Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 3/1 pp. 15-20
  • Mutanen Jehovah Da Suka Komo Suna Yabonsa A Dukan Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mutanen Jehovah Da Suka Komo Suna Yabonsa A Dukan Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Harshe Mai Tsabta” don Su Wanene?
  • An Ɗaukaka Bautar Jehovah
  • Bauta ta Gaskiya Tana Nasara
  • Aikin Koyarwa Mafi Girma Cikin Tarihi
  • Ka Nemi Jehovah Kafin Ranar Hasalarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ranar Shari’a Ta Jehovah Ta Gabato!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Zafaniya
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Kana Magana Da “Harshe Mai-tsarki” Sosai?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 3/1 pp. 15-20

Mutanen Jehovah Da Suka Komo Suna Yabonsa A Dukan Duniya

“Zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta, domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji.”—ZAFANIYA 3:9.

1. Me ya sa saƙon hukunci ya cika a kan Yahuza da kuma wasu al’ummai?

LALLE saƙon hukunci masu ƙarfi ne Jehovah ya hure Zafaniya ya idar! Waɗannan saƙonnin hukunci sun cika a kan Yahuza da babban birninta, Urushalima, domin shugabannan da kuma mutanen gaba ɗaya ba su yi nufin Jehovah ba. Al’ummai na kusa, su Filistiya, Mowab, da kuma Ammon, su ma za su sha hasalar Allah. Me ya sa? Domin hamayyarsu ta zalunci na ƙarnuka da yawa da mutanen Jehovah. Abin da ya sa ke nan ma, za a halaka mai iko da duniya, Assuriya, ba za a sake kafa ta ba.

2. Su wanene ake zancensu a Zafaniya 3:8?

2 Amma dai, da akwai waɗanda suke da zuciyar kirki a Yahuza ta dā. Waɗannan suna sauraron hukuncin Allah bisa miyagu, kuma lalle sune waɗannan kalmomi sun yi zance a kansu: “Ni Ubangiji na ce, ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al’umman duniya, da mulkoki, don in kwarara musu hasalata da zafin fushina, gama zafin kishina zai ƙone dukan duniya.”—Zafaniya 3:8.

“Harshe Mai Tsabta” don Su Wanene?

3. Wane saƙon bege aka hure Zafaniya ya idar?

3 Hakika, Zafaniya ya idar da saƙon hukunci na Jehovah. Amma kuma an hure annabin ya haɗa da saƙon bege mai ban sha’awa—wanda zai yi ta’aziyya wa waɗanda suka ci gaba da aminci ga Jehovah. Kamar yadda aka rubuta a Zafaniya 3:9, Jehovah Allah ya sanar: “Sa’an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta, domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji, su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.”

4, 5. (a) Menene zai faru wa marasa adalci? (b) Su wanene za su amfana daga wannan, kuma me ya sa?

4 Akwai mutane da ba za a ba su harshe mai tsabta ba. Annabcin ya lura da su, yana cewa: “Zan fitar da masu girmankai da masu fankama daga cikinka.” (Zafaniya 3:11) Saboda haka, za a fitar da masu girman kai waɗanda suke raina dokokin Allah kuma suke aikata rashin adalci. Su wanene za su amfana daga wannan? Zafaniya 3:12, 13, suka ce: “Zan [Jehovah] kuwa bar mutane masu tawali’u, da masu ladabi a cikinka, su kuwa za su nemi mafaka a wurin Ubangiji. Waɗanda suka ragu cikin Isra’ila, ba za su aikata mugunta ba, ba kuma za su faɗi ƙarya ba, gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba. Za su yi kiwo, su kwanta, ba wanda zai tsorata su.”

5 Masu aminci da suka rage cikin Yahuza ta dā ne za su amfana. Me ya sa? Domin sun aikata cikin jituwa da kalmomin nan: “Ku nemi Ubangiji, dukanku masu tawali’u na duniya, ku waɗanda ke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali’u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.”—Zafaniya 2:3.

6. Menene ya faru a cikar farko ta annabcin Zafaniya?

6 A cikar farko na annabcin Zafaniya, Allah ya hori Yahuza marar bangaskiya ta yarda wa Mai Iko da Duniya Babila, suka ci ta kuma suka kwashe mutanenta zuwa bauta a shekara ta 607 K.Z. An ceci wasu, haɗe da annabi Irmiya, wasu sun ci gaba da aminci ga Jehovah a wajen da suke bautanci. A shekara ta 539 K.Z., Mediya da Fasiya suka ci Babila a ƙarƙashin Sarki Sairus. Bayan shekara biyu, Sairus ya ba da doka a ƙyale sauran Yahudawa su koma ƙasarsu. A kwana a tashi, aka sake gina haikali na Urushalima, sai kuma aka mayar da tsarin firistoci domin su koyar da mutane daga Doka. (Malakai 2:7) Saboda haka, Jehovah ya ba sauran da aka komar ni’ima—waɗanda suka kasance da aminci.

7, 8. Su wanene kalmomin annabci na Zafaniya 3:14-17 ke nuni, kuma me ya sa ka amsa haka?

7 Game da waɗanda za su more komawar nan, Zafaniya ya annabta: “Ki raira waƙa da ƙarfi, ye ke Sihiyona! Ki ta da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna, ki yi farin ciki, ya ke Urushalima! Ubangiji ya kawar miki da hukuncinsa, ya kuma kori abokan gābanki. Ubangiji Sarkin Isra’ila, yana a tsakiyarki, ba za ki ji tsoro ba. A wannan rana za a ce wa Urushalima, ‘Kada ki ji tsoro, ke Sihiyona, kada ki bar hannuwanki su raunana. Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.’ ”—Zafaniya 3:14-17.

8 Waɗannan kalmomi na annabci suna nuni ga sauran da aka tattara daga bautar Babila da aka mai da su ƙasar kakaninsu. Wannan a bayyane yake a Zafaniya 3:18-20, inda muka karanta: “Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi, Waɗanda ke tare da ke, wato waɗanda nawayar zaman talala ta zamar musu abin zargi. Ga shi kuwa, a wannan lokaci zan hukunta masu zaluntarki, zan kuma ceci gurgu, zan tattara korarru, zan mai da kunyarsu ta zama yabo, za su yi suna a duniya duka. A wannan lokaci zan komo da ku gida, In tattara ku wuri ɗaya. Zan sa ku yi suna, ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka, A sa’ad da na mayar muku da arzikinku, ni Ubangiji na faɗa.”

9. Ta yaya Jehovah ya yi wa kansa suna game da Yahuza?

9 Ka ji yadda al’ummai na kewaye, waɗanda magabtan mutanen Allah ne za su yi mamaki! Babila mai girma ta kwashe mazauna Yahuza zuwa bauta, ba tare da wani begen ko za su sake komowa ba. Ban da haka ma, ƙasarsu ta zama kango. Ta wurin ikon Allah, an komar da su zuwa ƙasarsu bayan shekara 70, yayin nan kuma al’ummai maƙiya suka nufa halaka. Lalle Jehovah ya yi wa kansa suna ta komar da sauran da suke da aminci! Ya sa su ‘yi suna, su sami yabo a wurin mutanen duniya duka.’ Lallai wannan komawa ta kawo yabo ga Jehovah kuma ga waɗanda suke ɗauke da sunansa!

An Ɗaukaka Bautar Jehovah

10, 11. Yaushe ne annabcin komawa na Zafaniya ta samu cikawa mai girma, kuma yaya muka san wannan?

10 Wata komawa ta kasance a ƙarni na farko na Zamaninmu, lokacin da Yesu Kristi ya tattara sauran Isra’ila zuwa ga bauta ta gaskiya. Wannan hoton abin da zai zo ne, domin cika mai girma ta komawar tana a can gaba tukuna. Annabcin Mika ya annabta: “Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, zai fi tuddai tsayi, mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.”—Mika 4:1.

11 Yaushe wannan zai faru? Kamar yadda annabcin ya ce ‘a kwanaki na ƙarshe’—hakika, a wannan “zamanin ƙarshe.” (2 Timoti 3:1) Wannan zai faru kafin wannan mugun tsarin abubuwa ya ƙare yayin da al’ummai suna kan bauta wa allolinsu na ƙarya. Mika 4:5 ta ce: “Al’ummai suna bin gumakansu.” Masu bauta ta gaskiya kuma fa? Annabcin Mika ya amsa: “Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”

12. Yaya aka ɗaukaka bauta ta gaskiya a waɗannan kwanaki na ƙarshe?

12 Saboda haka, a cikin wannan kwanaki na ƙarshe, “haikalin Ubangiji [ya] zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu.” An mayar da bautar gaskiya ta Jehovah da girma sosai, tana kafe sosai, kuma an ɗaukaka ta fiye da kowane irin addini. Yadda annabcin Mika ya annabta, “mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.” Waɗanda suke yin bauta ta gaskiya za su “bi Ubangiji Allahn[su] har abada abadin.”

13, 14. Yaushe ne wannan duniya ta shiga “kwanaki na ƙarshe,” kuma me ke faruwa tun lokacin game da bauta ta gaskiya?

13 Aukuwa da take cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ta nuna cewa wannan duniyar ta shiga ‘zamani na ƙarshe’—kwanakinta na ƙarshe—a shekara ta 1914. (Markus 13:4-10) Tarihi ya nuna cewa Jehovah ya fara tattara raguwar shafaffu masu aminci zuwa bauta ta gaskiya, waɗanda suke da begen samaniya. Tattara “ƙasaitaccen taro . . . daga kowace al’umma, da kabila, da jama’a, da harshe” ya biyo bayan wannan—su waɗanda suke da begen rayuwa har abada a duniya.—Wahayin Yahaya 7:9.

14 Tun Yaƙin Duniya na I har zuwa yau, bauta wa Jehovah da waɗanda suke ɗauke da sunansa suke yi ya ci gaba sosai a ƙarƙashin jagabancinsa. Daga dubbai kalilan bayan Yaƙin Duniya na I, yanzu masu bauta wa Jehovah sun kusan miliyan shida, da suke cikin ikilisiyoyi 91,000 a ƙasashe 235. Kowacce shekara, waɗannan masu shelar Mulki sukan bayar fiye da sa’o’i biliyan a yabon Allah a fili. A bayyane yake cewa waɗannan Shaidu na Jehovah ne suke cika kalmomin annabci na Yesu: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”—Matiyu 24:14.

15. Ta yaya Zafaniya 2:3 take cika a yanzu?

15 Zafaniya 3:17 ya lura: “Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne.” Ni’ima ta ruhaniya da bayin Jehovah suke morewa a cikin wannan kwanaki na ƙarshe ita ce albarkar samunsa ‘a tsakiyarsu’ cewa shi ne Allahnsu mai iko duka. Haka take a yau yadda ya kasance lokacin da aka komar da Yahuza na dā a shekara ta 537 K.Z. Da haka, za mu ga yadda Zafaniya 2:3 ta sami cika mai girma a lokacinmu yayin da ta ce: “Ku nemi Ubangiji, dukanku masu tawali’u na duniya.” A shekara ta 537 K.Z., “dukanku” ya haɗa da sauran Yahudawa da suka dawo daga bauta a Babila. Yanzu yana wakiltan masu tawali’u ne na dukan al’ummai cikin duniya gabaki ɗaya, waɗanda suka saurari wa’azi na Mulki na duniya duka da kuma waɗanda suka ruga zuwa ‘dutsen Haikalin Ubangiji.’

Bauta ta Gaskiya Tana Nasara

16. Mai yiwuwa yaya magabtanmu za su aikata ga ni’ima na bayin Jehovah a lokatan zamani?

16 Bayan shekara ta 537 K.Z., al’ummai da yawa da suka kewaye su sun yi mamakin yadda Allah ya komar da bayinsa zuwa ga bauta ta gaskiya a ƙasarsu. Amma maidowar kaɗan ce kawai. Kana iya tsammanin abin da wasu—har magabtan mutanen Allah ma—suke faɗa yanzu da suna ganin girma, ni’ima, da kuma ci gaba da bayin Jehovah suke yi a lokatai na zamani? Babu shakka, wasu cikin waɗannan magabta suna ji yadda Farisawa suka ji lokacin da suka ga yadda mutane suke rugawa zuwa wajen Yesu. Suka ce: “Ai, duk duniya na bayansa.”—Yahaya 12:19.

17. Menene wani marubuci ya ce game da Shaidun Jehovah, kuma wane girma ne suka gani?

17 A cikin littafinsa These Also Believe, Shehun malami Charles. S. Braden ya ce: ‘A zahiri dai, Shaidun Jehovah sun cika duniya da wa’azinsu. Da gaske za a iya cewa babu wani rukunin addini a cikin duniya da ke nuna himma da kuma naciya a yaɗa bisharar Mulkin sai dai Shaidun Jehovah. Yana yiwuwa wannan rukunin zai ci gaba da ƙaruwa.’ Gaskiyarsa kuwa! Lokacin da ya rubuta waɗannan kalmomin shekara 50 da ta shige, Shaidu 300,000 ne kawai suke wa’azi a dukan duniya. Menene zai faɗa a yau, da yake ninki 20 na adadin nan—mutane miliyan shida—suna wa’azin bishara?

18. Menene ne harshe mai tsabta, kuma su wanene Allah ya ba wa?

18 Ta annabinsa, Allah ya yi alkawari: “Sa’an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta, domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji, su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.” (Zafaniya 3:9) A cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe, Shaidun Jehovah ne suke kira bisa sunan Jehovah, da suke bauta masa cikin haɗin kai na gamin ƙauna ta ƙwarai—hakika, “da zuciya ɗaya.” Su ne waɗanda Jehovah ya ba su harshe mai tsabta. Wannan harshe mai tsabta ya haɗa da fahimi na ƙwarai da kuma gane gaskiya game da Allah da kuma nufe-nufensa. Jehovah ne kaɗai ke tanadin wannan fahimi ta wurin ruhunsa mai tsarki. (1 Korantiyawa 2:10) Ga wanene yake ba da ruhunsa? Sai kaɗai ga “masu yi masa biyayya.” (Ayyukan Manzanni 5:32) Shaidun Jehovah ne kawai suke yin biyayya ga Allah wanda Sarki ne game da kome. Abin da ya sa ke nan, sune masu samun ruhun Allah da kuma faɗin harshe mai tsabta, gaskiya game da Jehovah da kuma nufe-nufensa masu girma. Suna yin amfani da wannan harshe mai tsabta a yabon Jehovah a duniya duka da ke girma kuma ke cin gaba.

19. Yin amfani da harshe mai tsabta ya ƙunshi menene?

19 Faɗan harshe mai tsabta ba ta nufin gaskata abin da ke gaskiya ko kuma koya wa wasu kawai amma mutum ya sa halayensa su jitu da dokoki da kuma ƙa’idodin Allah. Shafaffu Kiristoci sun yi ja-gora a neman Jehovah da kuma sun yi amfani da harshe mai tsabta. Ka duba abin da aka cim ma! Ko da shafaffu sun ragu ƙasa da 8,700, kusan wasu miliyan shida suna yin koyi da bangaskiyarsu ta neman Jehovah da kuma yin amfani da harshe mai tsabta. Waɗannan ne ƙasaitaccen taro da suke ƙaruwa daga dukan al’ummai da suka ba da gaskiya a cikin hadayar fansa ta Yesu, suna yi masa tsarkakken hidima a farfajiya ta duniya na haikalin ruhaniya na Allah, waɗanda za su tsira wa “matsananciyar wahala” da za ta zo ba da jimawa ba a kan wannan duniya mara adalci.—Wahayin Yahaya 7:9, 14, 15.

20. Menene ke jiran shafaffu masu aminci da kuma waɗanda suke cikin ƙasaitaccen taro?

20 Babban garken za a shigar da su cikin sabuwar duniya mai adalci na Allah. (2 Bitrus 3:13) Yesu Kristi da 144,000 shafaffu da aka tashe su zuwa rayuwa ta samaniya su yi hidima na sarakuna da firistoci da shi za su zama sabon rukunin masu sarauta bisa duniya. (Romawa 8:16, 17; Wahayin Yahaya 7:4; 20:6) Sai waɗanda suka tsira wa matsananciyar wahalar za su yi aiki su mai da duniya aljanna kuma su ci gaba da amfani da harshe mai tsabta da Allah ya bayar. A faɗaɗawa, kalmomin nan sun cika a kansu: “Ni kaina zan koya wa mutanenki, zan kuwa ba su wadata da salama. Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki.”—Ishaya 54:13, 14.

Aikin Koyarwa Mafi Girma Cikin Tarihi

21, 22. (a) Yadda aka nuna a Ayyukan Manzanni 24:15, waɗannene za su bukaci a koya musu harshe mai tsabta? (b) Wace koyarwa da babu kamarta za a yi a duniya ƙarƙashin sarautar Mulki?

21 Wani babban rukuni da za a ba zarafi su koya harshe mai tsabta a cikin sabuwar duniyar su ne, waɗanda aka yi maganarsu a Ayyukan Manzanni 24:15, wadda ta ce: “Za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” A dā, biliyoyin mutane sun rayu kuma sun mutu ba tare da samun cikakken sanin Jehovah ba. Zai mai da musu ransu, daidai bisa ƙa’ida. Irin waɗannan da za a tashe su za su bukaci a koya musu harshe mai tsabta.

22 Lalle za ta zama gata mu sa hannu cikin babban aikin koyarwar nan! Zai zama aikin koyarwa mafi girma cikin tarihin ’yan Adam. Za a cim ma wannan duka a ƙarƙashin sarauta mai taimakawa na Kristi Yesu cikin ikon Mulki. Sakamakon haka, mutane za su ga cikar Ishaya 11:9, da ta ce: “Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji kamar yadda tekuna ke cike da ruwa.”

23. Me ya sa za ka faɗi cewa mu mutanen Jehovah muna da gata sosai?

23 Gata ce muke da ita cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe mu yi shiri game da wannan lokaci na ban sha’awa da sanin Jehovah da gaske zai cika duniya! Kuma mu ji yadda yake gata a yanzu da muke mutanen Allah, waɗanda suke ganin cikar kalmomin annabci da ke rubuce a Zafaniya 3:20! A wajen mun samu tabbacin Jehovah: “Zan sa ku yi suna, ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Annabcin Zafaniya na komowa yana da waɗanne cika?

• Yaya bauta ta gaskiya take cin gaba a waɗannan kwanaki na ƙarshe?

• Wane babban aiki za a yi a sabuwar duniya?

[Hoto a shafi na 17]

Mutanen Jehovah sun koma ƙasarsu don su sake kafa bauta ta gaskiya. Ka san ma’anar wannan a yau?

[Hotuna a shafi na 18]

Ta wajen amfani da “harshe mai tsabta,” Shaidun Jehovah suna gaya wa mutane saƙon Littafi Mai Tsarki mai ta’azantarwa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba