Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 11/1 pp. 4-7
  • Mulkin Allah​—⁠Me Ya Sa Yake da Muhimmanci ga Yesu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mulkin Allah​—⁠Me Ya Sa Yake da Muhimmanci ga Yesu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA MULKIN ZAI YI WA UBAN YESU
  • ABIN DA MULKIN ZAI YI WA ’YAN ADAM MASU ADALCI
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 11/1 pp. 4-7

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MULKIN ALLAH—TA YAYA ZAI AMFANE KA?

Mulkin Allah ​—Me Ya Sa Yake da Muhimmanci ga Yesu?

Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, ya tattauna batutuwa da yawa. Alal misali, ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a da yadda za su faranta wa Allah rai da kuma yadda za su ji daɗin rayuwa. (Matta 6:5-13; Markus 12:17; Luka 11:28) Amma, batun da ya fi tattaunawa da mutane shi ne Mulkin Allah.—Luka 6:45.

Kamar yadda aka bayyana a talifi na baya, yin “wa’azi” da kuma shelar “bisharar Mulkin Allah” ne ya fi muhimmanci a rayuwar Yesu. (Luka 8:1) Ya ba da ƙarfi ga koyar da mutane game da Mulkin Allah, kuma ya yi ta yawo a cikin ƙasar Isra’ila gaba ɗaya yana yin hakan. An rubuta labarin hidimar Yesu a cikin littattafan Linjila huɗu, kuma a cikinsu an ambata Mulkin fiye da sau 100, yawanci daga furucin Yesu. Duk da haka, waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin furucin da Yesu ya yi game da Mulkin Allah!—Yohanna 21:25.

Me ya sa Mulkin ya kasance da muhimmanci ga Yesu sa’ad da yake duniya? Yesu ya san cewa Allah ya riga ya zaɓe shi ya zama Sarkin wannan Mulkin. (Ishaya 9:6; Luka 22:28-30) Amma Yesu bai shiga neman matsayi ko kuma ɗaukaka ba. (Matta 11:29; Markus 10:17, 18) Bai sanar da Mulkin domin amfanin kansa ba. Ainihi dai daga wancan lokacin zuwa yanzu, Yesu ya so Mulkin Allaha ne domin abin da Mulkin zai yi ma waɗanda Yesu yake ƙauna, wato Ubansa na samaniya da kuma mabiyansa amintattu.

ABIN DA MULKIN ZAI YI WA UBAN YESU

Yesu yana ƙaunar Ubansa na samaniya sosai. (Misalai 8:30; Yohanna 14:31) Yana son halayen Ubansa sosai, kamar su ƙauna da tausayi da kuma son gaskiya. (Kubawar Shari’a 32:4; Ishaya 49:15; 1 Yohanna 4:8) Saboda haka, Yesu ya tsani ya ji mutane suna yaɗa ƙarya game da Ubansa, cewa bai damu da wahalar da mutane suke sha ba kuma cewa yana so mu sha wahala. Amma, Yesu ya san cewa a kwana a tashi, Mulkin zai kawar da zargin da ake yi ma Ubansa. Hakan ne ya sa Yesu ya yi ɗokin yin shelar “bishara ta Mulkin.” (Matta 4:23; 6:9, 10) Ta yaya Mulkin zai kawar da zargin da ake yi ma Ubansa?

Jehobah zai yi amfani da wannan Mulkin ya yi gyara da za ta amfani ’yan Adam gabaki ɗaya. “Zai share dukan hawaye” daga idanun ’yan Adam masu aminci. Jehobah zai kawar da abubuwan da ke sa mutane zub da hawaye, kuma zai tabbata cewa “mutuwa . . . ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Ta wannan Mulkin, Allah zai kawo ƙarshen dukan wahalolin da ’yan Adam suke sha.b

Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Yesu ya yi ɗokin yin wa’azin Mulkin Allah! Yesu ya san cewa Mulkin zai nuna cewa Ubansa yana da iko da kuma jin ƙai sosai. (Yaƙub 5:11) Ban da haka ma, Yesu ya san cewa Mulkin zai amfani wasu kuma da yake ƙauna, wato ’yan Adam masu adalci.

ABIN DA MULKIN ZAI YI WA ’YAN ADAM MASU ADALCI

Yesu yana tare da Ubansa a sama da daɗewa kafin ya zo duniya. Uban ya halicci dukan abubuwa ta wurin Ɗansa. Waɗannan abubuwan sun ƙunshi samaniya mai ban al’ajabi cike da taurari da kyakkyawar duniyarmu da dukan abubuwan da ke cikinta. (Kolosiyawa 1:15, 16) Amma cikin dukan halittun nan, Yesu ya fi yin “murna da ’yan Adam” ne.—Misalai 8:31, Littafi Mai Tsarki.

Yadda Yesu ya yi hidimarsa ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam sosai. Tun somawar hidimarsa, ya sanar cewa ya zo duniya ne don ya “yi shelar bishara” ga mabukata. (Luka 4:18) Amma, Yesu bai taimaka wa mutane da baki kawai ba. Sau da sau ya yi abin da ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam. Alal misali, a lokacin da jama’a suka taru su saurare shi, Yesu ‘ya ji tausayinsu, ya warkar da marasa lafiya’ a cikinsu. (Matta 14:14) Sa’ad da wani mutum mai mummunar cuta ya ba da gaskiya cewa Yesu zai iya warkar da shi in Yesu ya so, sai Yesu ya nuna masa ƙauna. Saboda tausayi, Yesu ya ce masa: “Na yarda; ka tsarkaka,” kuma mutumin ya warke. (Luka 5:12, 13) Sa’ad da Yesu ya ga abokiyarsa Maryamu tana kukan mutuwar ɗan’uwanta Li’azaru, Yesu ya yi ‘nishi,’ “ya yi juyayi” kuma “ya yi hawaye.” (Yohanna 11:32-36, LMT) Sai Yesu ya yi wani abu mai ban al’ajabi, wato ya ta da Li’azaru wanda ya yi kwanaki huɗu da mutuwa!—Yohanna 11:38-44.

Hakika, Yesu ya san cewa taimakon da ya yi wa mutane ba zai dawwama ba. Ya san cewa ko ba jima ko ba daɗe, dukan waɗanda ya warkar da su za su sake rashin lafiya kuma dukan waɗanda ya tayar za su sake mutuwa. Amma Yesu ya san cewa Mulkin Allah zai kawo ƙarshen waɗannan matsalolin gabaki ɗaya. Hakan ne ya sa Yesu bai tsaya yin mu’ujiza kawai ba, amma ya yi shelar “bishara ta Mulkin” da ƙwazo sosai. (Matta 9:35) Mu’ujizojin da ya yi soma taɓi ne na abubuwan da Mulkin Allah zai yi a duniya ba da daɗewa ba. Ga wasu alkawuran da Littafi Mai Tsarki ya yi game da wannan lokacin.

  • Ba za a sake yin rashin lafiya ba.

    “Sa’an nan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe. Sa’an nan gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa, harshen bebe kuma za ya rera waƙa.” Ƙari ga haka, “wanda yake zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” —Ishaya 33:24; 35:5, 6.

  • Ba za a sake yin mutuwa ba.

    ‘Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.’—Zabura 37:29.

    “Ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” —Ishaya 25:8.

  • Mattatu za su sake rayuwa.

    “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29.

    “Za a yi tashin matattu.” —Ayyukan Manzanni 24:15.

  • Ba za a sake rasa aikin yi ko wurin kwana ba.

    “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; . . . Zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”—Ishaya 65:21, 22.

  • Ba za a sake yin yaƙi ba.

    “Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.”—Zabura 46:9.

    “Al’umma ba za ta zāre wa al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koyon yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:4.

  • Ba za a sake yin ƙarancin abinci ba.

    ‘Ƙasa tā ba da amfaninta: Allah wanda shi ke Allahnmu, za ya albarkace mu.’—Zabura 67:6.

    “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.”—Zabura 72:16.

  • Ba za a sake yin talauci ba.

    “Ba kullum za a manta da matalauta ba.”—Zabura 9:18.

    “Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: Matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi, za ya kuwa ceci rayukan matalauta.”—Zabura 72:12, 13.

Babu shakka bayan ka yi la’akari da waɗannan alkawura game da Mulkin, ka fahimci abin da ya sa Yesu ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai, ko ba haka ba? Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi zancen Mulkin da duk wanda ya saurare shi domin ya san cewa Mulkin zai kawo ƙarshen dukan matsalolin da ake fuskanta a yau.

Shin, waɗannan alkawura da Littafi Mai Tsarki ya yi game da Mulkin suna da ban sha’awa a gare ka kuwa? Idan haka ne, ta yaya za ka daɗa koya game da Mulkin? Mene ne za ka iya yi don ka amfana daga albarkun da Mulkin zai kawo? Talifi na ƙarshe cikin wannan jerin talifofin zai amsa waɗannan tambayoyin.

a Yesu yana sama, kuma tun komawarsa sama, Mulkin ya ci gaba da kasancewa da muhimmanci a gare shi.—Luka 24:51.

b Don bayani a kan dalilin da ya sa Allah ya ƙyale ’yan Adam suke shan wahala, ka duba babi na 11 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.pr418.com/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba