Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp22 Na 1 pp. 8-9
  • 2 | Kar Ka Rama da Mugunta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2 | Kar Ka Rama da Mugunta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
  • Abin da Ayar Take Nufi:
  • Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Ramako?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Sa’ad da Aka Yi Maka Laifi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
wp22 Na 1 pp. 8-9
Wasu mutane biyu masu fushi zaune kan reshe dabam-dabam na wani itace. Kowannensu yana yanka reshen da yake zaune a kai.

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

2 | Kar Ka Rama Da Mugunta

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Idan wani ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta . . . Ku yi iyakar ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. Kada ku zama masu ramuwa . . . Don kuwa a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, ‘Ramuwa tawa ce, ni kuwa zan rama, in ji Ubangiji.’”​—ROMAWA 12:​17-19.

Abin da Ayar Take Nufi:

Ba laifi ba ne mu yi fushi idan wani ya mana laifi, amma Allah ba ya so mu rama. Ya ce mu yi haƙuri domin nan ba da daɗewa ba, zai gyara kome.​—Zabura 37:​7, 10.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

Idan mutane suka rama mugunta da mugunta, yakan sa su ƙara tsanan junansu. Don haka, idan an maka laifi ko an cutar da kai, kada ka rama. Ka yi iya ƙoƙari ka kame kanka don kar ka ta da hankali. Wani lokaci gwamma ka yi kamar ba abin da ya faru. (Karin Magana 19:11) A wasu lokuta kuma, za ka iya kai ƙarar mutumin a wurin hukuma. Alal misali, idan aka maka ɓarna ko wani laifi da hukuma za su iya riƙe mutumin da shi, za ka iya kai ƙararsa.

Idan aka yi maka abu kuma ka rama, kanka kake cuta

Amma idan babu yadda za ka warware matsalar cikin kwanciyar hankali kuma fa? Ko kuma idan ka yi duk iya ƙoƙarinka ka magance matsalar amma ba ka yi nasara ba fa? Kada ka rama da mugunta. Domin idan ka rama, ba mamaki abin zai ƙara yin muni. Kar ka rama, don ka kawo ƙarshen ƙiyayyar da ke tsakaninku. Ka bar kome a hannun Allah. “Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.”​—Zabura 37:​3-5, Littafi Mai Tsarki.

Labarin Wani Mutum​—ADRIÁN

Ya Daina Rama Mugunta da Mugunta

Adrián.

A lokacin da Adrián yake matashi, zuciyarsa tana cike da ƙiyayya. Yana son yin faɗa kuma duk wanda ya tsokane shi, sai ya rama. Adrián ya ce: “Sau da yawa, ina faɗa da bindiga kuma a raunata ni sosai har a yar da ni kan titi ana zaton na mutu.”

Da Adrián ya kai shekara 16, sai ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Adrián ya ce: “Da na ci gaba da koyon Littafi Mai Tsarki, na fahimci cewa ina bukata in yi wasu canje-canje a halina.” Ya ga cewa ya kamata ya daina ƙin mutane kuma ya daina yin faɗa. Wata ayar da ta shiga zuciyarsa sosai, ita ce Romawa 12:​17-19 da ta ce kada mu yi ramuwa. Ya ce: “Na yarda cewa Jehobah zai magance rashin adalci a lokacin da ya ayana. Kuma a hankali a hankali, na daina yin faɗa.”

Wata rana da yamma, sai wasu matasa da suka saba faɗa da Adrián suka kawo masa hari. Sai shugabansu ya ɗaga murya ya ce idan ya isa ya zo su yi faɗa! Adrián ya ce: “Na ji haushi kuma na so in rama.” Amma Adrián bai rama ba, a maimakon haka, ya roƙi Allah ya taimake shi kuma ya tashi ya bar wurin.

Adrián ya ci-gaba da cewa: “Washegari, sai na sake haɗuwa da shugabansu shi kaɗai, na ji fushi sosai amma na sake yin addu’a ga Jehobah ya taimake ni in kame kaina. Abin mamaki, sai shugaban nasu ya zo ya same ni ya ce: ‘Ka gafarce ni da abin da na yi jiya. A gaskiya ni ma ina so in zama kamar kai kuma ina son in yi binciken Littafi Mai Tsarki.’ Na yi farin ciki cewa na iya kame kaina kuma daga baya, sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.”

Za ka iya karanta cikakken labarin Adrián a Hasumiyar Tsaro Na 5 2016, shafi na 14-15, akwai shi a dandalin jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba