Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 3 pp. 14-15
  • Zai Yiwu Ka More Albarkun Allah Har Abada

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zai Yiwu Ka More Albarkun Allah Har Abada
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Muꞌujizan Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ya So Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ta Annabawan Allah Ne Za Mu Koya Game da Shi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Kristi Shi Ne Ikon Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 3 pp. 14-15
Mutane daga kasashe dabam-dabam suna jin dadin rayuwa a aljanna a duniya.

“Yahweh zai ba da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuma za ta ba da amfanin gonarta.”​—ZABURA 85:12

Zai Yiwu Ka More Albarkun Allah Har Abada

Allah ya yi wa annabi Ibrahim alkawari cewa wani daga zuriyarsa zai sa “dukan ƙabilun duniya” su sami albarka. (Farawa 22:18) Wane ne Allah ya zaɓa?

Kusan shekaru 2,000 da suka shige, Allah ya ba Yesu Almasihu ikon yin mu’ujizai, kuma shi daga zuriyar annabi Ibrahim ne. Mu’ujizan nan sun nuna cewa ta wurin Almasihu ne Allah zai cika alkawarin da ya yi wa annabi Ibrahim.​—Galatiyawa 3:14.

Mu’ujizan sun kuma nuna cewa Almasihu ne wanda Allah ya zaɓa don ya yi wa dukan mutane albarka. Ƙari ga haka, abubuwan da Almasihu ya yi sun nuna irin alherin da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Ga misalin mu’ujizan da Almasihu ya yi, da suka nuna cewa yana da halayen kirki.

Almasihu mai alheri ne​—Ya warkar da marasa lafiya.

Akwai lokacin da wani kuturu ya roƙi Almasihu ya warkar da shi. Sai Yesu Almasihu ya taɓa shi kuma ya ce: “Na yarda.” Nan tāke, mutumin ya warke.​—Markus 1:​40-42.

Almasihu mai bayarwa ne​—Ya ciyar da mutanen da suke jin yunwa.

Yesu Almasihu bai ji daɗi ba da ya ga mutane suna jin yunwa. Fiye da sau ɗaya, Yesu ya yi amfani da ƙananan kifaye da burodi kaɗan, ya ciyar da dubban mutane. (Matiyu 14:​17-21; 15:​32-38) Kowa ya ci ya ƙoshi, har an sami raguwar abincin sosai. Wannan ba ƙaramin mu’ujiza ba ce!

Almasihu mai tausayi ne​—Ya tā da wani mutumin da ya mutu.

Yesu Almasihu “ya ji tausayin” wata gwauruwa da take kukan rasuwar ɗanta. Yesu ya tā da yaron don ya san gwauruwar ba ta da wanda zai kula da ita.​—Luka 7:​12-15.

DUNIYA ZA TA CIKA DA ALBARKAR ALLAH

Almasihu ya riga ya nuna cewa Allah yana da ikon yi wa dukan mutane albarka. Nan ba da daɗewa ba, Yesu Almasihu zai dawo kamar yadda ya yi alkawari. Idan ya dawo, Allah zai yi ayyukan al’ajabi a duk faɗin duniya ta wajen sa!

Yaya duniya za ta kasance sa’ad da alkawarin da Allah ya yi wa annabi Ibrahim ya cika? Waɗanda suke ƙaunar Allah kuma suna daraja shi, “za su gāji [“duniya,” NW ],” kuma za su yi ‘farin ciki cikin salama a yalwace.’ (Zabura 37:11) “Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

’Yan Adam za su yi rayuwa har abada a duniya cikin salama. Wannan ba ƙaramin gata ba ne. Don ƙarin bayani game da albarkun da Mulkin Allah zai kawo nan ba da daɗewa ba, ka shiga dandalin nan www.pr418.com/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba