Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 3/1 pp. 9-14
  • Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Farillai na Ceto
  • Me Ya Sa “Watakila” ne a Ɓoye Mu?
  • Magabtan Allah—Su Lura!
  • Kaito ga Masu Laifi Masu Rashin Kunya!
  • Ka Ci Gaba da Neman Jehovah
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Zafaniya
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Bidi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Mutanen Jehovah Da Suka Komo Suna Yabonsa A Dukan Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 3/1 pp. 9-14

Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa

“Ku nemi Ubangiji . . . Ku nemi adalci da tawali’u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.”—ZAFANIYA 2:3.

1. Yaya yanayin ruhaniya na Yahuza lokacin da Zafaniya ya fara aikinsa na annabci?

ZAFANIYA ya fara aikinsa na annabci a lokacin masifa ne a tarihin Yahuza. Yanayin ruhaniya na al’ummar a lalace yake. Mutanen sun dogara ga firistoci na arna da masana taurari don kāriya, maimakon su dogara ga Jehovah. Bautar Ba’al, da bukukuwanta na ni’ima, sun cika ko’ina a cikin ƙasar. Shugabannai—hakimai, sarakuna, da alƙalai—suna zaluntar waɗanda ya kamata su kare. (Zafaniya 1:9; 3:3) Abin da ya sa ke nan Jehovah ya yi shawarar ya ‘miƙa hannunsa’ gāba da Yahuza da Urushalima don ya halaka su!—Zafaniya 1:4.

2. Wane bege ne da akwai ga bayin Allah masu aminci a Yahuza?

2 Duk da irin wannan mummunar yanayin, da akwai alamar bege. Yosiya, ɗan Amon ne yake sarauta. Yaro ne, amma Yosiya yana da ƙauna ta gaske ga Jehovah. Idan kuwa sabon sarkin ya mai da tsarkakkiyar bauta a Yahuza, lalle zai zama abin ƙarfafa ga mutane kalilan da suke yi wa Allah bauta da aminci! Wataƙila wasu za su motsu su bi su kuma su tsira a ranar hasalar Jehovah.

Farillai na Ceto

3, 4. Waɗanne farillai uku ne dole a cika su don a ceci mutum a “ranar hasalar Ubangiji”?

3 Za a ceci wasu kuwa a ranar hasalar Jehovah? E, muddin sun cika abubuwa uku da aka jera a Zafaniya 2:2, 3. Yayin da muke karanta waɗannan ayoyin, mu lura da waɗannan farillai na musamman. Zafaniya ya rubuta: “Kafin a zartar da umarni, kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi, kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku, kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku. Ku nemi Ubangiji, dukanku masu tawali’u na duniya, ku waɗanda ke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali’u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.”

4 Don ya samu ceto, sai mutum ya (1) nemi Jehovah, (2) nemi adalci, na (3) ya nemi tawali’u. Waɗannan farillai ya kamata su zama abin marmari gare mu a yau. Me ya sa? Saboda kamar yadda Yahuza da Urushalima suka fuskanci ranar hisabi a ƙarni na bakwai K.Z., al’umman Kiristendam—kai, dukan miyagu—suna kan hanyar gamuwa da Jehovah Allah a ranar “matsananciyar wahala” da take zuwa. (Matiyu 24:21) Duk wanda yake so a ɓoye shi a wannan lokacin dole ya tsai da shawara ta gaske yanzu. Yaya? Ta neman Jehovah, neman adalci, da kuma neman tawali’u kafin ya makara!

5. Menene ‘neman Jehovah’ ya kunsa a yau?

5 Kana iya cewa: ‘Ai ni Shaidan Jehovah ne, bawan Allah ne ni da ya keɓe kai, na yi baftisma. Ba na riga na cika waɗannan farillai ba?’ Hakika, ya ƙunshi fiye da keɓe kanmu kawai ga Jehovah. Isra’ila al’umma ce keɓaɓɓiya, amma a zamanin Zafaniya mutanen Yahuza ba su rayu daidai da keɓewarsu ba. Saboda haka, aka yasar da al’ummar. ‘Neman Jehovah’ a yau ya ƙunshi gina da kuma riƙe dangantaka da shi tare da yin tarayya da ƙungiyarsa ta duniya. Yana nufin kai ga sanin ra’ayin Allah wajen batutuwa da kuma sauraron yadda yake ji. Neman Jehovah muke yi yayin da muka yi nazarin Kalmarsa a hankali, muka yi bimbini a kanta, kuma muka yi amfani da gargaɗinta a rayuwarmu. Yayin da muke neman ja-gorar Jehovah cikin addu’a sosai da kuma bin ja-gorar ruhunsa mai tsarki, dangantakarmu da shi tana da ƙarfi kuma za su motsa mu mu bauta masa ‘da zuciya ɗaya, dukan ranmu, da dukan ƙarfinmu.’—Maimaitawar Shari’a 6:5; Galatiyawa 5:22-25; Filibiyawa 4:6, 7; Wahayin Yahaya 4:11.

6. Ta yaya za mu “nemi adalci,” kuma me ya sa wannan zai yiwu har a wannan duniya?

6 Farilla ta biyu da aka ambata a Zafaniya 2:3 ita ce a “nemi adalci.” Yawancinmu mun yi muhimman canje-canje don mu cancanci baftisma ta Kirista, amma dole ne mu ci gaba da ɗaukaka mizanan Allah na adalci a dukan rayuwarmu. Wasu da suka soma da kyau haka, sun ƙyale duniya ta lalata su. Ba shi da sauƙi a nemi adalci, domin muna kewaye da mutane da suka ɗauki lalatar jima’i, ƙarya, da wasu zunubai abubuwa ne masu kyau. Amma muradi mai ƙarfi na son faranta wa Jehovah rai zai iya fin ƙarfin kowane irin nufi na neman gamsuwar duniya ta yin ƙoƙari mu yi daidai da ita. Yahuza ta yi hasarar tagomashin Allah domin ta yi ƙoƙarin yin kwaikwayon abin da maƙwabtanta arna suke yi. Maimakon mu yi koyi da duniya, bari mu zama “masu koyi da Allah,” muna gina “sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.”—Afisawa 4:24; 5:1.

7. Ta yaya za mu “nemi tawali’u”?

7 Darasi na uku da aka yi a Zafaniya 2:3 shi ne idan muna so a ɓoye mu a ranar hasalar Jehovah, dole ne mu “nemi tawali’u.” Kowacce rana, muna haɗuwa da maza da mata da matasa da ba su iya kome ba sai rashin tawali’u. A gare su, sauƙin hali, aibi ne. Suna ɗaukan yin biyayya raunana ce ƙwarai. Masu butulci ne, masu son kai, masu son bin nasu ra’ayi kuma, suna gaskata cewa “damarsu” da abin da suke so tilas ne kowa ya amince da shi. Lallai abin baƙin ciki ne idan muka bi wasu cikin irin halayen nan! Yanzu lokaci ne na ‘neman tawali’u.’ Ta yaya? Ta sarayadda kai ga Allah, cikin tawali’u ka amince da horonsa kuma ka bi nufinsa daidai.

Me Ya Sa “Watakila” ne a Ɓoye Mu?

8. Menene aka kwatanta da aka yi amfani da kalmar nan “watakila” a Zafaniya 2:3?

8 Ku lura cewa Zafaniya 2:3 ta ce: “Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.” Me ya sa aka yi amfani da wannan kalmar “watakila” lokacin da ake magana da “masu tawali’u na duniya”? Waɗannan masu tawali’u sun riga sun ɗauki mataki mai kyau, amma ba za su buga ƙirji ba. Ba su kai ƙarshen tafarkinsu na aminci a rayuwa ba. Yana yiwuwa wasu cikinsu su faɗa cikin zunubi. Haka wannan yake a gare mu. Yesu ya ce: “Wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.” (Matiyu 24:13) Hakika, tsira a ranar hasalar Jehovah ta dangana ne a kan ci gabanmu a yin abin da ke daidai a idanunsa. Abin da ka ƙuduri aniyyar yi ke nan?

9. Waɗanne matakai masu kyau Sarki Yosiya matashi ya ɗauka?

9 Babu shakka a bin kalmomin Zafaniya, Sarki Yosiya ya motsu ya “nemi Ubangiji.” Nassosi sun ce: “A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin [Yosiya] yana yaro [wajen shekara 16] sai ya fara neman [ko kuma, “biɗan,” New International Version] Allah na kakansa Dawuda.” (2 Tarihi 34:3) Yosiya kuma ya ci gaba da ‘neman adalci,’ mun karanta: “A shekara ta goma sha biyu, [lokacin da Yosiya yake da shekara 20] sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi. Sai suka farfashe bagadai na Ba’al a gabansa.” (2 Tarihi 34:3, 4) Yosiya ya “nemi tawali’u” ma, cikin tawali’u ya aikata ya faranta wa Jehovah rai ta wajen tsarkake ƙasar daga gumaka da wasu ayyuka na addinan ƙarya. Lalle wasu masu tawali’u za su yi murna don waɗannan ayyuka!

10. Menene ya faru a Yahuza a shekara ta 607 A.Z., amma su waɗannene aka ceci?

10 Yahudawa da yawa sun komo ga Jehovah a lokacin sarautar Yosiya. Amma bayan mutuwar sarkin, yawanci suka koma ga hanyoyinsu na dā—ga ayyuka da Allah bai amince da su ba sam. Yadda Jehovah ya faɗa, Babiloniyawa suka ci Yahuza suka halaka babban birninta, Urushalima, a shekara ta 607 K.Z. Duk da haka, ba a yi hasarar kome da kome ba. An ɓoye annabi Irmiya, Ebed-melek mutumin Habasha, zuriyar Yonadab, tare da wasu masu aminci ga Allah a ranar nan ta hasalar Jehovah.—Irmiya 35:18, 19; 39:11, 12, 15-18.

Magabtan Allah—Su Lura!

11. Me ya sa kalubale ne a kasance da aminci ga Allah a yau, amma zai yi kyau magabtan mutanen Jehovah su yi la’akari da menene?

11 Yayin da muke jiran ranar hasalar Jehovah a kan wannan mugun tsarin, mukan sadu da “gwaje-gwaje iri iri.” (Yakubu 1:2) A wasu ƙasashe da suke da’awar suna daraja ’yancin addini, limamai sun yi amfani da ikonsu wajen masu mulki don su tsananta wa mutanen Allah ƙwarai. Wasu marasa ƙa’ida sun tsegunta Shaidun Jehovah, suna ce su “rukuni mai haɗari” ne. Allah yana sane da dukan ayyukansu—kuma waɗannan za su sha horo. Zai yi kyau waɗannan magabtansa su yi la’akari da abin da ya faru da irin waɗannan magabtan mutanensa a dā, kamar su Filistiyawa. Annabcin ya ce: “Za a bar Gaza ba kowa, Ashkelon za ta zama kufai, za a kori mutanen Ashdod da tsakar rana, Ekron kuwa za a tumɓuke ta.” Biranen Filistiyawa na Gaza, Ashkelon, Ashdod, da Ekron za a halaka su.—Zafaniya 2:4-7.

12. Menene ya faru da Filistiya, Mowab, da Ammon?

12 Annabcin ya ci gaba: “Na ji ba’ar da Mowab ta yi, da zagin Ammonawa, yadda suka yi wa mutanena ba’a, sun yi alwashi, cewa za su cinye ƙasarsu.” (Zafaniya 2:8) Hakika, Masar da Kush sun sha wahala a hannun magabta Babiloniyawa. Menene hukuncin Allah bisa Mowab da Ammon, al’ummai da suka fito daga Lutu, ɗan wan Ibrahim. Jehovah ya annabta: “Mowab za ta zama kamar Saduma, Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata.” Ba kamar kakaninsu ba—’ya’yan Lutu biyu, da suka tsira daga halaka ta Saduma da Gwamrata—ba za a ɓoye Mowab da Ammon masu fahariya daga hukuncin Allah ba. (Zafaniya 2:9-12; Farawa 19:16, 23-26, 36-38) A yau, ina Filistiya, ina biranen su kuma? Me kuma za a ce game da Mowab da Ammon masu fahariya a dā? Ka neme su a ko’ina, ba za ka gansu ba.

