Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Maris p. 7
  • “Ku Yi Tsaro”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Yi Tsaro”
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Kana Bin Gargadin Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • An Iske ‘Bawan Da Aminci’ A Lokacin Bincike!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Yadda Za a Bayyana Sarkin Tawayen Nan
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Maris p. 7
Budurwai goma da Yesu ya yi kwatanci da su

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 25

“Ku Yi Tsaro”

25:​1-12

Ko da yake kwatancin da Yesu ya yi na budurwai goma musamman ga shafaffun Kiristoci ne, amma dukan Kiristoci za su iya koyan darussa daga kwatancin. (w15 3/15 12-16) “Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.” (Mt 25:13) Shin za ka iya bayyana ma’anar kwatancin nan da Yesu ya yi?

  • Angon (aya ta 1)​—Yesu

  • Masu hikima, budurwai da suka yi shiri (aya ta 2)​—Shafaffun Kiristoci da suka yi shiri don su yi aikinsu da aminci kuma suka ci gaba da haskakawa har zuwa ƙarshe (Fib 2:15)

  • Ji murya: “Ga ango!” (aya ta 6)​—Alamar bayyanuwar Kristi

  • Budurwai marasa-azanci (aya ta 8)​—Shafaffun Kiristoci da suka fita don su marabci Angon amma ba su ci gaba da yin tsaro da kuma kasancewa da aminci ba

  • Budurwai masu hikiman sun ƙi su ba da mān su (aya ta 9)​—Bayan da aka hatimce su a ƙarshe, babu wani lokaci da ya rage don a taimaka wa shafaffun da suka daina kasancewa da aminci

  • “Ango ya zo” (aya ta 10)​—Yesu ya zo ya yi shari’a a ƙarshen ƙunci mai girma

  • Da budurwai masu hikima suka shiga wurin biki tare da angon, sai aka rufe kofar (aya ta 10)​—Yesu ya tattara shafaffunsa zuwa sama, amma shafaffu marasa aminci sun rasa gādonsu na zuwa sama

Kwatancin bai nuna cewa wasu da yawa a cikin shafaffun za su daina kasancewa da aminci kuma a zaɓi wasu su maye gurbinsu ba. A maimakon haka, gargaɗi ne cewa kowane Kirista shafaffe zai iya zaɓa ya kasance a shirye kuma ya yi tsaro ko kuma ya zaɓa ya bi mugun tafarki kuma ya daina kasancewa da aminci. Yesu ya ce: “Ku fa ku zama da shiri.” (Mt 24:44) Ko da wane irin bege muke da shi, Yesu yana son mu yi shiri sosai don mu ci gaba da kasancewa da aminci kuma mu riƙa yin tsaro.

Ta yaya zan nuna cewa ina yin tsaro?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba