KA YI WA’AZI DA KWAZO
Yadda Za Mu Yi Wa’azi
Rarraba Takardar Gayyata Na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu (19 ga Maris–15 ga Afrilu)
“Muna farin cikin gayyatar ka zuwa wani taro da miliyoyin mutane za su halarta. Taron na Tunawa da Mutuwar Yesu ne.” Ka ba wa maigidan takardar gayyata ko ka tura masa ta wayarsa. “A cikin wannan takardar, akwai lokaci da kuma wurin da za a yi taron [ko kuma yadda za ka halarci taron ta na’ura]. Ban da haka, muna so mu gayyace ka zuwa wani taro na musamman da za a yi mako ɗaya kafin makon da za a yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu.”
Idan Mutumin Ya Son Wa’azin: Ka nuna [ko ka tura] masa bidiyon nan Ka Tuna da Mutuwar Yesu.
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Me ya sa Yesu ya mutu?
Haɗuwa ta Faria (1-18 ga Maris, 16-30 ga Afrilu)
Tambaya: Wane ne Yesu?
Nassi: Mt 16:16
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Me ya sa Yesu mutu?
Komawa Ziyarab
Tambaya: Me ya sa Yesu mutu?
Nassi: Mt 20:28
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Ta yaya za mu nuna godiya don fansar da Yesu ya ba da?