13. Waɗanne haƙe-haƙen ƙasa aka gano a Nineba?

13 A zamanin Zafaniya, Daular Assuriya tana kan ikonta. Da yake kwatanta wani sashin fadar da ya haƙa a Nineba, babban birnin Assuriya, manazarcin tarihin haƙe-haƙen ƙasa Austen Layard ya rubuta: “Silin ɗin . . . an rarraba su rabuwar dandali, an yi musu ado da furanni ko kuma da zanen sifar dabbobi. An yi amfani da haure wajen yin adon wasu, kowanne waje kusurwoyi da gine-gine masu gwanin kyau sun kewaye su. Wataƙila an lulluɓe azara da kuma dukan gefen ɗakunan su da zinariya da azurfa; da kuma katako kyawawa masu ƙamshi, aka yi amfani da su a aikin sassaƙa.” Duk da yadda aka annabta a cikin annabcin Zafaniya, za a halaka Assuriya da kuma babban birninta, Nineba, za ta zama “busasshen kufai marar amfani.”—Zafaniya 2:13.

14. Yaya annabcin Zafaniya ya cika a kan Nineba?

14 Bayan shekara 15 kawai da Zafaniya ya furta wannan annabci, aka halaka Nineba babba, aka ragargaza fadarta mai ɗaukaka. Hakika, birnin fahariyar nan aka yi rugu rugu da ita. An annabta tsananin halakarta sarai a waɗannan kalmomi: “Mujiya da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta [da ta faɗi], ga muryar kuka a taga. Ga risɓewa a bakin ƙofa.” (Zafaniya 2:14, 15) Manya-manyan gine-ginen Nineba za su zama wurin zaman bushiya da mujiya. Ba za a ji harkoki cikin titunan birninta ba kuma, ba muryar mayaƙa, da waƙe-waƙen firistoci. A wurin nan da a dā ake harka, za a ji muryar kuka ne daga taga, wataƙila kukan tsuntsu ko fiton iska. Bari dukan magabtan Allah su zo ƙarshensu kamar haka!

15. Menene za mu koya daga abin da ya faru wa Filistiya, Mowab, Ammon, da Assuriya?

15 Me za mu iya koya daga abin da ya faru da Filistiya, Mowab, Ammon, da kuma Assuriya? Wannan: Da shi ke mu bayin Jehovah ne, ba abin da za mu ji tsoronsa daga magabtanmu. Allah yana ganin abin da waɗanda suke hamayya da mutanensa suke yi. Jehovah ya aikata gaba da magabtansa a can dā, hukuncinsa zai zo bisa duniya duka a yau. Amma za a samu masu tsira—‘ƙasaitaccen taro daga kowace al’umma.’ (Wahayin Yahaya 7:9) Za ka iya kasancewa cikinsu—amma sai ka ci gaba da neman Jehovah, neman adalci, da kuma neman tawali’u.

Kaito ga Masu Laifi Masu Rashin Kunya!

16. Menene annabcin Zafaniya ya ce game da hakimai na Yahuza da shugabannan addinai, me ya sa waɗannan kalmomin sun yi daidai da Kiristendam?

16 Annabcin Zafaniya ya sake mai da hankali ga Yahuza da Urushalima. Zafaniya 3:1, 2 suka ce: “Taka ta ƙare, kai mai tayarwa, ƙazantaccen birni mai zalunci! Ba ya kasa kunne ga muryar kowa, ba ya karɓar horo. Bai dogara ga Ubangiji ba, bai kuma kusaci Allahnsa ba.” Lalle bala’i ne cewa mutanensa sun yi kunnen uwar shegu ga ƙoƙarin Jehovah ya hore su! Hakika, abin baƙin ciki ne rashin hankalin hakimai, sarakuna, da alƙalai. Zafaniya kuma ya nuna rashin amincewarsa ga rashin kunya na shugabannan addinansu, cewa: “Annabawansa sakarkari ne, maciya amana. Firistocinsa sun ƙazantar da abin da ke mai tsarki. Sun kuma keta dokoki.” (Zafaniya 3:3, 4) Kalmomin nan sun yi daidai da yanayin annabawan Kiristendam da firistoci a yau! Da rashin kunya, suka kawar da sunan Allah daga fassaran Littafi Mai Tsarki nasu kuma suna koyarwa da sun murguɗa Wanda suke da’awar wai suna bauta masa.

