LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE
Na damu da kaina ne kawai a dā
SHEKARAR HAIHUWA: 1951
ƘASAR HAIHUWA: JAMUS
TARIHI: MAI FAHARIYA DA SON ’YANCIN KAI
RAYUWATA A DĀ:
Bayan an haife ni, iyalinmu sun yi zama na ’yan shekaru a birnin Leipzig, a Jamhuriyar Jamus ta Gabas, kusa da iyakar ƙasashen Czech da Poland. Sa’ad da na kai ɗan shekara shida, iyalinmu suka ƙaura zuwa ƙasar Brazil, daga baya kuma zuwa ƙasar Ecuador domin irin aikin da mahaifina yake yi.
Sa’ad da na kai ɗan shekara 14, sai aka kai ni makarantar kwana a ƙasar Jamus. Da yake iyayena suna nesa da ni a can Amirka ta Kudu, na soma kula da kaina. Hakan ya sa na zama mai son ’yancin kai. Ban damu da yadda rayuwata take shafan wasu ba.
A lokacin da nake ɗan shekara 17, iyayena sun dawo ƙasar Jamus. Da farko, na zauna tare da su. Amma saboda halin son ’yanci, na kasa bin shugabancinsu. Sa’ad da na kai shekara 18, sai na bar gida.
Da wucewar lokaci, na kasa zama wuri ɗaya domin ina neman in san manufar rayuwa. Bayan na binciki salon rayuwar mutane dabam-dabam da kuma rukunoni da dama, na yanke shawara cewa abu mafi inganci da ya kamata in yi shi ne in yi yawo ina bincika wannan kyakkyawar duniyar, kafin ’yan Adam su gama hallaka ta.
Sai na bar ƙasar Jamus kuma na nufi Afirka a kan babur ɗina. Amma ba da daɗewa ba, na komo Turai don in gyara babur ɗina. Jim kaɗan bayan hakan, na je wata gaɓar teku a ƙasar Portugal kuma na yanke shawarar yin tafiyar ta jirgin ruwa. Hakan ya sa na bar babur ɗina a baya.
Na bi wasu matasa da suke shirin haye Tekun Atalantika. Daga cikinsu ne na sami matar da na aura, wato Laurie. Da farko, mun haye zuwa tsibiran Caribbean. Bayan mun huta kaɗan a tsibirin Puerto Rico, sai muka koma Turai. Ni da Laurie mun so mu sami ƙaramin jirgin ruwa da za mu mai da shi irin jirgin da ake zama a ciki kamar gida. Amma bayan mun yi nema na watanni uku kawai, sai aka tilasta mini in shiga soja a Jamus. Hakan ya ɗan taka mana birki.
Na yi watanni 15 ina aikin sojan ruwa a Jamus. A wannan lokacin, ni da Laurie muka yi aure kuma muka yi shirin ci gaba da irin rayuwarmu ta yin tafiye-tafiye. Kafin in zama soja, mun riga mun sayi jikin kwalekwale na ceton mutane. A lokacin da nake aikin soja, mun riƙa gina kwalekwalen don mu iya yin tafiyar da shi. Mun shirya za mu riƙa zama a ciki yayin da muke yawo muna binciken wannan kyakkyawar duniyar. Bayan na bar aikin soja, amma kafin mu gama gina wannan jirgin, sai Shaidun Jehobah suka ziyarce mu kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mu.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:
Da farko, ban ga dalilin canja salon rayuwata ba, domin na riga na auri matar da nake zama da ita a dā, kuma na daina shan taba. (Afisawa 5:5) Ƙari ga haka, na ɗauka cewa babu wata matsala da shirinmu na zagaya duniya muna yin bincike, tun da yake ba laifi ba ne mutum ya ba da rayuwarsa ga binciken halittun Allah.
Amma a gaskiya fa, na bukaci yin gyara, musamman ma a halina. Domin ina ji da kaina sosai kuma ina bala’in son ’yancin kai, na mai da hankali gaba ɗaya ga iyawata da kuma abubuwa da nake cimmawa. Rayuwata gaba ɗaya game da kaina ne kawai.
Wata rana, na karanta wa’azin da Yesu ya yi a kan Dutse. (Matta, surori 5-7) Da farko, ban fahimci koyarwar Yesu game da zama da farin ciki ba. Alal misali, ya ce farin ciki ya tabbata ga waɗanda suke jin yunwa da kuma ƙishirwa. (Matta 5:6) Na kasa fahimtar yadda mutum zai zama da farin ciki idan shi mabukaci ne. Yayin da na ci gaba da yin nazari, na fahimci cewa dukanmu muna bukatar ƙulla dangantaka da Allah, amma sai mun yarda da hakan kafin mu iya biya wa kanmu wannan bukatar. Hakan ya yi daidai da abin da Yesu ya faɗa cewa: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.”—Matta 5:3, New World Translation.
Bayan mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki a Jamus, sai ni da Laurie muka ƙaura zuwa Faransa kuma daga baya zuwa Italiya. Mun tarar da Shaidun Jehobah a duk waɗannan wuraren da muka tafi. Haɗin kansu da kuma yadda suke ƙaunar juna ya burge ni sosai. Na gano cewa Shaidun Jehobah a duk faɗin duniya ’yan’uwan juna ne. (Yohanna 13:34, 35) Da wucewar lokaci, ni da Laurie muka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah.
Bayan na yi baftisma, na ci gaba da gyara halina. Da ma ni da Laurie mun riga mun shirya za mu haye ta gaɓar Afirka, sai mu ci gaba zuwa Tekun Atalantika, sa’an nan mu haye zuwa Amirka. Sa’ad da mu biyu kawai muke tsakiyar ruwa a cikin wannan ƙaramin kwalekwalen, na fahimci cewa ni ba kome ba ne idan aka gwada ni da Mahaliccinmu mai girma. A nan tsakiyar teku, inda nake da lokaci barkatai, na soma karanta Littafi Mai Tsarki da zuciya ɗaya. Labarin rayuwar Yesu a duniya ya burge ni sosai. Ko da yake shi mutumi ne da bai yi zunubi ba kuma iyawarsa ta fi na kowa, bai ɗaukaka kansa ba. Bai mai da hankali ga kansa ba, amma ga Ubansa na samaniya.
Na gano cewa ina bukatar in sa Mulkin Allah farko a rayuwata
Yayin da na yi bimbini a kan misalin Yesu, na gano cewa ina bukatar in sa Mulkin Allah farko a rayuwata maimakon wasu abubuwa dabam da nake sha’awarsu. (Matta 6:33) Sa’ad da ni da Laurie muka isa Amirka, mun yanke shawara cewa za mu zauna a wurin kuma mu mai da hankali ga ibadarmu.
YADDA NA AMFANA:
A dā da nake dogara da kaina, ina yawan shakkar shawarwari da nake yankewa. Amma a yanzu, ina da ja-gora mai kyau sosai. (Ishaya 48:17, 18) Ƙari ga haka, na sami manufa a rayuwa, wato, bauta wa Allah da kuma taimaka ma wasu su san shi.
Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sun taimaka wa ni da matata Laurie mu inganta zaman aurenmu, kuma Jehobah ya ba mu kyakkyawar yarinya mai tsoron Allah.
Ba wai rayuwarmu tana da daɗi a kowane lokaci kamar zuma ba ne. Amma da taimakon Jehobah, ba za mu taɓa daina bauta masa ko kuma dogara da shi ba.—Misalai 3:5, 6.