Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Marubucin Karin Magana 30:18, 19 ya ce “shaꞌanin tafiyar saurayi da yarinya” ya fi ganewarsa. Mene ne yake nufi?
Mutane da yawa har ma da wasu masanan Littafi Mai Tsarki, sun kasa gane abin da furucin nan yake nufi. Ga abin da aka rubuta a ayoyin gabaki ɗaya: “Akwai abu ukun da saninsu ya fi ganewata, I, har huɗu waɗanda ban sani ba. Su ne tafiyar gaggafa a sararin sama, da tafiyar maciji a kan dutse, da tafiyar jirgin ruwa a kan tsakiyar teku, da shaꞌanin tafiyar saurayi da yarinya.”—K. Mag. 30:18, 19.
A dā muna gani kamar furucin nan, “shaꞌanin tafiyar saurayi da yarinya” yana kwatanta abu ne marar kyau. Me ya sa muka ce haka? Wasu ayoyi da ke surar sun ambata munanan abubuwa da ba sa cewa “ya isa.” (K. Mag. 30:15, 16) Kuma aya 20 ta yi magana game da mace “mai zina” da tana ganin abin da ta yi ba laifi ba ne. Saboda haka, mun ɗauka cewa kamar yadda ba a iya gane ko gaggafa ta yi firiya a sararin sama, ko maciji ya yi tafiya a kan dutse, ko kuma jirgin ruwa ya yi tafiya a tsakiyar teku, haka ma mutum zai iya yin wani abu kuma babu wanda zai sani. Hakan ya sa muka ɗauka cewa furucin nan “shaꞌanin tafiyar saurayi da yarinya” yana nufin abin da bai da kyau, wato yadda wani saurayi ya ruɗi wata yarinya don su yi lalata.
Amma akwai wasu dalilan da suka sa muke ganin kamar ayoyin nan suna magana game da abu mai kyau ne. Marubucin ayoyin nan yana bayyana wasu abubuwa da suke ba shi mamaki.
Ainihin littattafan Ibrananci na Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa ayoyin nan suna magana ne game da abu mai kyau. Wani littafin da ake kiran Theological Lexicon of the Old Testament ya ce, kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “ya fi ganewata” a Karin Magana 30:18 tana nufin abu mai ban mamaki sosai, ko kuma abin da ake ganin ba zai taɓa yiwuwa ba.
Wani farfesa mai suna Crawford H. Toy da ke Jamiꞌar Harvard a Amurka ya bayyana cewa ayoyin nan ba sa nufin abu marar kyau. Ya ce: “Marubucin ayoyin nan yana ƙoƙarin ya bayyana yadda abubuwan da ya ambata suke da ban mamaki ne.”
Saboda haka, za mu iya cewa marubucin Karin Magana 30:18, 19, yana bayyana abubuwan da suke da ban mamaki, har ma sun fi ganewarmu. Kamar marubucin ayoyin nan, mu ma muna mamaki ƙwarai yadda gaggafa take firiya a sararin sama, da yadda maciji da bai da ƙafafu yake tafiya a kan dutse, da yadda jirgin ruwa yake tafiya a kan teku duk da nauyinsa, da kuma yadda saurayi da yarinya suke soma soyayya kuma su ji daɗin rayuwarsu tare.