Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Yuli pp. 8-13
  • Ka San Bambancin Gaskiya da Karya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka San Bambancin Gaskiya da Karya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • HALAYE DA ZA SU TAIMAKA MANA MU SAN GASKIYA
  • YADDA ZA MU RIƘE GASKIYAR DA MUKA KOYA
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Yuli pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 28

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

Ka San Bambancin Gaskiya da Ƙarya?

“Ku tsaya da ƙarfi, gaskiya ta zama ɗamararku.” —AFIS. 6:14.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu koyi yadda za mu bambanta gaskiyar da Jehobah yake koya mana da ƙaryar da Shaiɗan da maƙiyanmu suke yaɗawa.

1. Yaya kake ji game da gaskiyar da muke koya?

BAYIN Jehobah suna son gaskiyar da ke Kalmar Allah. Gaskiyar nan ita ce tushen dukan abubuwan da muka yi imani da su. (Rom. 10:17) Ba ma shakkar cewa Jehobah ne ya kafa ikilisiyar Kirista ta zama “ginshiƙi da kuma tushen gaskiya.” (1 Tim. 3:15) Kuma muna son yin biyayya ga waɗanda suke ja-goranci a tsakaninmu domin suna bayyana mana gaskiyar da ke Kalmar Allah, kuma suna ba mu umurnai da suke taimaka mana mu yi nufin Allah.—Ibran. 13:17.

2. Kamar yadda Yakub 5:19 ta nuna, mene ne zai iya faruwa da mu bayan mun koyi gaskiyar da ke Kalmar Allah?

2 Amma ko da mun yarda da gaskiyar da muka koya, kuma mun yarda cewa muna bukatar mu bi ja-gorancin ƙungiyar Jehobah, idan ba mu yi hankali ba, za mu iya bijirewa. (Karanta Yakub 5:19.) Babban burin Shaiɗan shi ne ya sa mu daina yarda da Littafi Mai Tsarki, da kuma ja-gorancin da ƙungiyar Jehobah take mana.—Afis. 4:14.

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙe gaskiyar da muka koya kuma mu bi ta? (Afisawa 6:13, 14)

3 Karanta Afisawa 6:13, 14. Nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan zai yi amfani da ƙarya da wayo don ya ruɗi dukan alꞌummai su yi gāba da Jehobah. (R. Yar. 16:13, 14) Kuma mun san cewa Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa ya ruɗi bayin Jehobah. (R. Yar. 12:9) Shi ya sa yake da muhimmanci sosai mu koyi yadda za mu bambanta gaskiya da ƙarya, kuma mu bi gaskiyar. (Rom. 6:17; 1 Bit. 1:22) Yin hakan ne zai sa mu tsira ma ƙunci mai girma.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifi?

4 A wannan talifi, za mu ga halaye biyu da muke bukata don mu iya gane gaskiyar da ke Kalmar Allah, kuma mu yarda da ja-gorancin ƙungiyar Jehobah. Bayan haka, za mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka mana mu riƙe gaskiyar da muka koya sosai.

HALAYE DA ZA SU TAIMAKA MANA MU SAN GASKIYA

5. Idan muna tsoron Jehobah, ta yaya hakan zai taimaka mana mu san gaskiya?

5 Tsoron Jehobah. Tsoron Jehobah yana nufin mu ƙaunace shi sosai, da har ba za mu so mu yi wani abin da zai ɓata masa rai ba. Idan muna tsoron Jehobah, za mu so mu san bambanci da ke tsakanin gaskiya da ƙarya, da kuma abin da ya dace da wanda bai dace ba, don kar mu yi abin da zai ɓata masa rai. (K. Mag. 2:3-6; Ibran. 5:14) Kada mu taɓa yarda tsoron mutum ya hana mu yin abin da zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah, domin a yawancin lokuta, abin da mutane suke so yakan ɓata ma Jehobah rai.

6. Ta yaya tsoron mutum ya sa ꞌyan leƙen asiri goman nan suka kasa faɗin gaskiya?

6 Idan muna tsoron mutane fiye da Jehobah, hakan zai iya sa mu gaskata abin da ba gaskiya ba ne. Bari mu ga abin da ya faru da mutane 12 da suka je leƙen asiri a Ƙasar Alkawari. Mutane goma daga cikinsu sun ji tsoron Kanꞌaniyawa fiye da Jehobah. Sun gaya ma sauran jamaꞌar Israꞌila cewa: “A ina! Ba za mu iya ci su da yaƙi ba, gama sun fi mu ƙarfi!” (L. Ƙid. 13:27-31) A ido kam, Kanꞌaniyawan su fi Israꞌilawa ƙarfi. Amma duk wanda ya ce Israꞌilawa ba za su iya cin su da yaƙi ba, ya manta da Jehobah ke nan. Da a ce maza goman nan sun mai da hankali a kan abin da Jehobah yake so Israꞌilawa su yi, kuma sun yi tunani a kan yadda Jehobah ya cece su a baya, da sun ga cewa Kanꞌaniyawa ba su kai kome ba a gaban Allah Mai Iko Duka. Amma maza biyu da suka rage, wato Joshua da Kaleb, ba su bi halin waɗannan marasa bangaskiya ba, domin suna so su faranta ma Jehobah rai. Sun gaya ma Israꞌilawan cewa: “Idan Yahweh yana jin daɗinmu, zai kai mu ƙasar, ya kuma ba mu ita.”—L. Ƙid. 14:6-9.

7. Idan muna so mu daɗa jin tsoron Jehobah, me za mu yi? (Ka kuma duba hoton.)

7 Don mu daɗa jin tsoron Jehobah, dole mu mai da hankali ga abin da zai faranta masa rai a kowane lokaci. (Zab. 16:8) Yayin da kake karanta labaran Littafi Mai Tsarki, ka tambayi kanka, ‘Da a ce ni ne a wannan yanayin, shin abin da zai faranta ma Jehobah rai ne zan sa a gaba?’ Alal misali, a ce kana cikin Israꞌilawa lokacin da ꞌyan leƙen asirin suka kawo labari cewa Israꞌilawa ba za su iya cin mutanen Kanꞌana da yaƙi ba, za ka yarda da maganarsu kuma ka ji tsoro? Ko dai za ka yi ƙarfin zuciya don kana ƙaunar Jehobah kuma kana so ka faranta masa rai? Dukan taron jamaꞌar Israꞌila ba su yarda da gaskiyar da Joshua da Kaleb suka gaya musu ba. Don haka, ba waninsu da ya shiga Ƙasar Alkawari.—L. Ƙid. 14:10, 22, 23.

Israꞌilawa suna so su jejjefi Joshua da Kaleb da duwatsu. Joshua da Kaleb kuma suna ƙoƙari su kwantar musu da hankali, ga kunshin girgije a bayansu.

Da kana a wurin, da maganar wa za ka bi? (Ka duba sakin layi na 7)


8. Wane hali ne muke bukata, kuma me ya sa?

8 Ka zama mai sauƙin kai. Jehobah yana sa masu sauƙin kai su gane gaskiyar da ke Kalmarsa. (Mat. 11:25) Sauƙin kai ne ya sa muka yarda a koya mana gaskiya. (A. M. 8:30, 31) Duk da haka, dole ne mu yi hankali don kada mu zama masu girman kai. Girman kai zai iya sa mu soma yin tunani cewa raꞌayinmu yana da muhimmanci kamar ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da umurni da ƙungiyarmu ta bayar.

9. Mene ne zai taimaka mana mu ci-gaba da zama masu sauƙin kai?

9 Don mu ci-gaba da zama masu sauƙin kai, muna bukatar mu tuna cewa mu ba wani abu ba ne idan aka kwatanta mu da Jehobah. (Zab. 8:3, 4) Wani abu kuma da zai taimaka mana shi ne, mu roƙi Jehobah ya sa mu zama masu sauƙin kai, kuma mu zama waɗanda za a iya koyar da su. Jehobah zai taimaka mana mu ɗauki raꞌayinsa da muke koya a Littafi Mai Tsarki da umurnai da ƙungiyarsa take ba mu da muhimmanci, fiye da namu raꞌayi. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka bincika abubuwa da suka nuna cewa Jehobah yana son mai sauƙin kai, kuma yana ƙin mai girman kai da mai taurin kai. Ƙari ga haka, ka yi hankali sosai don kar ka zama mai girman kai, musamman idan aka ba ka wani aiki da zai sa mutane su san ka.

YADDA ZA MU RIƘE GASKIYAR DA MUKA KOYA

10. Su wane ne Jehobah ya yi amfani da su don ya yi wa mutanensa ja-goranci?

10 A kullum, ka yarda da umurnai da ƙungiyarmu take ba mu. A lokacin Israꞌilawa, Jehobah ya yi amfani da Musa da Joshua ya ba wa jamaꞌarsa umurnai. (Yosh. 1:16, 17) Kuma da Israꞌilawan suka ɗauki Musa da Joshua a matsayin wakilan Jehobah, Jehobah ya albarkace su. Daga baya, da aka kafa ikilisiyar Kirista, Jehobah ya yi amfani da manzannin Yesu 12 don ya yi wa mutanensa ja-goranci. (A. M. 8:14, 15) A-kwana-a-tashi, masu ja-gorancin sun haɗa da dattawa da suke Urushalima. Kuma da ikilisiyar suka bi ja-gorancin mutanen nan, bangaskiyarsu ta ƙaru sosai kuma sun yi ta “ƙara yawa kowace rana.” (A. M. 16:4, 5) Mu ma a yau, duk saꞌad da muka bi umurnin da ƙungiyarmu take ba mu, muna samun albarka sosai. Amma yaya Jehobah zai ji idan muka ƙi yarda da waɗanda ya naɗa su yi mana ja-goranci? Abin da ya faru lokacin da Israꞌilawa za su shiga Ƙasar Alkawari zai taimaka mana mu san yadda zai ji.

11. Me ya faru da waɗanda suka raina Musa, wanda Jehobah ya naɗa ya yi wa mutanensa ja-goranci? (Ka kuma duba hoton.)

11 Da Israꞌilawa za su Ƙasar Alkawari, akwai lokacin da wasu shugabannin jamaꞌar, waɗanda aka san su sosai, suka raina matsayin Musa na shugaba da Jehobah ya naɗa. Sun ce: “Dukan taron jamaꞌar nan an keɓe kowannensu da tsarki [ba Musa kaɗai ba], Yahweh kuma yana tare da su.” (L. Ƙid. 16:1-3) Ko da yake gaskiya ne cewa an keɓe “dukan taron jamaꞌar” da tsarki, Musa ne Jehobah ya zaɓa ya yi musu ja-goranci. (L. Ƙid. 16:28) Don haka, da suka raina Musa, Jehobah ne suka raina. Maimako su mai da hankali a kan abin da Jehobah yake so, abin da suke so ne suka sa a gaba, wato matsayi da suna. Saboda haka, Jehobah ya hallaka dukansu, har da dubban mutane da suka goyi bayansu. (L. Ƙid. 16:30-35, 41, 49) Ba shakka, a yau ma Jehobah zai yi fushi da duk wanda ya ƙi ya yarda da waɗanda Ya naɗa su yi ja-goranci a ƙungiyarsa.

Musa da Haruna suna tsaye a kan wani dutse, a gabansu kuma ga Israꞌilawa suna ihu suna daga hannayensu sama.

Da kana a wurin, da wa za ka goyi bayansa? (Ka duba sakin layi na 11)


12. Me ya sa za mu iya yarda da ƙungiyar Jehobah a koyaushe?

12 Za mu iya yarda da ƙungiyar Jehobah a koyaushe. Me ya sa? Domin idan waɗanda suke ja-goranci a ƙungiyarmu suka ga cewa muna bukatar yin gyara a yadda muka fahimci wata koyarwar Littafi Mai Tsarki, ko kuma a yadda muke yin abubuwa, sukan yi gyaran ba tare da ɓata lokaci ba. (K. Mag. 4:18) Sukan yi haka ne domin abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne su faranta ma Jehobah rai. Ƙari ga haka, suna iya ƙoƙarinsu su yanke shawarwari bisa ga Kalmar Allah, domin Kalmar Allah ce ya kamata dukan bayin Jehobah su bi.

13. Mece ce “koyarwar nan ta gaskiya,” kuma me ya kamata mu yi da ita?

13 “Ka riƙe koyarwar nan ta gaskiya sosai.” (2 Tim. 1:13) “Koyarwar nan ta gaskiya” tana nufin abubuwan da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. (Yoh. 17:17) Abubuwan da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ne muka yi imani da su. Kuma ƙungiyar Jehobah tana koya mana mu riƙe koyarwar nan sosai. Idan muna yin haka, za mu sami albarka.

14. Ta yaya wasu Kiristoci suka daina riƙe “koyarwar nan ta gaskiya”?

14 Me zai faru da mu idan muka daina riƙe “koyarwar nan ta gaskiya”? Don mu ga amsar, bari mu bincika wani abin da ya faru a karni na farko. Da alama wasu ꞌyanꞌuwa sun yaɗa labarin ƙarya cewa ranar Jehobah ta zo. Wataƙila wani ne ya rubuta musu wasiƙa da sunan Bulus, kuma ya yi musu wannan ƙaryar. Maimako wasu ꞌyanꞌuwa da suke Tasalonika su bincika su ga ko gaskiya ne, sun gaskata da wannan ƙaryar kuma sun yi ta yaɗa ta. Da sun riƙe abubuwan da Bulus ya koya musu lokacin da yake tare da su, da ba a ruɗe su ba. (2 Tas. 2:1-5) Bulus ya gargaɗi ꞌyanꞌuwan cewa ba kome da suka ji ne za su gaskata ba. Domin Bulus ba ya so su sake yin wannan kuskure, ya nuna musu yadda za su san wasiƙar da ta fito daga wurinsa. Ya ce: “Ni Bulus, nake wannan gaisuwa da hannuna. Wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.”—2 Tas. 3:17.

15. Me zai taimaka mana kar a ruɗe mu idan muka ji abin da ya yi kama da gaskiya? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)

15 Mene ne za mu iya koya daga abin da Bulus ya gaya wa ꞌyanꞌuwa da ke Tasalonika? Idan muka ji wani abin da bai yi daidai da abin da muka koya a Littafi Mai Tsarki ba, ko muka ji wani labari mai ban mamaki, mu yi hankali. A Tarayyar Soviet ta dā, maƙiyanmu sun yaɗa wani saƙo ta wasiƙa da sunan hedkwatarmu. Wasiƙar ta ƙarfafa wasu ꞌyanꞌuwanmu su ƙafa tasu ƙungiya mai zaman kanta. Kuma an rubuta wasiƙar kamar daga hedkwatarmu ce. Amma ꞌyanꞌuwa masu aminci ba su yarda da wasiƙar ba, domin sun ga cewa abin da ta ce bai jitu da gaskiyar da suka koya ba. A yau ma, maƙiyanmu suna amfani da abubuwa kamar intane da dandalin sada zumunta don su raɓa kanmu ko su rikitar da mu. Maimako mu “jijjigu da sauri,” mu dakata mu yi tunani ko abin da muka ji, ko muka karanta, ya jitu da gaskiyar da muka riga muka koya. Hakan zai sa mu tsaya daram a kan gaskiya.—2 Tas. 2:2; 1 Yoh. 4:1.

Hotuna: 1. Abin da ya faru shekaru da yawa da suka shige. ꞌYanꞌuwa sun taru a wani gida, kuma wani danꞌuwa yana nuna musu wasika da aka rubuta da sunan “Watch Tower.” 2. A zamaninmu, ꞌyanꞌuwa sun taru suna shakatawa, sai wani danꞌuwa ya dauki wayarsa yana nuna musu wani bidiyo da ake yadawa a intane game da Shaidun Jehobah.

Kada ka yarda da ƙarairayi da suka yi kama da gaskiya (Ka duba sakin layi na 15)a


16. Bisa ga Romawa 16:17, 18, me ya kamata mu yi idan wasu suka daina bin gaskiya?

16 Ka ci-gaba da yin abokantaka da waɗanda suke ƙaunar Jehobah. Allah yana so mu riƙa bauta masa da haɗin kai. Kuma idan muka ci-gaba da riƙe gaskiyar da muke koya, za mu ci-gaba da kasancewa da haɗin kai. Waɗanda suka daina bin wannan gaskiyar sukan kawo rashin jituwa a ikilisiya, shi ya sa Allah ya ce mu “yi nesa da su!” In ba haka ba, za su iya sa mu daina bin gaskiya.—Karanta Romawa 16:17, 18.

17. Ta yaya za mu amfana idan muka san gaskiya kuma muka riƙe ta?

17 Idan muka gane gaskiya kuma muka riƙe ta sosai, ba abin da zai raba mu da Jehobah, kuma bangaskiyarmu ba za ta yi sanyi ba. (Afis. 4:15, 16) Koyarwar ƙarya da Shaiɗan yake yaɗawa ba za ta yi tasiri a kanmu ba, kuma Jehobah zai kiyaye mu a lokacin ƙunci mai girma. Ku ci-gaba da riƙe koyarwar gaskiya sosai, “Allah mai salama kuwa zai kasance tare da ku.”—Filib. 4:8, 9.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu san gaskiya?

  • Ta yaya tsoron Jehobah da sauƙin kai za su taimaka mana mu san gaskiya kuma mu bi ta?

  • Me zai taimake mu mu riƙe gaskiyar da muka koya sosai?

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

a BAYANI A KAN HOTO: Hoton ya kwatanta abin da ya faru shekaru da dama da suka shige a Tarayyar Soviet, lokacin da wasu ꞌyanꞌuwa suka sami wasiƙa da maƙiyanmu suka rubuta ta kamar daga hedkwatarmu ne aka turo. A zamaninmu ma, maƙiyanmu za su iya yin amfani da intane, don su yaɗa ƙarairayi game da ƙungiyarmu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba