Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 pp. 26-27
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • “Kamar Dai Ina da Kome da Nake So”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 pp. 26-27

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

MENE ne ya motsa wani ɓarawo kuma ɗan caca ya shawo kan jarabarsa kuma ya canja rayuwarsa? Ka karanta abin da ya ce.

“Ina son sukuwa sosai.”—RICHARD STEWART

SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1965

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: JAMAICA

TARIHI: ƊAN CACA KUMA MAI AIKATA LAIFI

RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a wani ɓangaren Kingston, a babban birnin Jamaica, inda talauci ya yi yawa ga kuma yawan jama’a. Akwai rashin aikin yi sosai a wurin, kuma ana yawan aikata laifi. ’Yan daba sun jefa mutane cikin tsoro. Ina jin ƙarar bindiga kusan kowace rana.

Mahaifiyata wadda take aiki tuƙuru ta yi iyakacin ƙoƙarinta don ta kula da ni da ƙanena da kuma ƙanwata. Ta tabbata cewa mun je makaranta mai kyau. Ba na sha’awar zuwa makaranta sosai, na fi son sukuwa. Ina ƙin zuwa makaranta, sa’an nan in wuce zuwa filin sukuwa. Sai da ma na hau dawakan.

Ba da daɗewa ba, na soma yin cacar sukuwa sosai. Na zama ɗan iska, kuma na soma bala’in neman mata. Na sha wi-wi kuma na yi fashi da makami domin in ci gaba da samun kuɗin yin irin rayuwar da nake yi. Na mallaki bindigogi da yawa, amma yanzu ina farin ciki cewa ban kashe kowa ba lokacin da nake fashi da makami.

Daga baya, ’yan sanda suka kama ni kuma suka jefa ni kurkuku domin laifuffukan da na aikata. Bayan an sake ni, na ci gaba da rayuwata ta dā. Kuma hakan ya sa na ƙara lalacewa. Ko da yake fuskata tana kama da na mai hankali, ni azzalumi ne, mai ƙarfin zuciya kuma ina da saurin fushi. Ban damu da kowa ba sai kaina.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A lokacin nan da rayuwata take cike da matsaloli, mahaifiyata ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta zama Mashaidiyar Jehobah. Na ga canje-canje masu kyau a halinta sai na fara ɗokin sanin dalilin hakan. Na yanke shawarar sanin abin da ya sa mahaifiyata ta yi wannan canjin, saboda haka, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu.

Na ga cewa koyarwar Shaidun Jehobah ta bambanta da na sauran addinai kuma Shaidu suna koyar da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Su kaɗai ne rukunin da na san cewa suna yin wa’azi gida-gida, kamar yadda Kiristoci na farko suka yi. (Matta 28:19; Ayyukan Manzanni 20:20) Sa’ad da na ga irin ƙauna ta ƙwarai da suke nuna wa juna, hakan ya sa na gamsu cewa wannan shi ne addini na gaskiya.—Yohanna 13:35.

Domin abin da na koya cikin Littafi Mai Tsarki, na gan cewa ina bukatar yin canje-canje da dama a rayuwata. Na fahimci cewa Jehobah Allah ya ƙi jinin fasikanci kuma idan ina son in faranta masa rai, dole ne in daina yin ayyukan da suke ƙazantar da jikina. (2 Korintiyawa 7:1; Ibraniyawa 13:4) Sa’ad da na koyi cewa abubuwan da nake yi za su iya sa Jehobah baƙin ciki ko farin ciki, hakan ya ratsa zuciyata sosai. (Misalai 27:11) Saboda haka, na ƙudurta daina shan wi-wi, na kawar da bindigogina, kuma na yi ƙoƙarin gyara halayena. Wasu daga cikin canji mafi wuya da na yi su ne daina neman mata da yin caca.

Da farko, ba na son abokaina su san cewa ina nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Amma na canja ra’ayina sa’ad da na karanta Matta 10:33, inda aka rubuta waɗannan kalmomi na Yesu: “Dukan wanda za ya yi musun sanina a gaban mutane, shi zan yi musunsa a gaban Ubana wanda ke cikin sama kuma.” Wannan furucin ya sa na gaya wa abokaina cewa ina nazari da Shaidu. Abin ya ba su mamaki. Ba su yarda cewa mutumi iri na zai so ya zama Kirista ba. Amma na gaya musu cewa na rabu da halayena na dā kuma ba zan ƙara yin su ba.

YADDA NA AMFANA: Mahaifiyata ta yi farin ciki sosai sa’ad da ta ga cewa na soma yin rayuwar da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki. Yanzu ta daina damuwa cewa zan aikata miyagun abubuwa. Muna yin hira game da dangantakarmu da Jehobah. A wasu lokatai, idan na tuna dā, ina mamakin irin canjin da na yi da taimakon Allah. Na daina sha’awar rayuwar lalata da son abin duniya yadda nake yi a dā.

Da a ce ban karɓi saƙon Littafi Mai Tsarki ba, da yanzu na riga na mutu ko kuma ina ɗaure a kurkuku. Yanzu ina da kyakkyawan iyali da ke cike da farin ciki. Bauta wa Jehobah Allah tare da ɗiyata mai hankali da kuma matata da ke ba ni goyon baya, yana faranta raina sosai. Ina godiya ga Jehobah da ya bar ni in kasance cikin ’yan’uwa Kirista masu ƙauna. Ina godiya cewa wani ya ƙoƙarta ya koya mini gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma ba na wasa da damar da nake samu na taimaka ma wasu su koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Ina matuƙar godiya ga Jehobah Allah domin ƙauna ta aminci da ya nuna mini ta wajen jawo ni wajensa.

[Bayanin da ke shafi na 27]

“Na koyi cewa abubuwan da nake yi suna iya sa Jehobah baƙin ciki ko farin ciki”

[Hoton da ke shafi na 27]

Tare da matata da ɗiyata

[Hoton da ke shafi na 27]

Na gan canji masu kyau a halin mahaifiyata

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba