DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 TASALONIKAWA 1-3
Yadda Za a Bayyana Sarkin Tawayen
2:6-12
Me Bulus yake nufi a waɗannan ayoyin?
- “Hana shi” (aya ta 6)—Da alama manzannin ne 
- “Bayyana” (aya ta 6)—Bayan mutuwar manzannin, Kiristoci ’yan ridda sun nuna munafurcinsu a fili da kuma koyarwarsu ta ƙarya 
- “Asirin ikon tawayen” (aya ta 7)—A zamanin Bulus, ba a fahimci “sarkin tawayen” ba 
- “Sarkin tawayen” (aya ta 8)—Yana nufin limaman Kiristendom 
- “Ubangiji Yesu zai . . . halaka [sarkin tawayen] . . . a ranar komowarsa” (aya ta 8)—Yesu zai bayyana a matsayin Sarki mai sarauta a sama ta wurin zartar da hukuncin Jehobah a kan Shaiɗan da duk magoya bayansa har da “sarkin tawayen” 
Ta yaya waɗannan ayoyin suka ƙarfafa ka ka yi wa’azi da ƙwazo?