AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Me ya sa zai dace ka yi addu’a Mulkin Allah ya zo?
Mulkin Allah gwamnati ce ta samaniya. Yesu ya ce wa mabiyansa su yi addu’a Mulkin ya zo domin Mulkin zai sa a sake samun zaman lafiya da kuma adalci a duniya. Babu gwamnatin ɗan Adam da za ta iya kawar da mugunta da rashin adalci da cututtuka, sai dai Mulkin Allah, kuma tabbas zai yi hakan. Allah ya riga ya zaɓi Yesu ya zama Sarkin wannan Mulkin. Ƙari ga haka, Jehobah ya zaɓi wani rukuni daga cikin mabiyan Yesu su yi sarauta tare da shi a Mulkin.—Karanta Luka 11:2; 22:28-30.
Ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai kawar da dukan waɗanda ba sa goyon bayan sarautarsa. Saboda haka, a duk lokacin da muke addu’a Mulkin Allah ya zo, muna roƙo ne gwamnatin Allah ya maye gurbin dukan gwamnatocin ’yan Adam.—Karanta Daniyel 7:13, 14; Ru’ya ta Yohanna 11:15, 18.
Me ya sa Mulkin Allah zai amfani mutane?
Yesu yana da jin ƙai, saboda haka, shi ya dace ya zama Sarkin Mulkin Allah. A matsayinsa na Sarkin da Allah ya naɗa, Yesu yana da iko ya taimaka wa dukan waɗanda suke roƙon Allah ya taimake su. —Karanta Zabura 72:8, 12-14.
Mulkin Allah zai amfani dukan waɗanda suke addu’a Mulkin ya zo kuma suna rayuwar da ta jitu da nufin Allah. Idan ka ƙoƙarta ka koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Mulkin Allah, ba za ka taba yin da-na-sani ba.—Karanta Luka 18:16, 17; Yohanna 4:23.