Mutane ba za su iya kawo ƙarshen yaƙi ba
Yadda Za A Kawo Ƙarshen Yaƙi da Tashin Hankali
Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ne zai “tsai da yaƙe-yaƙe a dukan duniya,” ba mutane ba.—Zabura 46:9.
ALLAH ZAI HALLAKA GWAMNATOCIN ꞌYANꞌADAM
Allah zai kawo ƙarshen gwamnatocin ꞌyanꞌadam ta wurin yaƙin da Littafi Mai Tsarki ya kira yaƙin Armageddon.a (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 16:16) A lokacin, za a tattara “dukan sarakunan duniya, . . . saboda yaƙi a babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka.” (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 16:14) Armageddon shi ne yaƙin da Allah zai yi amfani da shi ya kawo ƙarshen dukan yaƙe-yaƙe.
Allah zai cire gwamnatocin ꞌyanꞌadam kuma ya kawo Mulkinsa, ko kuma gwamnatinsa. Gwamnatin za ta yi sarauta daga sama, kuma ba za a taɓa hallaka ta ba. (Daniyel 2:44) Allah ya zaɓi Ɗansa, Yesu Kristi, ya zama Sarkin Mulkinsa. (Ishaya 9:6, 7; Matiyu 28:18) Wannan gwamnatin shi ne Mulkinb da Yesu ya ce wa mabiyansa su yi adduꞌa ya zo. (Matiyu 6:9, 10) Gwamnatin nan da Yesu ne Sarkinta za ta yi sarauta a dukan duniya, kuma za ta sa dukan mutane a faɗin duniya su kasance da haɗin kai.
Yesu ba zai yi amfani da ikonsa don amfanin kansa kamar yadda mutane masu mulki suke yi ba. Da yake Yesu mai adalci ne kuma ba ya nuna bambanci, babu wanda zai ji kamar ba a damu da shi ba, ko kuma an yi masa rashin adalci saboda launin fatarsa, ko ƙasarsa, ko kuma ƙabilarsa. (Ishaya 11:3, 4) Kuma mutane ba za su yi faɗa don su kwato ꞌyancinsu ba. Me ya sa? Domin Yesu zai biya bukatun kowane mutum. Zai ‘kuɓutar da masu bukata yayin da suka yi kira, da matalauta da kuma marasa taimako. . . . Daga masu danniya da masu ta da hankali zai fanshe su.’—Zabura 72:12-14.
Mulkin Allah zai kawar da muggan makamai daga duniya. (Mika 4:3) Zai kuma hallaka mugayen mutane da suka ƙi daina yaƙi ko kuma suke ta da hankalin mutane. (Zabura 37:9, 10) Kowa zai kasance da kwanciyar hankali a duk inda yake a duniya.—Ezekiyel 34:28.
Saꞌad da gwamnatin Allah ta soma sarauta a duniya, kowa zai yi farin ciki kuma ya ji daɗin rayuwa. Gwamnatin za ta cire matsalolin da suke jawo yaƙi a tsakanin mutane, kamar talauci, da yunwa, da kuma rashin gida. Kowa zai samu isasshen abinci mai gina jiki da kuma gida mai kyau.—Zabura 72:16; Ishaya 65:21-23.
Mulkin Allah zai cire dukan sakamako marasa kyau da yaƙe-yaƙe suka jawo. Hakan ya haɗa da raunuka, da matsalar ƙwaƙwalwa, da baƙin ciki da mutane suke fama da shi saboda yaƙe-yaƙe. Waɗanda suka mutu ma, za a ta da su kuma za su rayu a duniya. (Ishaya 25:8; 26:19; 35:5, 6) Iyalai za su sake haɗuwa da juna, kuma mutane ba za su sake tuna da mummunan abubuwan da suka faru ba, domin “abubuwan dā sun ɓace.”—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.
ALLAH ZAI KAWAR DA ZUNUBI
Mulkin Allah zai sa kowa ya bauta wa Allah na gaskiya, wato Jehobahc, “Allah mai ƙauna da salama.” (2 Korintiyawa 13:11) Mutane za su koyi yadda za su zauna lafiya da juna. (Ishaya 2:3, 4; 11:9) Waɗanda suka yi biyayya ga Allah za su zama kamiltattu.—Romawa 8:20, 21.
ALLAH ZAI HALLAKA SHAIƊAN DA ALJANUNSA
Mulkin Allah zai hallaka waɗanda suke sa mutane su yi yaƙi, wato Shaiɗan da aljanunsa. (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 20:1-3, 10) Idan aka hallaka su, za a sami “salama” a yalwace.—Zabura 72:7.
Za ka iya kasance da tabbaci cewa alkawarin da Allah ya yi cewa zai kawo ƙarshen yaƙi da tashin hankali zai cika. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana da niyya da kuma ikon kawo ƙarshen yaƙi.
- Allah yana da hikima da kuma ikon da ake bukata don kawo ƙarshen yaƙi. (Ayuba 9:4) Babu abin da zai gagare shi.—Ayuba 42:2. 
- Allah ba ya so mutane su sha wahala ko kaɗan. (Ishaya 63:9) Ƙari ga haka, “yakan ƙi mai son tā da hankali.”—Zabura 11:5. 
- A kullum Allah yana cika abin da ya faɗa, ba zai taɓa yin ƙarya ba.—Ishaya 55:10, 11; Titus 1:2. 
A nan gaba, Allah zai kawo salama ta gaske, wadda za ta kasance har abada.
Allah zai kawo ƙarshen yaƙi
a Ka karanta talifin nan “Mene ne Yaƙin Armageddon?” a dandalin jw.org/ha.
b Ka kalli bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah? a dandalin jw.org/ha.
c Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.—Zabura 83:18.