Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp23 Na 1 pp. 10-11
  • 3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Hakan Yake Nufi
  • Yadda Yin Hakan Zai Taimaka
  • 2 | “Karfafa Daga Kalmar Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • 4 | Za Mu Sami Shawara Mai Kyau a Cikin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
  • Idan Ina da Wata Cuta Fa? (Sashe na 3)
    Tambayoyin Matasa
  • Ta Yaya Zan Rika Bi da Yadda Nake Ji?
    Tambayoyin Matasa
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2023
wp23 Na 1 pp. 10-11
Annabi Musa yana fama da bakin ciki, yana kallon sama da yin adduꞌa.

3 | Taimako Daga Mutane da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki

LITTAFI MAI TSARKI YA AMBATA . . . Maza da mata masu aminci da suka yi fama da matsaloli “kamar mu.”​—YAKUB 5:17.

Abin da Hakan Yake Nufi

A cikin Littafi Mai Tsarki akwai labaran maza da mata da suka yi fama da baƙin ciki iri-iri. Saꞌad da muka karanta labaransu, za mu ga ɗaya daga cikinsu da ya yi fama da irin yanayin da muke ciki.

Yadda Yin Hakan Zai Taimaka

Dukanmu muna bukatar mu san cewa mutane sun fahimci yadda muke ji. Hakan ya fi muhimmanci ma idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Idan muka karanta labaran mutane a Littafi Mai Tsarki, za mu koya cewa su ma sun yi fama da irin yanayin da muke ciki. Hakan zai sa mu gane cewa su ma sun yi fama kamar mu kuma sun sami taimako saꞌad da suke fama da tsananin damuwa da yanayi mai wuya.

  • Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da furuci da waɗanda suke cikin yanayi mai wuya suka faɗa. Ka taɓa yin tunanin cewa, ‘Kai! Wannan yanayin ya ishe ni’? Musa da Iliya da Dauda sun yi hakan.​—Littafin Ƙidaya 11:14; 1 Sarakuna 19:4; Zabura 55:4.

  • Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wata mata mai suna Hannatu da ke cike da “ɓacin zuciya” domin ta kasa haihuwa kuma kishiyarta ta yi ta wulaƙanta.​—1 Sama’ila 1:​6, 10.

  • Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wani mutum mai suna Ayuba da ya fuskanci irin yanayin da muke ciki. Ko da yake shi mai bangaskiya ne sosai ya yi fama da tsananin baƙin ciki, har ma ya ce: “Ina ƙyamar raina, na gaji da rayuwa.”​—Ayuba 7:16.

Idan muka koya yadda suka jimre da yanayinsu, mu ma za mu iya samun ƙarfin jimrewa da matsalolinmu.

Yadda Littafi Mai Tsarki Yake Taimakawa Kevin

Yadda Ciwon Bipolar Ya Shafe Ni

Kevin yana shan shayi da abokansa guda biyu.

“Da na kusan shekara hamsin, an gano cewa ina da ciwon bipolar da ke shafan yadda mutum ke ji a ransa wanda yakan sauya yanzu yanzu daga tsananin farin ciki ya koma tsananin baƙin ciki. Akwai lokutan da nakan ji kamar zan iya magance matsalolina. Amma a wasu lokuta nakan ji kamar ba amfanin rayuwa.”

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Taimaka Min

“Wani a Littafi Mai Tsarki da ya yi fama kamar ni shi ne manzo Bitrus. Ya yi kurakurai da suka sa ya ji kamar ba shi da amfani. Maimakon Bitrus ya ci gaba da irin wannan tunanin, ya yi tarayya da abokai da suka taimaka masa. Idan ina fama da wannan ciwon, nakan yi tunani game da kurakuran da na yi kuma in ji kamar ba ni da amfani. Kamar Bitrus nakan yi cuɗanya da abokaina da suke so su taimaka mini kada in karaya.

“Wani da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da ya ƙarfafa ni sosai shi ne Sarki Dauda. Sau da yawa ya yi baƙin ciki game da yanayinsa kuma ya yi da-na-sani don kurakuransa. Yanayinsa ya yi kamar nawa domin a wasu lokuta na yi da-na-sani don abin da na yi ko kuma na fada. Furucin Dauda a Zabura ta 51 yana ƙarfafa ni. A aya ta 3, Dauda ya ce: ‘Ina sane da zunuban gangancina, zunubaina suna a gabana kullum.’ Haka nake ji saꞌad da nake baƙin ciki sosai, yana yi mini wuya in kasance da raꞌayin da ya dace game da kaina. Nakan yi tunani a kan kalmomin Dauda da ke aya ta 10 da ta ce: ‘Ya Allah, bari ka halicci zuciya marar ƙazanta a cikina, ka ba ni sabon ruhu da zuciya marar canjawa.’ Ina yi wa Allah irin wannan roƙon don ya taimaka mini in kasance da raꞌayin da ya dace game da kaina. Ƙari ga haka, aya ta 17 tana ƙarfafa ni, kuma ta ce: ‘Halin sauƙin kai da zuciya mai tuba ba za ka ƙi ba, ya Allah.’ Wannan ayar tana ƙarfafa ni cewa Allah yana ƙaunata.

“Ta wajen mai da hankali ga labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki da abin da Allah ya ba ni yanzu, hakan ya sa in daɗa kasancewa da bege. Na kasance da tabbaci cewa alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su faru kuma hakan ya taimaka mini.”

Don Samun Ƙarin Bayani:

Ka karanta talifin nan, “Saꞌad da Ka Gaji da Rayuwa,” da ke mujallar Hasumiyar Tsaro! na 2, na 2019 a dandalin jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba