Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Yuni p. 7
  • Ka Zabi Nishadi Mai Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Zabi Nishadi Mai Kyau
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Zabi Nishadi da Zai Faranta Ran Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Za Mu Zabi Nishadin da Ya Dace
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Yadda Za a Zabi Nishadi Mai Kyau
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Yuni p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Ka Zaɓi Nishaɗi Mai Kyau

Me ya sa ya zama dole mu zaɓi nishaɗi mai kyau? Dalilin shi ne fina-finan da muke kalla ko waƙoƙin da muke ji da dandalin da muke zuwa ko littattafan da muke karantawa ko wasan bidiyo da muke yi su ne muke tunaninsu. Abubuwan da muke yi sukan shafi halinmu. Abin baƙin ciki shi ne yawancin nishaɗin da ake da shi a yanzu sun ƙunshi abubuwan da Jehobah ya tsana. (Za 11:5; Ga 5:​19-21) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu riƙa mai da hankali ga yin abubuwan da suke girmama Jehobah.​—Fib 4:8.

KU KALLI BIDIYON NAN WANE IRIN NISHAƊI NE ZAN ZAƁA? SAI KU AMSA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

  • Wani wasan fada da ake yi a zamanin Romawa

    Ta yaya wasu wasannin da ake yi a zamanin Romawa suka yi daidai da waɗanda ake yi a zamaninmu?

  • Wani dan’uwa majagaba yana wa’azi tare da wani dan’uwa matashi a ikilisiyarsu

    Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su taimaka wa matasa su zaɓi nishaɗin da ya dace?

  • Wani soja

    Ta yaya Romawa 12:9 za ta taimaka mana sa’ad da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi?

  • Wasu ’yan’uwa matasa suna wasan kwallo

    Waɗanne irin nishaɗi masu kyau ne ake yi a yankinku?

WANE IRI NE KAKE YI?

Yawancin nishaɗi na yanzu sukan sa mutum ya riƙa kallon abubuwan da wasu suke yi, maimakon ya yi da kansa. Fina-finai da littattafai da shirye-shiryen telibijin sukan nuna ra’ayoyi da ƙwarewar wasu ne, ba naka ba. Ko da yake kallon waɗannan abubuwan ba laifi ba ne, amma mutane da yawa sun shaida cewa yin nishaɗi da kanka maimakon kallon wanda wasu suke yi yana da matuƙar amfani. Alal misali, wasu suna jin daɗin kiɗa kayan sauti ko kuma yin zane. Wasu kuma suna jin daɗin wasannin motsa jiki ko iyo ko kuma rawar gargajiya. Ko da wane irin nishaɗi muka zaɓa, mu “yi kome saboda ɗaukakar Allah.”​—1Ko 10:31.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba