Me Ya Sa Ba A Daina Yaƙi da Tashin Hankali Ba?
Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da yake jawo yaƙi da tashin hankali da kuma abin da ya sa ba su daina faruwa ba.
ZUNUBI
Allah ya halicci iyayenmu na farko, wato Adamu da Hauwaꞌu, a kamanninsa. (Farawa 1:27) Hakan yana nufin cewa za su riƙa nuna halayen Allah, kamar salama da ƙauna. (1 Korintiyawa 14:33; 1 Yohanna 4:8) Amma, Adamu da Hauwaꞌu sun yi wa Allah rashin biyayya kuma sun yi zunubi. Ta haka, dukanmu mun gāji zunubi da kuma mutuwa. (Romawa 5:12) Da yake mun gāji zunubi, a yawanci lokaci mukan yi tunani marar kyau, kuma hakan yana sa mutane da yawa su aikata mugunta.—Farawa 6:5; Markus 7:21, 22.
GWAMNATIN ꞌYANꞌADAM
Allah bai halicce mu mu yi mulkin kanmu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba mutum ne yake da iko ya kiyaye tafiyarsa ba.” (Irmiya 10:23) Saboda haka, gwamnatocin ꞌyanꞌadam ba za su iya sa a daina yaƙi da tashin hankali gabaki-ɗaya ba.
SHAIƊAN DA ALJANUNSA
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “duniya duka tana a hannun mugun nan.” (1 Yohanna 5:19) Shaiɗan Ibilis shi ne “mugun nan,” kuma shi mugu ne mai kisa. (Yohanna 8:44) Shaiɗan tare da aljanu ne suke sa mutane su soma yaƙi da tashin hankali.—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9, 12.
Mutane ba za su iya cire abubuwan da suke jawo yaƙi da tashin hankali ba, amma Allah zai iya.