TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE
Yaushe Ne Mulkin Allah Ya Soma Sarauta? —Sashe na 1
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wani Mashaidi mai suna Cameron ya ziyarci wani mutum mai suna Jon.
KA CI GABA DA “NEMAN” FAHIMI
Cameron: Jon, na ji daɗin tattaunawar da muka daɗe muna yi da kai a kan Littafi Mai Tsarki.a A tattaunawarmu ta ƙarshe, ka yi wata tambaya game da Mulkin Allah. Ka tambayi dalilin da ya sa Shaidun Jehobah suka gaskata cewa Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914.
Jon: E, na karanta wani littafinku da ya ce Mulkin Allah ya soma sarauta ne a shekara ta 1914. Hakan ya sa na so in sami ƙarin bayani da yake kun ce dukan koyarwarku daga Littafi Mai Tsarki ne.
Cameron: Hakan gaskiya ne.
Jon: Na taɓa karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya, amma ban ga inda aka ambata shekarar nan 1914 ba. Kuma na duba Littafi Mai Tsarki a cikin Intane amma ban ga inda aka rubuta shekara ta 1914 ba.
Cameron: Gaskiya ka yi ƙoƙari. Na yaba maka saboda dalilai biyu. Na farko, domin ka karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya. Hakan tabbaci ne cewa kana son Kalmar Allah sosai.
Jon: Hakika kuwa. Babu kamarsa.
Cameron: Na yarda da kai. Dalili na biyun kuwa shi ne yadda ka bincika Littafi Mai Tsarki domin ka sami amsar tambayarka. Ka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi. Ya ce mu ci gaba da “neman” fahimi.b
Jon: Na gode. Ai ni mai son ƙarin ilimi ne. Na ma yi wasu bincike a cikin wannan littafin da muke nazarinsa kuma na ɗan sami bayani a kan 1914. Ya ambata mafarkin da wani sarki ya yi game da wani babban itace da aka sare, amma ya sake girma.
Cameron: Oho! Kana zancen annabcin da ke cikin littafin Daniyel sura 4 game da mafarkin da Nebuchadnezzar, Sarkin Babila ya yi ko?
Jon: E, shi ɗin ne. Na karanta shi sau da sau, amma a gaskiya, ban ga abin da ya haɗa shi da Mulkin Allah ko kuma shekarar nan, 1914 ba.
Cameron: To ka san wani abu ne? Ko annabi Daniyel da kansa ma bai fahimci dukan abubuwan da aka gaya masa ya rubuta ba.
Jon: Da gaske?
Cameron: E. A cikin Daniyel 12:8, annabin ya ce: “Na ji, amma ban gane ba.”
Jon: Ashe ba ni kaɗai ba ne.
Cameron: A gaskiya, Daniyel bai fahimci wannan annabcin ba domin lokaci bai kai da Allah zai bayyana wa ’yan Adam annabce-annabcen da ke cikin littafin Daniyel ba. Amma a yanzu, za mu iya fahimtarsu.
Jon: Me ya sa ka faɗi hakan?
Cameron: Ka lura da abin da za mu karanta a cikin aya ta tara. Daniyel 12:9 ta ce: ‘Gama an kulle zantattukan, an hatimce su har kwanakin ƙarshe.’ Hakan ya nuna cewa ba za a fahimci waɗannan annabce-annabcen nan da nan ba, sai an shiga “kwanakin ƙarshe.” Ba da daɗewa ba, za mu yi nazari a kan dukan abubuwan da suka nuna cewa muna raye ne a waɗannan kwanakin.c
Jon: To za ka iya bayyana mini annabcin Daniyel ɗin?
Cameron: E to, bari mu gwada mu gani.
MAFARKIN NEBUCHADNEZZAR
Cameron: Bari mu soma da abin da Sarki Nebuchadnezzar ya gani a mafarkinsa. Bayan haka, sai mu tattauna ma’anar mafarkin.
Jon: To.
