DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Bi Jehobah da Dukan Zuciyarku
Kaleb ya bi Jehobah da dukan zuciyarsa tun yana matashi (Yos 14:7, 8)
Kaleb ya dogara ga Jehobah ya taimaka masa don ya yi wani aiki mai wuya (Yos 14:10-12; w04 12/1 7 sakin layi na 2)
Jehobah ya albarkaci Kaleb don ya bauta masa da dukan zuciyarsa (Yos 14:13, 14; w06 10/1 18 sakin layi na 11)
Kaleb ya ƙara kasancewa da bangaskiya yayin da ya bi ja-gorancin Jehobah kuma ya sami albarka. Mu ma za mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da ya amsa addu’o’inmu kuma muka ga yadda yake taimaka mana.—1Yo 5:14, 15.