DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZAFANIYA 1–HAGGAI 2
Ku Biɗi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa
Zep 2:2, 3
Ba yin alkawari cewa za mu bauta wa Jehobah kaɗai muke bukata mu yi ba idan muna so mu tsira a ranar fushinsa. Wajibi ne mu bi umurnin da Zafaniya ya ba Isra’ilawa.
Ku biɗi Ubangiji: Ku kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah a matsayin mutanen da ke ƙungiyarsa
Ku biɗi adalci: Ku riƙa bin ƙa’idodin Jehobah sosai
Ku biɗi tawali’u: Ku yi nufin Allah cikin sauƙin kai kuma ku amince idan ya yi muku gyara
Ta yaya zan biɗi Jehobah da adalci da kuma tawali’u sosai?