DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 38-42
Jehobah Yana Ba da Ƙarfi ga Masu-Kasala
40:29-31
Da taimakon iska, gaggafa za ta iya kasancewa a sama na sa’o’i da yawa ba tare da ta faɗo ƙasa ba. Da zarar an soma iska, sai gaggafar ta buɗe fukafukanta tana zagayawa kuma iska ta riƙa haurawa da ita sama. Haka za ta ci gaba da yi har ta kai inda take so
Yadda gaggafa take tashi sama ba tare da yin amfani da kuzari sosai ba ta nuna yadda muke amfani da ikon Allah wajen cim ma ayyukanmu na ibada