RAYUWAR KIRISTA
“A Kan Waɗannan Sai Ku” Riƙa Yin Tunani
Waɗanne abubuwa ke nan? Littafin Filibiyawa 4:8 ta ce mu yi tunani a kan abin da ke na gaskiya da na ban girma da abin da yake daidai da abin da ke jawo ƙauna da abin da yake na kirki da abin da ya isa yabo. Hakan ba ya nufin Littafi Mai Tsarki ne kawai Kirista zai riƙa tunani a kai. Amma, ya kamata abubuwan da muke tunani a kan su su faranta ma Jehobah rai. Kada mu yi tunani a kan abubuwan da za su sa mu kasa yi masa biyayya.—Za 19:14.
Guje ma tunanin banza zai iya kasancewa da wuya domin mu ajizai ne. Ƙari ga haka, Shaiɗan wanda shi ne “allah na zamanin nan” yakan yi ƙoƙari don ya sa mu riƙa tunanin banza. (2Ko 4:4) Shi ne yake iko da ƙaffofin yaɗa labarai, kamar su shirye-shiryen talabijin da rediyo da intane da jaridu da kuma littattafai. Saboda haka, dole ne mu mai da hankali sosai a kan abubuwan da muke kalla ko muke saurara ko kuma karantawa. Idan ba mu yi hakan ba, Shaiɗan zai sa mu riƙa tunanin banza kuma hakan zai shafi halinmu.—Yak 1:14, 15.
KU KALLI BIDIYON NAN KU GUJI ABUBUWAN DA ZA SU SA KU ZAMA MARASA AMINCI—NISHAƊI MARAR KYAU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Mene ne ɗan’uwan yake kallo a wayarsa kuma ta yaya hakan ya shafi halinsa?
Ta yaya littafin Galatiyawa 6:7, 8 da Zabura 119:37 suka taimaka masa?