17. Ko mutane sun ji ko babu, me ya sa za ka ci gaba da yin shelar bishara?

17 Daidai wa daida, Jehovah ya gargaɗi mutanensa na dā game da abin da yake son ya yi. Ya aike bayinsa annabawa—cikinsu, akwai Zafaniya da Irmiya—don su motsa mutanen su tuba. Hakika, “Ubangiji . . . Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba.” Menene martanin? “Amma mugu bai san kunya ba,” in ji Zafaniya. (Zafaniya 3:5) Ana ba da irin wannan gargaɗin, a wannan lokaci. Idan kai mai shelar bishara ne, kana da hannu cikin wannan aiki na yin gargaɗi. Ka ci gaba da yin shelar bisharar babu fasawa! Ko mutane sun ji ko babu, hidimarka tana samun nasara a yadda Allah yake ɗaukanta muddin kana ci gaba da yinta cikin aminci; ba ka da dalilin kunya yayin da ka ke aikin Allah da himma.

18. Yaya Zafaniya 3:6 zai cika?

18 Zartar da hukunci na Allah ba zai ƙare da halaka Kiristendam kawai ba. Jehovah ya faɗaɗa hukuncinsa ya haɗa da dukan al’ummai: “Na datse al’umman duniya, Hasumiyansu sun lalace. Na kuma lalatar da hanyoyinsu, ba mai tafiya a kansu. An mai da biranensu kufai.” (Zafaniya 3:6) Amintattu ne kalmomin nan sosai, Jehovah ya faɗa game da halakar kamar ta riga ta auku. Menene ya faru da biranen Filistiya, Mowab, da kuma Ammon? Nineba, babban birnin Assuriya kuma fa? Halakarsu ta zama misalin gargaɗi ga al’ummai na yau. Ba a yi wa Allah ba’a.

Ka Ci Gaba da Neman Jehovah

19. Waɗanne tambayoyi masu sa tunani ya kamata mu yi?

19 A zamanin Zafaniya, hasalar Allah ta zo kan waɗannan mugaye da suke “lalatar da ayyukansu.” (Zafaniya 3:7) Haka zai faru a lokacinmu. Kana ganin tabbaci cewa ranar hasalar Jehovah ta gabato? Kana cin gaba da ‘neman Jehovah’ ta karanta Kalmarsa a kai a kai—kowacce rana? Kana ‘neman adalci’ ta yin rayuwa mai ɗabi’a mai tsabta cikin jituwa da mizanan Allah? Kana ‘neman tawali’u’ ta nuna sauƙin hali, halin biyayya ga Allah da tsarinsa don samun ceto?

20. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a talifi na ƙarshe na wannan tsarin annabcin Zafaniya?

20 Idan mun ci gaba da neman Jehovah, adalci, da tawali’u cikin aminci, za mu more albarka da yawa ko a yanzu ma—I, ko a cikin waɗannan “zamanin ƙarshe,” da ke gwada bangaskiya. (2 Timoti 3:1-5; Karin Magana 10:22) Amma za mu so mu yi tambayar nan, ‘A waɗanne hanyoyi muke samun albarka mu bayin Jehovah na zamanin yau, kuma wace albarka ta nan gaba ce annabcin Zafaniya ya kafa wa waɗanda za a ɓoye su a ranar hasalar Jehovah da ke zuwa da sauri?’

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya mutane suke ‘neman Jehovah’?

• Menene ‘neman adalci’ ya ƙunsa?

• Yaya za mu “nemi tawali’u”?

• Me ya sa ya kamata mu ci gaba da neman Jehovah, adalci, da kuma tawali’u?

[Hoto a shafi na 10]

Kana neman Jehovah ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a sosai?

[Hotuna a shafi na 13]

Domin sun ci gaba da neman Jehovah, ƙasaitaccen taro za su tsira wa ranar hasalarsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba