DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 19-20
Darussa Daga Kwatancin Fam Goma
Mene ne kwatancin yake nufi?
Babban mutumin na wakiltar Yesu
Bayin kuma suna wakiltar shafaffun Kiristoci
Kuɗin da maigidan ya ba bayinsa yana wakiltar gatan almajirantar da mutane da aka ba Kiristoci shafaffu
Wannan kwatancin yana ɗauke da gargaɗi a kan abin da zai faru da duk wani shafaffen Kirista da ya bi misalin mugun bawan. Yesu yana son mabiyansa su yi amfani da lokacinsu da ƙarfinsu, har ma da dukiyarsu don su taimaka wa mutane su zama mabiyansa.
Ta yaya zan bi misalin shafaffun Kiristoci a yadda suke taimaka wa mutane su zama mabiyan Yesu?