Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Satumba p. 5
  • Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aure da Rashin Aure.
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Satumba p. 5
Mata da miji suna wa’azi tare.

RAYUWAR KIRISTA

Aure Dangantaka Ce da Ake Yi Muddin Rai

Idan ma’auratan da suke bauta wa Jehobah suna zaman lafiya, hakan yana ɗaukaka Jehobah kuma za su yi farin ciki. (Mk 10:⁠9) Kiristocin da suke so su yi aure kuma su zauna lafiya, suna bukatar su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki wajen zaɓan waɗanda za su aura.

Zai dace mutum “ya wuce lokacin da sha’awar yin jima’i yake da ƙarfi sosai,” kafin ya soma fita zance. (1Ko 7:​36, NW) Zai dace ka yi amfani da lokacin da ba ka yi aure ba don ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma ka yi ƙoƙari ka kyautata halayenka. Hakan zai taimaka maka ka yi nasara idan ka yi aure.

Kafin ka amince da zancen aure, ya kamata ka yi tunani sosai kuma ka fahimci halin mutumin da za ka aura da kyau. (1Bi 3:4) Idan ka soma yin shakka game da wani abin da mutumin yake yi, zai dace ku tattauna batun. Idan mutum ya yi aure, bai kamata ya riƙa nuna sonkai ba, amma ya mai da hankali ga taimaka wa wanda ya aura. (Fib 2:​3, 4) Idan mutum yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kafin ya yi aure, zai yi masa sauƙi ya ci gaba da yin hakan bayan ya yi aure. Kuma hakan zai sa su zauna lafiya.

KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ZA KA YI SHIRIN YIN AURE​—KASHI NA 3: ‘KA YI LISSAFI’ SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya faru sa’ad da ’yar’uwar ta soma soyayya da Shane?

  • Mene ne ta fahimta sa’ad da suka ci gaba da soyayya?

  • Ta yaya iyayenta suka taimaka mata? Kuma wace shawara ce mai kyau ta yanke?

Ɗan’uwan da yake fita zance da wata ’yar’uwa zai iya yin tunani a kan tambayoyin nan:

Waɗanne halayen kirki ne take da su? Ta yaya take nuna cewa tana biɗan Mulkin Allah farko a rayuwarta? Tana daraja umurnan da ƙungiyarmu take bayarwa da kuma na Littafi Mai Tsarki? Tana nuna cewa ta damu da wasu mutane?

’Yar’uwar da take fita zance da wani ɗan’uwa za ta iya tunani a kan tambayoyin nan:

Waɗanne halayen kirki ne yake da su? Yana ɗaukan ibada da kuma ayyukansa na ikilisiya da muhimmanci fiye da neman kuɗi da wasanni da kuma shaƙatawa? Yana kula da iyayensa da ’yan’uwansa da kyau kuwa? Yana nuna cewa ya damu da wasu mutane?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba