koyi da shi.—2 Kor. 5:14, 15; 1 Yoh. 4:11.

3. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa mu masu godiya ne a lokacin tunawa da mutuwar Yesu?

3 Ku Nuna Godiya: Yana da muhimmanci mu kasance masu godiya. (Kol. 3:15) Amma, godiya hali ne da ake nunawa, kamar yadda wannan kuturun ya ƙoƙarta wajen neman Yesu don ya gode masa. Babu shakka cewa ya riƙa gaya wa mutane game da yadda aka warkar da shi, kuma ya yi hakan da farin ciki. (Luk 6:45) Bari mu nuna godiya ga Allah don hadayar fansa da ya tanada ta wajen yin wa’azi da ƙwazo a wannan lokacin kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu. Yin hidimar majagaba na ɗan lokaci wata hanya ce kuma na nuna wannan godiyar. Godiya ga Allah zai sa mu marabci baƙin da za su halarci wannan taron hannu bibbiyu, kuma mu kasance a shirye don mu amsa tambayoyinsu.

4. Me ya kamata mu yi don mu guji yin da-na-sani bayan wannan taron?

4 Shin za a sake yin wani taron Tuna da Mutuwar Yesu bayan wannan? (1 Kor. 11:26) Ba mu sani ba. Amma abin da muka sani shi ne, idan wannan ne zai zama na ƙarshe, to ba za mu sake samun irin wannan muhimmiyar dama na nuna godiya ba. Saboda haka, kada ku bar wannan damar ta wuce ku. Muna fatan cewa Jehobah, Allah mai karimci da ya tanadar mana da wannan fansar zai amshi godiya da muke nuna masa, ta furucinmu da kuma tunaninmu.—Zab. 19:14.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba