DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 KORINTIYAWA 1-3
Jehobah Ne Allahn da Ke “Mana Kowace Irin Ta’aziyya”
Jehobah yana amfani da ’yan’uwa a ikilisiya don ya yi mana ta’aziyya. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya ƙarfafa waɗanda suke fama da baƙin ciki?
Ta wurin saurarar su sosai sa’ad da suke magana
“Ku yi kuka tare da masu kuka.”—Ro 12:15
Ku tura musu saƙon ƙarfafawa ta waya ko imel.—w17.07 15, akwati
Ku yi addu’a tare da su da kuma a madadin su