ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MULKIN ALLAH—TA YAYA ZAI AMFANE KA?
MULKIN ALLAH —Ta Yaya Zai Amfane Ka?
Mai yiwuwa daga bayanan da aka yi a talifofin baya, ka fahimci cewa Shaidun Jehobah suna ɗaukan Mulkin Allah da muhimmanci sosai. Wataƙila wasu daga cikin albarkun da aka bayyana cewa Mulkin Allah zai kawo nan gaba sun burge ka. Amma, kana iya ganin kamar da wuya waɗannan alkawuran su cika.
A gaskiya, maimakon ka gaskata da duk abin da ka ji haka kawai, zai dace ka yi hattara. (Misalai 14:15) Akwai wasu mutane a birnin Biriyaa ta dā da suka yi hattara kamarka. Sa’ad da suka ji bisharar Mulkin, sun ba da gaskiya, amma ba don sun so su yi hakan kawai ba. Maimakon haka, sun bincika Nassosi da kyau don “su gani ko waɗannan al’amura haka suke.” (Ayyukan Manzanni 17:11) Mutanen Biriya sun gwada bisharar da suka ji da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. A sakamakon haka, sun gaskata cewa bisharar daga Kalmar Allah ce.
Shaidun Jehobah suna ƙarfafa ka ka yi hakan kai ma. Nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi da mutane kyauta zai ba ka damar gwada abubuwan da Shaidun Jehobah suka gaskata game da Mulkin Allah da kuma koyarwar Littafi Mai Tsarki.
Ban da haka ma, yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka sami amsoshin tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa, kamar waɗanda ke gaba.
Ta yaya muka soma wanzuwa?
Mece ce manufar rayuwa?
Me ya sa Allah ya ƙyale mutane su sha wahala?
Me ke faruwa da mutum bayan ya mutu?
Za a hallaka duniya ne?
Me zai taimaka wa iyali ta zauna lafiya?
Mafi muhimmanci shi ne, yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka “kusato ga Allah.” (Yaƙub 4:8) Yayin da kake daɗa kusantar Allah, za ka ga yadda Mulkin Allah zai amfane ka a yanzu da kuma har abada. Yesu da kansa ma ya ambata cikin addu’a ga Ubansa cewa: ‘Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.’—Yohanna 17:3.
a Biriya wani birni ne a ƙasar Makidoniya ta dā.