Ka Taɓa Yi Wa Kanka Tambayoyin Nan?
Idan kowa yana son zaman lafiya, me ya sa ake yawan yaƙe-yaƙe?
Zai yiwu mu sami kwanciyar hankali a duniyar nan da ke cike da mugunta?
Za a taɓa daina yin yaƙi kuwa?
Amsoshin waɗannan tambayoyin da Littafi Mai Tsarki ya bayar za su iya ba ka mamaki, kuma ba shakka za su ƙarfafa ka.
Za ka iya bincika da kanka don ka ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batu mai muhimmanci. Akwai ƙarin abubuwa da za ka iya koya daga wannan fitowar Hasumiyar Tsaro.