Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp22 Na 1 p. 3
  • Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Gabatarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Lokacin da Za A Daina Kiyayya Kwata-kwata!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Kiyayya Tana a Ko’ina a Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
wp22 Na 1 p. 3
Hotuna: Wani mutum yana bakin ciki don kiyayyar da ake nuna masa. 1. Wata mata rike da waya ta ki jininsa. 2. Wata mata kuma tana masa kallon banza. 3. Wani mutumin da ke karanta jarida ya bi ya kyamace shi. 4. Wani yana karanta labarai a talabijin.

Zai Yiwu Mu Daina Nuna Ƙiyayya!

An taɓa nuna maka ƙiyayya?

Ko ba a taɓa ƙin ka ba, ba mamaki ka taɓa ganin ana ƙin mutane. Mun saba jin labaran mutane da aka ƙi jininsu don ƙasarsu, ko ƙabilarsu, da dai sauransu. Shi ya sa a wasu wurare, gwamnati take kafa dokoki don a hukunta duk wanda ya cutar da mutum sakamakon irin wannan ƙiyayyar.

A yawancin lokaci, mutane suna ƙin waɗanda suke ƙinsu. Idan aka cuce su, sukan rama. Da haka sai ka ga mutane sun ci gaba da ƙin juna kuma suna cutar da junansu.

Ƙila kai ma an taɓa nuna maka bambanci, ko an ƙi jininka, ko an yi maka dariya, ko an zage ka, ko kuma an yi maka barazana. Ban da haka, ƙiyayya takan sa mutane su aikata mugunta iri-iri. Alal misali, ƙiyayya takan sa a zalunci mutane, a kai musu hari ko a yi musu ɓarna, ko a yi wa mutum fyaɗe, ko a kashe shi, har ma a shiga kisan ƙāre dangi.

Wannan mujallar za ta bayyana yadda za a daina nuna ƙiyayya. Kuma za ta ba da amsar tambayoyin nan:

  • Me ya sa ƙiyayya ta yi yawa haka?

  • Me mutum zai yi don ya daina nuna ƙiyayya?

  • Shin lokaci na zuwa da ba za a sake nuna ƙiyayya ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba