RAYUWAR KIRISTA
Ka Ji Daɗin Yin Wa’azin Bishara
Shin yin wa’azi yana maka wuya ne? Yawancin mu za mu ce e. Me ya sa? Wataƙila don mutanen da ke yankinmu ba sa saurara ko kuma ba ma jin daɗin yin magana da baƙi. Hakika, irin waɗannan abubuwan za su iya sa mu baƙin ciki. Amma Allahnmu mai farin ciki ne kuma yana so mu riƙa yin farin ciki sa’ad da muke bauta masa. (Za 100:2; 1Ti 1:11) Me ya sa ya kamata mu riƙa jin daɗin yin wa’azi? Ga dalilai uku:
Na farko, muna gaya wa mutane albishiri. Ko da yake mutane a yau ba su da bege, za mu iya gaya musu “bishara ta alheri.” (Ish 52:7) Amma mu ma bishara game da Mulkin Allah za ta sa mu farin ciki. Kafin mu fita wa’azi, mu riƙa yin bimbini a kan albarkar da Mulkin Allah zai kawo mana a nan duniya.
Na biyu, wa’azin da muke yi yana amfanar mutane sosai. Yana sa su canja halayensu kuma su samu begen yin rayuwa har abada a duniya. (Ish 48:17, 18; Ro 1:16) Mu ɗauka cewa aikin ceto muke yi. Ko da akwai wasu da ba sa so su sami ceto, duk da haka, za mu ci gaba da neman waɗanda suke so su tsira.—Mt 10:11-14.
Na uku, wa’azin da muke yi yana ɗaukaka Jehobah. Wannan ne ya fi muhimmanci. Jehobah yana ɗaukan wa’azin da muke yi da tamani sosai. (Ish 43:10; Ibr 6:10) Ƙari ga haka, yana ba mu ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu yi aikin. Don haka, mu roƙi Jehobah ya sa mu riƙa farin ciki domin wannan halin yana ɗaya daga cikin ’ya’yan ruhu mai tsarki. (Ga 5:22) Da taimakonsa, za mu iya daina jin tsoro kuma mu yi wa’azi da gaba gaɗi. (A. M. 4:31) Hakan zai sa mu ji daɗin yin wa’azi ko da mutane suna saurara ko a’a.—Eze 3:3.
Wane irin ra’ayi ne kake so ka kasance da shi a wa’azi? Ta yaya za ka nuna cewa kana farin ciki?
KU KALLI BIDIYON NAN NAZARI DA BIMBINI ZA SU SA KA JI DAƊIN WA’AZI, BAYAN HAKA KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Ko da muna daɗewa sosai a wa’azi kowane wata, me ya sa ya kamata mu ɗauki nazarin Littafi Mai Tsarki da muhimmanci sosai?
A wace hanya ce za mu iya bin misalin Maryamu?
A wane lokaci ne kake yin bimbinin Kalmar Allah?
Mene ne yake sa ka farin ciki sa’ad da kake wa’azi?