Ku Bi Gurbin Annabawa—Habakkuk
1. Ta yaya yanayinmu ya yi daidai da na annabi Habakkuk?
1 Yayin da muke fama da matsaloli da dama a duniyar nan, za mu ji kamar Habakkuk, sa’ad da ya tambayi Jehobah: “Don me kake nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma?” (Hab. 1:3; 2 Tim. 3:1, 13) Yin bimbini a kan abin da Habakkuk ya faɗa da kuma amincinsa zai taimaka mana mu jimre yayin da muke jiran ranar shari’ar Jehobah.—2 Bit. 3:7.
2. Ta yaya za mu nuna cewa muna da aminci a yau?
2 Ya Kasance da Aminci: Maimakon annabin ya yi sanyin gwiwa, ya kasance a faɗake da kuma ƙwazo sosai. (Hab. 2:1) Jehobah ya tabbatar wa annabin cewa Kalmarsa za ta cika a lokacin da ya ƙayyade kuma “adali ta wurin bangaskiyarsa za ya rayu.” (Hab. 2:2-4) Wace ƙarfafa ce Kiristoci da ke rayuwa a waɗannan kwanaki na ƙarshe za su samu daga waɗannan kalaman? Abin da ya fi muhimmanci ba sanin yaushe ƙarshen zai zo ba, amma kasancewa da tabbaci cewa ƙarshen zai zo. Bangaskiya tana taimaka mana mu kasance a faɗake kuma mu sa hidimar Jehobah farko a rayuwarmu.—Ibran. 10:38, 39.
3. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin farin ciki a hidimarmu ga Jehobah?
3 Ku Yi Alfahari da Jehobah: Za a gwada bangaskiyarmu a lokacin da Gog na ƙasar Magog ya kai wa mutanen Allah hari. (Ezek. 38:2, 10-12) Mutane suna shan wahala sosai a lokacin yaƙi, har da waɗanda suka ci yaƙin ma. Ana yin karancin abinci da hasarar dukiyoyi sosai a lokacin kuma hakan na sa rayuwa ta yi wuya ainun. Me ya kamata mu yi sa’ad da muka sami kanmu cikin irin wannan yanayin? Habakkuk ya kasance a shirye don mawuyacin lokacin da ke gaba, don haka ya tsai da shawarar yin farin ciki a hidimarsa ga Jehobah. (Hab. 3:16-19) Abin da zai taimaka mana mu jimre matsalolin da za su same mu a nan gaba shi ne “farin ciki na Ubangiji.”—Neh. 8:10; Ibran. 12:2.
4. Wane farin ciki ne za mu yi yanzu da kuma a nan gaba?
4 Mutanen da Jehobah ya ceci a ranar shari’a da ke tafe za su ci gaba da koyan abubuwa daga wurinsa. (Hab. 2:14) Waɗanda aka tayar daga mutuwa ma za su koya game da Jehobah. Ko a yanzu ma, zai dace mu yi amfani da kowane zarafi da muka samu don koya wa mutane game da Jehobah da kuma ayyukansa masu ban al’ajabi!—Zab. 34:1; 71:17.