DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 1 TIMOTI 1-3
Ku Yi ‘Marmarin Zama Masu Kula’ da Ikilisiya
3:1, 13
Zai fi kyau ’yan’uwa maza su soma marmarin zama masu kula da ikilisiya tun suna ƙanana. Hakan zai sa su sami isashen horo kuma su zama bayi masu hidima sa’ad da suka girma. (1Ti 3:10) Mene ne ɗan’uwa zai yi don ya nuna cewa yana marmarin zama mai kula da ikilisiya? Yana bukatar ya kasance da halayen nan:
Son taimaka wa mutane.—km 7/13 2-3 sakin layi na 2
Son ibada.—km 7/13 3 sakin layi na 3
Mai gaskiya da kuma aminci.—km 7/13 3 sakin layi na 4