Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp22 Na 1 pp. 10-11
  • 3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
  • Abin da Ayar Take Nufi:
  • Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
  • An Jejjefi Istafanus
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
wp22 Na 1 pp. 10-11
Wani mutum yana tunanin cewa shi da wani da kabilarsu ba daya ba suna shan hannu. Inuwarsu kuma ta nuna yadda suke zanga-zanga kuma suna gardama da juna a dā.

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

3 | Ka Cire Ƙiyayya Daga Zuciyarka

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.”​—ROMAWA 12:2.

Abin da Ayar Take Nufi:

Irin tunani da muke yi yana da muhimmanci a wurin Allah. (Irmiya 17:10) Kuma ƙiyayya takan soma a tunanin zuciyar mutum ne, kafin ma ya faɗi wani abu ko ya aikata shi. Saboda haka, idan muna so mu daina ƙin mutane, dole mu daina tunanin abubuwa da za su sa mu ƙi su. Abin da zai sa mu “canja” ke nan.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

Ka bincika irin abubuwan da kake tunani a kai da kuma yadda kake ganin mutane, musamman waɗanda ƙasarsu ko ƙabilarsu ba ɗaya ba ne da naka. Ka tambayi kanka: ‘Yaya nake ganinsu? Abin da na sani game da su ne ya sa nake da wannan ra’ayin? Ko na ƙi jininsu ne kawai don sun bambanta da ni?’ Ka guji kallon bidiyoyi ko karanta duk wani bayani da ake yi da ke zuga mutane su nuna ƙiyayya ko su yi mugunta. Har da waɗanda ake yaɗawa ta dandalin sada zumunta.

Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu cire ƙiyayya daga tunanin zuciyarmu

Bai da sauki mutum ya bincika kansa ya san ko tunaninsa da yadda yake ji a ransa ya dace ko bai dace ba. Amma Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu “gane duk tunani da nufin da suke cikin zuciya.” (Ibraniyawa 4:12) Don haka, ka ci gaba da yin binciken Littafi Mai Tsarki don ka ga ko tunaninka ya jitu da abin da ya ce. Idan ka ga cewa tunanin da kake yi bai dace ba, ka yi iya ƙoƙarinka ka yi gyara. Maganar Allah za ta iya taimaka mana mu daina ƙin mutane ko da ƙiyayyar ta yi “ƙarfi” a zukatanmu.​—2 Korintiyawa 10:​4, 5.

STEPHEN

Ya Cire Ƙiyayya Daga Zuciyarsa

Stephen.

Stephen da wasu ’yan gidansu sun sha wuya sosai a hannun turawa. Don haka, ya shiga wani rukunin ’yan adawa da suke yaƙi don su kwato wa mutane hakkinsu. A kwana a tashi, sai shi kansa ya shiga nuna ƙiyayya. Stephen ya ce: “Akwai lokacin da muka kalli wani fim da ya nuna yadda ’yan Amirka suke wulakanta ’yan Afirka a dā. Da muka ji haushi, sai muka yi wa turawan da ke gidan siliman dūkan tsiya. Bayan haka, sai muka shiga unguwoyi muna neman turawa za mu yi musu dūka.”

Da Stephen ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, nan da nan sai ra’ayinsa ya canja. Ya ce: “Da yake na saba gani ana nuna wariya, na yi mamaki sosai sa’ad da na lura cewa halin Shaidun Jehobah dabam ne. Alal misali, akwai lokacin da wani bature ya yi tafiya kuma ya bar yaransa a hannun wani baƙin fata don ya kula da su. Ban da wannan ma, na ga wani iyalin turawa sun ce ma wani matashi baƙin fata da ke neman gida ya zo ya zauna da su.” Hakan ya tabbatar wa Stephen cewa Shaidun Jehobah suna nuna wa juna irin ƙaunar da Yesu ya ce almajiransa na gaske za su nuna.​—Yohanna 13:35.

Me ya taimaka wa Stephen shi ma ya daina nuna ƙiyayya da yin faɗa? Abin da ke Romawa 12:2 ne ya taimaka masa. Stephen ya ce: “Na fahimci cewa ya kamata in canja ra’ayina. Na yi ƙoƙari sosai in canja halina don in yi zaman lafiya da mutane, kuma na tabbata cewa wannan ita ce hanyar da ta dace.” Yanzu Stephen ya yi shekaru 40 ba ya nuna wa mutane ƙiyayya.

Za ka iya karanta cikakken labarin Stephen a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuli, 2015, shafi na 10-11, akwai shi a dandalin jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba