Ana gayyatar mutane zuwa taronmu a Tsibirin Cook
Gabatarwa
HASUMIYAR TSARO
Tambaya: Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da mala’iku?
Nassi: Za 103:20
Littafi: Wannan mujallar ta bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mala’iku da kuma yadda suke shafan rayuwarmu.
KU KOYAR DA GASKIYA
Tambaya: Kana ganin ilimin kimiyya ya ƙaryata Littafi Mai Tsarki ne?
Nassi: Ish 40:2
Gaskiya: Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan batun kimiyya daidai ne.
TAKARDAR GAYYATA ZUWA TARO (inv)
Littafi: Ina son in gayyace ka ka saurari wani jawabin da za a yi a Majami’ar Mulkinmu. [Ka ba da takardar gayyatar, ka nuna masa lokaci da kuma wurin da ake taron kuma ka ambata jigon jawabin da za a yi a ranar.]
Tambaya: Ka taɓa zuwa Majami’ar Mulki kuwa? [Idan da dama, ka nuna bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki?]
KA RUBUTA TAKA GABATARWA
Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.