2 | Ƙarfafa Daga Kalmar Allah
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Duk abin da aka rubuta tun dā a cikin Rubutacciyar Maganar Allah an rubuta ne domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya ta wurin jimrewa da ƙarfafawa waɗanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.”—ROMAWA 15:4.
Abin da Hakan Yake Nufi
A cikin Littafi Mai Tsarki za mu sami abubuwan da za su ƙarfafa mu idan muna yawan tunani da bai kamata ba. Saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege cewa abin da ke sa mu baƙin ciki ba za su ƙara kasancewa ba.
Yadda Yin Hakan Zai Taimaka
Dukanmu mukan yi baƙin ciki a wasu lokuta, amma waɗanda suke ciwon baƙin ciki ko tsananin damuwa suna iya yin fama da wannan abu a kowace rana. Amma ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana?
Akwai abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa mu kuma su sa mu daina baƙin ciki. (Filibiyawa 4:8) Za su sa mu kasance da kwanciyar hankali kuma za su taimaka mana mu kame kanmu.—Zabura 94:18, 19.
Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu kawar da raꞌayi cewa ba mu da amfani.—Luka 12:6, 7.
Ayoyi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki sun tabbatar mana cewa Allah Mahaliccinmu yana tare da mu kuma ya fahimci yadda muke ji.—Zabura 34:18; 1 Yohanna 3:19, 20.
Littafi Mai Tsarki ya yi mana alkawari cewa Allah zai kawar da dukan abubuwan da suka faru da mu da suke sa mu baƙin ciki. (Ishaya 65:17; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4) Saꞌad da muke fama da waɗannan abubuwan, alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki za su ƙarfafa mu mu jimre.