DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ESTHER 1-5
Esther Ta Kāre Mutanen Allah
Esther ta nuna bangaskiya da ƙarfin hali a lokacin da take kāre mutanen Allah
- Za a iya kashe mutum idan ya je gaban sarki ba tare da izini ba. Kuma ba a gayyaci Esther ba har na tsawon kwana 30 
- Sarki Ahasuerus, wanda ake kira Xerxes na Ɗaya, mai zafin hali ne sosai. Akwai lokacin da ya sa a tsare wani mutum kashi biyu don ya koya wa wasu darasi. Kuma a lokacin da sarauniya Vashti ta yi masa rashin biyayya, ya sauƙe ta daga matsayinta 
- Esther ta gaya masa cewa ita Bayahudiya ce kuma amininsa ya yaudare shi