Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Nuwamba–Disamba
“Da yake Allah ne Maɗaukaki, kana ganin shi ne ke jawo dukan munanan abubuwan da ke faruwa a duniya kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Yaƙub 1:13.] Talifin da ke shafi na 14 na wannan mujallar ya bayyana dalilin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa da kuma matakin da Allah zai ɗauka don ya cire mugunta da kuma wahala.”
Awake! Disamba
“Muna ziyartar iyalai ne a unguwarku. Kowa yana son zaman lafiya a iyalinsa. Me kake tsammanin ya fi muhimmanci ga iyalai, yin ƙoƙarin guje wa gardama ne ko kuwa koyan yadda za a magance ta? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka yi la’akari da wannan karin maganar da ke Littafi Mai Tsarki. [Karanta Misalai 26:20.] Wannan mujallar tana ɗauke da wasu shawarwari na Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa iyalai su zauna lafiya.”