RAYUWAR KIRISTA
Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Yadda Za Su Sa Allah Farin Ciki
Jehobah yana ɗaukan yara ƙanana da muhimmanci sosai. Yana lura da yadda bangaskiyarsu da ƙaunarsu a gare shi suke ƙaruwa kuma yana lura da yadda suke jimrewa. (1Sam 2:26; Lu 2:52) Ko da su yara ƙanana ne, za su iya sa Jehobah farin ciki ta halayensu masu kyau. (K. Ma 27:11) Ta wurin ƙungiyarsa, Jehobah ya tanadar da abubuwan da za su taimaka wa iyaye su koya wa yaransu su riƙa ƙaunar Jehobah da kuma yi masa biyayya.
KU KALLI BIDIYON NAN YARA, YADDA KUKE JIMREWA YANA SA JEHOBAH FARIN CIKI! SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Wane taimako ne Jehobah yake ba wa yara shekaru da yawa yanzu?
Waɗanne abubuwa ne aka yi kwanan nan don a taimaka wa iyaye?
Idan kai yaro ne ko yarinya, wane tanadi ne Jehobah ya yi da ya amfane ka, kuma me ya sa?