Yadda Za Ka Sami Salama Duk da Cewa Ana Yaƙi da Tashin Hankali
Gary wanda ya yi aikin soja a dā ya ce: “Kafin in fara nazarin Littafi Mai Tsarki, na kasa gane dalilin da ya sa ake yawan mugunta da rashin adalci da kuma tashin hankali a duniya. Amma yanzu ina da kwanciyar hankali. Na san cewa Jehobah zai kawo salama a dukan duniya.”
Ba Gary kaɗai ne ya ji hakan ba. Ka ga yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka ma wasu ma.
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Gama kai, ya Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara.”—Zabura 86:5.
YADDA HAKAN YAKE TAIMAKAWA: Wilmar daga ƙasar Kwalambiya ya ce: “Wannan ayar ta tabbatar mini cewa Jehobah mai jinƙai ne. Na san cewa a shirye yake ya gafarta mini dukan abubuwan da na yi saꞌad da nake aikin soja.”
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ga shi, ina halittar sabon sama da sabuwar ƙasa! Ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba, tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.”—Ishaya 65:17.
YADDA HAKAN YAKE TAIMAKAWA: Zafirah daga ƙasar Amurka ta ce: “Na yi fama sosai da ciwon tsananin damuwa bayan tashin hankali, da kuma baƙin ciki saboda abubuwan da na shaida saꞌad da nake aikin soja. Amma wannan nassin ya tuna mini cewa nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai sa in manta da dukan abubuwan nan. Ba za su ƙara kasancewa a zuciyata ba. Wannan kyauta ne mai muhimmanci!”
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Bari adalci ya yalwata a kwanakinsa, salama ta ƙaru muddin wata yana nan.”—Zabura 72:7.
YADDA HAKAN YAKE TAIMAKAWA: Oleksandra daga ƙasar Yukiren ta ce: “Ina yawan tunani a kan kalmomin nan. Nan ba da jimawa ba yaƙi da mummunan sakamakonsa za su ƙare, kuma ba za mu damu cewa wani abu marar kyau zai faru da waɗanda muke ƙauna ba.”
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Mutanenku da suka mutu za su rayu, . . . Ya ku masu zama a ƙura, ku tashi ku yi waƙoƙin farin ciki!”—Ishaya 26:19.
YADDA HAKAN YAKE TAIMAKAWA: Marie daga ƙasar Ruwanda ta ce: “An kashe kusan dukan ꞌyan iyalina saꞌad da aka yi ma ƙabilar Tutsi kisan kare dangi. Amma wannan ayar ta tabbatar mini da cewa zan sake ganin su. Ina sa ran ganin lokacin da zan ji muryoyinsu bayan an ta da su daga mutuwa!”
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ba da daɗewa ba mugaye za su ɓace, . . . Amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”—Zabura 37:10, 11.
YADDA HAKAN YAKE TAIMAKAWA: Daler daga ƙasar Tajikistan ya ce: “Ko da yake an gama yaƙin, amma akwai rashin adalci da kuma mugayen mutane. Waɗannan ayoyin sun taimaka mini sosai. Jehobah yana ganin kome kuma ya fahimci yanayina. Ya yi alkawari cewa nan ba da jimawa ba dukan matsaloli za su ƙare kuma za mu manta da su.”
Mutanen da aka ambata a wannan mujallar suna cikin miliyoyin Shaidun Jehobah waɗanda Littafi Mai Tsarki ya taimaka musu su sami salama. Sun koyi yadda za su daina nuna ƙiyayya domin bambancin launin fata, ko bambancin ƙasa, ko na ƙabila, da dai sauransu. (Afisawa 4:31, 32) Shaidun Jehobah ba sa saka hannu a harkokin siyasa kuma ba sa yin yaƙi.—Yohanna 18:36.
Shaidun Jehobah suna kuma taimaka wa junansu kamar iyali. (Yohanna 13:35) Alal misali, Oleksandra, da muka ambata ɗazu, tare da ꞌyarꞌuwarta sun gudu zuwa wata ƙasa domin yaƙi. Ta ce: “Saꞌad da muka ƙetare iyakar ƙasar, sai nan da nan muka ga wasu ꞌyanꞌuwa da suka zo su karɓe mu. Taimakon da suka yi mana, ya taimaka mana mu saba da rayuwa a matsayin ꞌyan gudun hijira a ƙasar.”
Muna gayyatar ka zuwa taronmu don ka ƙara koyan yadda za ka sami salama a yanzu, da kuma alkawarin da Littafi Mai Tsarki ya yi cewa a nan gaba za a sami salama a duniya. Ka ziyarci dandanlin jw.org/ha don ka ga wurin taronmu da ke kusa da kai, ko kuma ka ce wani Mashaidin Jehobah ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta, da littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!