Cameron: A mafarkin da Nebuchanezzar ya yi, ya ga wani babban itace da tsawonsa ya kai sama. Sai ya ji wani mala’ikan Allah ya ce a sare itacen, amma kada a tuge gindinsa. Bayan “lokatai guda bakwai,” itacen zai sake girma.d Wannan annabcin ya soma cika ne a kan Sarki Nebuchadnezzar da kansa. Kamar wannan itacen da girmansa ya kai sama, Nebuchadnezzar babban sarki ne. Duk da haka, an tuge shi har tsawon “lokatai guda bakwai.” Ka tuna da yadda hakan ya faru?
Jon: A’a, na mance.
Cameron: Littafi Mai Tsarki ya ce Nebuchadnezzar ya haukace har tsawon lokatai bakwai ko kuma shekaru bakwai. Ya kasa yin sarauta a wannan lokacin. Amma a ƙarshen waɗannan lokatai bakwai, Nebuchadnezzar ya dawo cikin hankalinsa kuma ya ci gaba da sarauta.e
Jon: To, na fahimci bayaninka. Amma me ya haɗa wannan bayanin da Mulkin Allah da kuma shekara ta 1914?
Cameron: A taƙaice dai, wannan annabcin ya cika a hanyoyi biyu. A cikarsa na farko, an dakatar da mulkin Sarki Nebuchadnezzar. Cikarsa na biyu kuma ya shafi lokacin da aka dakatar da sarautar Allah. Saboda haka, wannan cika na biyun ne yake da nasaba da Mulkin Allah.
Jon: Ta yaya ka san cewa wannan annabcin yana da cika na biyu da ya shafi Mulkin Allah?
Cameron: Wannan annabcin da kansa ya bayyana hakan. Littafin Daniyel 4:17 ya nuna cewa an yi wannan annabcin ne don “masu-rai su sani Maɗaukaki yana riƙe da sarauta a cikin mulkin mutane, yana bayar ga wanda ya ga dama.” Shin ka lura da furucin nan “mulkin mutane”?
Jon: E, ayar ta ce “Maɗaukaki yana riƙe da sarauta a cikin mulkin mutane.”
Cameron: Haka ne. To a ganinka wane ne wannan ‘Maɗaukakin’?
Jon: Allah ne ko?
Cameron: Hakika. Hakan ya nuna mana cewa wannan annabcin bai cika a kan Nebuchadnezzar kaɗai ba. Annabcin ya kuma shafi “mulkin mutane,” wato sarautar Allah bisa ’yan Adam. Kuma idan muka sake bincika annabcin gaba ɗaya, za mu ga cewa wannan bayanin ya yi daidai.
Jon: Ban fahimce ka ba.
AINIHIN BATUN DA KE LITTAFIN DANIYEL
Cameron: Littafin Daniyel ya yi magana a kan batu guda sau da sau. Ya bayyana yadda Yesu Ɗan Allah zai soma sarauta a Mulkin Allah. Alal misali, mu ga abin da ke cikin Daniyel 2:44. Don Allah ka karanta mana.
Jon: To. Ayar ta ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar wa wata al’umma ba; amma za ya parpashe dukan waɗannan mulko ki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”
Cameron: Na gode. Shin kana ganin wannan ayar tana magana ne game da Mulkin Allah?
Jon: Kai, da ƙyar.
Cameron: Ka tuna cewa ayar ta ce wannan Mulkin zai “tsaya har abada.” To idan ba Mulkin Allah ba, kana ganin akwai gwamnatin ɗan Adam da za ta tsaya har abada?
Jon: Gaskiya kam babu.
Cameron: Wani annabci a littafin Daniyel da ya yi zancen Mulkin Allah kuma shi ne Daniyel 7:13, 14. Annabcin ya yi magana game da wani sarki da zai yi sarauta nan gaba cewa: ‘Aka ba shi sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa; sarautarsa madawwamiya ce, wanda ba za ta shuɗe ba, mulkinsa kuma wanda ba shi hallakuwa.’ Shin ka lura da wani abu a cikin wannan nassin da ke da nasaba da abin da muke tattaunawa?
Jon: E, nassin ya ambata wani mulki.
Cameron: Haka ne. Kuma ka lura cewa nassin ya ce wannan Mulkin zai mallaki “al’ummai, da dangogi, da harsuna.” Ma’ana, wannan Mulkin zai mallaki dukan duniya.
Jon: Ban taɓa sanin hakan ba, amma gaskiyarka ne.
Cameron: Ban da haka ma, ga abin da nassin ya sake faɗa: “Sarautarsa madawwamiya ce, wanda ba za ta shuɗe ba, mulkinsa kuma wanda ba shi hallakuwa.” Wannan annabcin ya yi daidai da wanda muka karanta a Daniyel 2:44, ko ba haka ba?
Jon: Haka ne fa.
Cameron: To, bari mu ɗan yi bitar abin da muka tattauna. An yi annabcin da ke Daniyel sura 4 ne don “masu-rai su sani Maɗaukaki yana riƙe da sarauta a cikin mulkin mutane.” Hakan ya nuna cewa annabcin bai cika a kan Nebuchadnezzar kaɗai ba, kuma a cikin littafin Daniyel gaba ɗaya, mun ga annabce-annabce dabam-dabam game da yadda Allah zai kafa wani Mulki ƙarƙashin Ɗansa. Shin kana ganin zai dace mu kammala cewa annabcin da ke Daniyel sura 4 ya shafi Mulkin Allah?
Jon: E, to. Amma har ila, ban ga yadda hakan ya shafi shekara ta 1914 ba.
“A BAR LOKATAI GUDA BAKWAI” SU WUCE
Cameron: Ka tuna cewa itacen da aka ambata a wannan nassin yana wakiltar Sarki Nebuchadnezzar ne. An dakatar da sarautarsa na tsawon lokatai bakwai sa’ad da ya haukace na ɗan lokaci. Waɗannan lokatan sun ƙare a lokacin da Nebuchadnezzar ya dawo cikin hankalinsa kuma ya koma gadon sarauta. A cikar annabcin na biyu, za a ɗan dakatar da sarautar Allah, amma hakan ba ya nufin cewa Allah ya kasa.
Jon: Me kake nufi?
Cameron: A zamanin Isra’ilawa, sarakunan da suke sarauta a Urushalima suna zama ne a “kursiyin Ubangiji.”f Suna yin mulki bisa mutanen Allah a madadinsa. Saboda haka, a duk lokacin da sarakunan suke sarauta, yana nan kamar Allah ne yake sarauta. Amma a kwana a tashi, yawancin sarakunan sun juya wa Allah baya kuma yawancin talakawansu suka bi su. A sakamakon haka, Allah ya bar Babiloniyawa su ci su da yaƙi a shekara ta 607 kafin zamaninmu. Tun wannan lokacin, ba a sake yin sarki a Urushalima da ya wakilci Jehobah ba. To yadda aka ɗan dakatar da sarautar Allah ke nan. Ka fahimci bayanin da na yi yanzu?
Jon: E.
Cameron: Bisa ga wannan bayanin, waɗannan lokatai bakwai sun soma ne a shekara ta 607 kafin zamaninmu, kuma lokacin da aka dakatar da sarautar Allah ke nan. A ƙarshen waɗannan lokatai bakwai, Allah zai naɗa sabon sarki a sama da zai wakilce Shi. Ta hakan ne sauran annabce-annabcen da muka karanta a littafin Daniyel za su cika. Amma ga wata tambaya: A yaushe ne waɗannan lokatai bakwai suka ƙare? Idan mun san amsar wannan tambayar, za mu iya sanin lokacin da Mulkin Allah ya soma sarauta.
Jon: Oho, haka ne? To bari in ce lokatai bakwai ɗin sun ƙare a shekara ta 1914.
Cameron: Gaskiyarka.
Jon: Amma ta yaya muka san hakan?
Cameron: A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, ya nuna cewa waɗannan lokatai bakwai ba su ƙare ba tukun.g Hakan ya nuna cewa lokatan za su ɗauki shekaru da yawa. Lokatai bakwai ɗin sun soma shekaru da yawa kafin Yesu ya zo duniya kuma ba su ƙare nan da nan bayan ya koma sama ba. Ka tuna cewa ba za a fahimci ma’anar annabcin da ke littafin Daniyel ba sai an shiga “kwanakin ƙarshe.”h Daga shekara ta 1870, wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi marmarin sanin ma’anar waɗannan annabce-annabcen kuma suka yi bincike a kansu sosai. Sai suka fahimci cewa lokatai bakwai ɗin za su ƙare a shekara ta 1914. Kuma abubuwan da suka faru a faɗin duniya daga shekara ta 1914 sun tabbatar da cewa a wannan shekara ce Mulkin Allah ya soma sarauta a sama. A shekarar nan ne muka shiga kwanaki na ƙarshe. Na san cewa mun tattauna abubuwa da yawa da za ka so ka yi tunani a kansu sosai.
Jon: Ƙwarai kuwa. Zan sake bincika wannan bayanin don in gane da kyau.
Cameron: Ko ni ma ya ɗauki lokaci kafin na fahimci waɗannan annabce-annabcen da yadda suka cika. Amma, ina fatan tattaunawar nan ta taimaka maka ka ga cewa koyarwar Shaidun Jehobah game da Mulkin Allah daga Littafi Mai Tsarki ne.
Jon: Sosai kuwa. Ai, yadda kuke bayyana imaninku daga Littafi Mai Tsarki yana burge ni sosai.
Cameron: Na lura cewa kai ma kana so ka yi imani da abin da ke Littafi Mai Tsarki. Kamar yadda na faɗa, za ka bukaci lokaci don ka yi tunani a kan abubuwan da muka tattauna yanzu. Na san wataƙila kana da wasu tambayoyi. Alal misali, mun riga mun gano cewa waɗannan lokatai bakwai sun shafi Mulkin Allah kuma sun soma ne a shekara ta 607 kafin zamaninmu. Amma, ta yaya muka san cewa sun ƙare a shekara ta 1914?i
Jon: Babu shakka, tambayar da nake so in yi ke nan.
Cameron: Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu san tsawon waɗannan lokatai bakwai. Za ka so mu tattauna hakan idan na sake zuwa?j
Jon: E, hakan zai yi kyau.
Ka taɓa tunanin wani abu da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai daga cikin Littafi Mai Tsarki? Za ka so ka ƙara sanin wasu daga cikin koyarwar Shaidun Jehobah ko kuma dalilin da ya sa suka yi imani da wasu abubuwa? Idan kana so, ka sami wata ko wani Mashaidin Jehobah da zai bayyana maka waɗannan batutuwan. Mashaidin zai yi farin cikin tattaunawa da kai.
a Shaidun Jehobah suna tattauna Littafi Mai Tsarki da maƙwabtansu a gidajensu kyauta ta wajen bin wani tsari na nazari.
b Misalai 2:3-5.
c Ka duba babi na 9 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.
d Daniyel 4:13-17.
e Daniyel 4:20-36.
f 1 Labarbaru 29:23.
g A cikin annabcinsa game da kwanaki na ƙarshe, Yesu ya ce: ‘Al’ummai za su tattake Urushalima [wadda ta wakilci sarautar Allah] . . . har zamanan Al’ummai su cika.’ (Luka 21:24) Saboda haka, an dakatar da sarautar Allah har zuwa zamanin Yesu, kuma hakan ya ci gaba har zuwa kwanaki na ƙarshe.
h Daniyel 12:9.
i Ka duba shafuffuka na 215-218 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Za ka iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.
j Talifi na gaba cikin wannan jerin talifofin zai tattauna Nassosin da suka yi bayani a kan tsawon waɗannan lokatai bakwai.