Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 3 p. 13
  • Yin Alheri Zai Sa Mu Sami Albarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Alheri Zai Sa Mu Sami Albarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • GA ABIN DA NASSOSI MASU TSARKI SUKA CE
  • TA YAYA ZA MU TAIMAKA WA MUTANE?
  • Ta Yaya Za Mu Bi Halin “Basamariye Mai Kirki”?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Kana Amincewa Da Taimakon Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ta Yaya za a Magance Ƙiyayya Tsakanin Ƙabilu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 3 p. 13
Wani mutum yana nuna wa wani bako hanyar da zai bi a cikin taswira.

Zai dace ka taimaka wa mutane, ko da inda kuka fito, da addininku da shekarunku ba ɗaya ba ne

Yin Alheri Zai Sa Mu Sami Albarka

A yau mutane da yawa suna bukatar abinci da wurin kwana. Wasu kuma suna bukatar a ƙarfafa su ne kawai. Idan mun yi ƙoƙarin taimaka wa mutane, Allah zai albarkace mu.

GA ABIN DA NASSOSI MASU TSARKI SUKA CE

“Mai yi wa . . . talaka kirki, kamar ya ba Yahweh rance ne, Yahweh kuwa zai saka masa.”​—KARIN MAGANA 19:17.

TA YAYA ZA MU TAIMAKA WA MUTANE?

Yesu Almasihu ya taɓa ba da labarin wani Bayahude da ɓarayi suka yi masa dūka, kuma suka bar shi a bakin rai da mutuwa. (Luka 10:​29-37) Da wani mutumin kirki ya zo ya gan shi, sai ya taimaka masa. Mutumin ya taimaka masa duk da cewa shi ba Bayahude ba ne.

Mutumin ya yi wa wanda ɓarayi suka yi masa dūka tanadin magani da kuɗin jinya. Ƙari ga haka, ya ƙarfafa shi kuma ya taimaka masa ya fita daga yanayin da yake ciki.

Mene ne labarin nan ya koya mana? Almasihu ya nuna cewa ya kamata mu riƙa taimaka wa mutane a duk hanyar da za mu iya yin hakan. (Karin Magana 14:31) Nassosi Masu Tsarki sun ce, nan ba da daɗewa ba Allah zai kawo ƙarshen wahala da talauci. Ƙila ka ce, ‘Ta yaya Allah zai yi hakan, kuma yaushe?’ A talifi na gaba, za ka ga albarkun da za ka iya samuwa daga wurin Mahaliccinka.

“ALLAH BAI MANTA DA NI BA”!

Wani ɗan gudun hijira daga Gambiya ne ya ba da labarin

“Na isa Turai ba ni da kome; ba aiki, ba kuɗi, ba wurin kwana. Abubuwan da na koya daga Nassosi Masu Tsarki ne suka sa na yi tunanin yadda zan taimaka wa kaina, da yadda zan yi aiki tuƙuru, har ma in taimaka wa wasu maimakon in tsaya ina bara. Hakika, Allah ya taimaka min sosai!”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba