Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp23 Na 1 pp. 6-7
  • 1 | Adduꞌa​—“Ku Danka Masa Dukan Damuwarku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1 | Adduꞌa​—“Ku Danka Masa Dukan Damuwarku”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Hakan Yake Nufi
  • Yadda Yin Hakan Zai Taimaka
  • Ku Gaya wa Jehobah Damuwarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka wa Maza da Suke Yawan Damuwa
    Karin Batutuwa
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Yadda Za Ka Sami Salama Kuma Ka Yi Farin Ciki In Kana Cikin Damuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
wp23 Na 1 pp. 6-7
Wani mutum da ke bakin ciki ya saka hannu a kirjinsa saꞌad da yake adduꞌa.

1 | Adduꞌa—“Ku Danƙa Masa Dukan Damuwarku”

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ku danƙa masa dukan damuwarku, gama shi ne mai lura da ku.”​—1 BITRUS 5:7.

Abin da Hakan Yake Nufi

Jehobah ya ce mu gaya masa duk abin da yake damunmu. (Zabura 55:22) Babu matsalar da ba za mu iya yin adduꞌa a kai ba. Idan abin da yake damunmu yana da muhimmanci a gare mu, Jehobah zai ɗauke shi da muhimmanci. Yin adduꞌa zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar hankali.​—Filibiyawa 4:​6, 7.

Yadda Yin Hakan Zai Taimaka

Idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa, za mu ji kamar mun kaɗaita. Ba kowane lokaci ne mutane suke fahimtar yanayin da muke ciki ba. (Karin Magana 14:10) Amma idan muka yi adduꞌa kuma muka gaya wa Jehobah yadda muke ji, zai tausaya mana kuma ya san abin da muke fama da shi. Jehobah yana ganin duk famar da muke yi kuma ya san dukan damuwarmu, yana so mu yi adduꞌa mu gaya masa duk abin da yake damunmu.​—2 Tarihi 6:​29, 30.

Idan mun gaya wa Jehobah abin da ke damunmu, hakan yana sa mu kasance da tabbaci cewa ya damu da mu. Idan muka yi haka, mu ma za mu ji kamar wani marubucin Zabura da ya yi adduꞌa cewa: “Ka ga wahalata, ka san damuwar zuciyata.” (Zabura 31:7) Sanin cewa Jehobah yana ganin abubuwan da muke fama da su, zai taimaka mana mu jimre yanayoyi masu wuya. Amma ba ganin matsalolin kawai yake yi ba. Babu wanda ya kai Jehobah fahimtar abin da muke ciki kuma zai taimaka mana mu sami ƙarfafar da muke bukata daga Littafi Mai Tsarki.

Yadda Littafi Mai Tsarki Yake Taimakawa Julian

Yadda Cutar Tsananin Damuwa Ta Shafe Ni

Julian.

“Na yi fama da cutar tsananin damuwa da na raɗaɗi wato, cutar da take sa mutum ya riƙa yin abu ɗaya a kai a kai da ake kira OCD. Cutar tsananin damuwa tana kama ni a lokutan da ban tsammani ba. Wani lokaci ina nan kalau ba matsala, amma kafin ka ankara, na soma yawan damuwa ba gaira ba dalili. Ina yawan damuwa idan ina tare da mutane. Ina yawan damuwa a kan yadda suke gani na.

“Abokaina da suka san abin da nake ciki sun yi ƙoƙari sosai wajen taimaka min. A wasu lokuta sukan faɗi abin da ba na so in ji. Amma ina godiya don yadda suke so su taimaka min.

“A wasu lokuta, cutar tsananin damuwa da kuma na raɗaɗi suna sa ya yi min wuya in yi adduꞌa. Yakan yi min wuya sosai in mai da hankali in yi adduꞌa ga Jehobah. Nakan yi tunani a kan abubuwa da dama a lokaci guda kuma hakan yakan ruɗar da ni. Idan na rikice, yakan mini wuya in bayyana wa Jehobah yadda nake ji da kuma tunanin da nake yi.”

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Taimaka Min

“Na koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi cewa ba sai adduꞌar mutum ta yi tsayi ko ya tsara maganarsa ba ne Allah yake amsa adduꞌar ba. A wasu lokutan da ba zan iya gaya wa Jehobah yadda nake ji ba, nakan yi adduꞌa cewa: ‘Jehobah, ka taimaka min.’ Ko a irin wannan yanayin Jehobah yakan fahimce ni kuma yakan ba ni abin da nake bukata a wannan lokacin. Ban da adduꞌoꞌin da nake yi, na je asibiti neman taimako. Ina farin ciki cewa yanayi na ya gyaru don waɗannan abubuwan da suka taimaka min. Ko da yake yana min wuya in nemi taimako daga wurin Ubanmu na sama, ina yin hakan don na san yana ƙaunata kuma yana so ya taimaka min.”

Taimako don Matasa

Bidiyon nan “Ka Zama Abokin Jehobah​—Ka Yi Addu’a a Kowane Lokaci.”

A dandalin jw.org, za ka ga dalilin da zai sa ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ji kuma ya amsa adduꞌoꞌinka.

Ka duba bidiyon nan, Ka Zama Abokin Jehobah​—Ka Yi Addu’a a Kowane Lokaci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba