Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Maris pp. 20-25
  • Mu Riƙa Yin Tafiya Cikin Bangaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Riƙa Yin Tafiya Cikin Bangaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SAꞌAD DA MUKE ZAƁAN AIKIN DA ZA MU YI
  • SAꞌAD DA MUKE NEMAN WANDA ZA MU AURA
  • SAꞌAD DA ƘUNGIYARMU TA BA MU UMURNI
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ta Yaya Za Ka Kau da Shakka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Maris pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 12

WAƘA TA 119 Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

Mu Riƙa Yin Tafiya Cikin Bangaskiya

“Tafiyar bangaskiya muke yi, ba bisa ga abin da muke gani da ido ba.”—2 KOR. 5:7.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu bi ja-gorancin Jehobah idan muna so mu tsai da shawarwari masu muhimmanci.

1. Me ya sa manzo Bulus ya yi farin ciki da ya yi tunani a kan rayuwarsa?

DUK da cewa manzo Bulus ya san cewa za a kashe shi, ya yi farin ciki sosai da ya yi tunani a kan irin rayuwar da ya yi. Ya ce: “Na kuma yi tserena har ga ƙarshe, na kuma riƙe amanar bangaskiyar.” (2 Tim. 4:​6-8) Bulus ya yanke shawarar yin amfani da rayuwarsa don bauta wa Jehobah, wannan shawara ce mai kyau. Kuma ya kasance da tabbaci cewa Jehobah na alfahari da shi. Mu ma idan mun yake shawarwari masu kyau, Jehobah zai yi alfahari da mu. Ta yaya za mu yi hakan?

2. Me ake nufi da yin tafiya cikin bangaskiya?

2 Saꞌad da Bulus yake magana game da kansa da wasu amintattun Kiristoci ya ce: “Tafiyar bangaskiya muke yi, ba bisa ga abin da muke gani da ido ba.” (2 Kor. 5:7) Mene ne Bulus yake nufi? A wasu lokuta a Littafi Mai Tsarki, kalmar nan ‘tafiya’ tana nufin irin rayuwar da mutum yake yi. Mutanen da ba su da bangaskiya, wato waɗanda ba sa dogara ga Jehobah, sukan yanke shawarwari bisa abubuwan da suke gani da abubuwan da suke ji ne kawai. Amma, idan mutum yana da bangaskiya, zai tsai da shawarwarin da suka nuna cewa yana dogara ga Jehobah. Mutumin yana da tabbaci cewa idan ya bi shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki, zai yi rayuwa mai kyau yanzu kuma Jehobah zai albarkace shi sosai a nan gaba.—Zab. 119:66; Ibran. 11:6.

3. Idan muna tafiya cikin bangaskiya, ta yaya za mu amfana? (2 Korintiyawa 4:18)

3 A wasu lokuta, dukanmu mukan yanke shawarwari bisa abubuwan da muke gani da abubuwan da muke ji. Amma idan muna tsai da shawarwari bisa abubuwan da muke gani da kuma ji ne kawai, ba mamaki mu yi kurakurai. Me ya sa? Domin ba lallai ne abubuwan da muke gani da kuma ji su zama daidai ba. Ko da a ce abubuwan daidai ne, idan muka tsai da shawarwari bisa ga abubuwan nan kawai, za su iya sa mu yi abin da Jehobah ba ya so. (M. Wa. 11:9; Mat. 24:​37-39) Amma idan muka tsai da shawarwari da suka nuna cewa muna da bangaskiya, za mu tsai da shawarwarin da za su “gamshi Ubangiji.” (Afis. 5:10) Bin abin da Allah ya faɗa zai ba mu kwanciyar rai kuma za mu yi farin ciki sosai. (Zab. 16:​8, 9; Isha. 48:​17, 18) Ban da haka ma, idan muna tafiya cikin bangaskiya, za mu yi rayuwa har abada.—Karanta 2 Korintiyawa 4:18.

4. Idan mutum yana so ya san bisa mene ne yake yanke shawarwari, mene ne zai dace ya yi?

4 Zai dace dukanmu mu tambayi kanmu cewa: Bisa ga mene ne nake yanke shawarwari? Bisa ga abubuwan da nake gani ne kawai? Ko bisa ga abin da Jehobah yake so? A talifin nan, za mu tattauna yadda bangaskiya za ta taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau a yanayoyin nan: saꞌad da muke zaɓan aikin da za mu yi, da saꞌad da muke neman wanda za mu aura, da kuma saꞌad da ƙungiyarmu ta ba mu umurni. A kowane yanayi, za mu tattauna abubuwan da ya kamata mu yi tunani a kai don mu iya yanke shawarwari masu kyau.

SAꞌAD DA MUKE ZAƁAN AIKIN DA ZA MU YI

5. Me muke tunani a kai idan muna so mu zaɓi aikin da za mu yi?

5 Dukanmu muna son aikin da zai taimaka mana mu iya biyan bukatunmu da na iyalinmu. (M. Wa. 7:12; 1 Tim. 5:8) Wasu ayyukan suna da albashi mai tsoka. Irin waɗannan ayyukan za su iya taimaka wa mutum ya biya bukatunsa na yau da kullum, har ya yi ajiya don nan gaba. Amma wasu ayyukan, albashinsu kaɗan ne, kuma irin ayyukan nan za su iya taimaka wa mutum ya iya biyan bukatun da suka fi muhimmanci ne kawai, kamar abinci da riguna da wurin kwana. Babu shakka, idan muna so mu zaɓi aikin da za mu yi, muna ƙoƙari mu san nawa za a biya mu. Amma idan mutum yana mai da hankali ga albashin ne kawai, hakan ya nuna cewa yana yanke shawarwari bisa abin da yake gani ne.

6. Ta yaya za mu nuna cewa muna tafiya cikin bangaskiya idan muna so mu zaɓi aikin da za mu yi? (Ibraniyawa 13:5)

6 Idan muna tafiya cikin bangaskiya, za mu duba yadda aikin zai shafi dangantakarmu da Jehobah. Zai dace mu tambayi kanmu: ‘Aikin zai sa in yi abubuwan da Jehobah ba ya so?’ (K. Mag. 6:​16-19) ‘Aikin zai shafi ayyukan ibadan da nake yi, ko zai sa in bar iyalina na dogon lokaci?’ (Filib. 1:10) Idan amsar kowace tambayar nan e ce, zai fi kyau kada mu yi aikin, ko da samun aiki na da wuya. Idan muna tafiya cikin bangaskiya, za mu yanke shawarwarin da za su nuna cewa muna da tabbacin cewa Jehobah zai biya mana bukatunmu.—Mat. 6:33; karanta Ibraniyawa 13:5.

7-8. Ta yaya wani ɗanꞌuwa mai suna Javier ya nuna cewa ya san muhimmancin tafiya cikin bangaskiya? (Ka kuma duba hoton.)

7 Wani ɗanꞌuwa daga Kudancin Amurka mai suna Javier,a ya nuna cewa ya san muhimmancin tafiya cikin bangaskiya. Ya ce: “Na nemi a ƙara min matsayi a wurin aiki da zai ninka albashina sau biyu kuma ya sa in ji daɗin rayuwa.” Amma Ɗanꞌuwa Javier yana so ya yi hidimar majagaba. Ya ci-gaba da cewa: “An shirya in haɗu da manajan. Amma kafin ya yi mini intabiyu, na roƙi Jehobah ya taimaka mini don na san cewa ya san abin da na fi so. Na so in sami babban matsayi da za a biya ni albashi mai tsoka, amma ba na son matsayin idan zai hana ni cim ma maƙasudaina.”

8 Javier ya ƙara da cewa: “Manajan ya gaya mini cewa, zan riƙa yin aiki har a lokacin da an tashi. Sai na gaya masa cewa ba zan iya yin hakan ba domin ayyukan ibadata.” A ƙarshe, Javier bai karɓi aikin ba. Mako biyu bayan haka, ya soma hidimar majagaba. ꞌYan watanni bayan haka, ya sami wani aiki da ba ya bukatar ya riƙa yi kullum. Ya ce: “Jehobah ya ji adduꞌata kuma ya sa na sami aikin da zai ba ni damar yin hidimata. Ina matukar farin ciki don aikin da nake yi yana ba ni damar bauta wa Jehobah da kyau da kuma taimaka wa ꞌyanꞌuwa.”

Wani ɗanꞌuwa sanye da overall yana riƙe da hular kwano. Da shi da ogansa sun je wani ofishi da babu kowa. Ogan yana so ya ƙara mai matsayi a wurin aiki.

Idan an ƙara maka matsayi a wurin aiki, me za ka yi? Za ka yi zaɓin da zai nuna cewa ka dogara ga Jehobah da tabbacin cewa zai kula da kai? (Ka duba sakin layi na 7-8)


9. Mene ne ka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Trésor?

9 Me ya kamata mu yi idan muka ga cewa aikinmu yana sa ayyukan ibada su yi mana wuya? Labarin Ɗanꞌuwa Trésor, daga Congo zai taimaka mana. Ya ce: “Ina matukar son sabon aikin da na samu. Albashina ya ninka wanda nake karɓa a dā sau uku, kuma mutane suna daraja ni sosai.” Amma, Ɗanꞌuwa Trésor yana yawan fasa taro domin yana aiki har a lokacin da aka tashi. Kuma ana matsa masa ya yi ƙarya game da wasu abubuwa marar kyau da ake yi a wurin aikinsu. Trésor ya so ya bar aikin, amma ya damu don bai san ko zai sake samun wani aiki ba. Me ya taimaka masa? Ya ce: “Habakkuk 3:​17-19 ya taimaka mini in san cewa Jehobah zai kula da ni ko da na daina aikin kuma ba na samun yawan kuɗin da nake samuwa. Don haka, na bar aikin.” Ya kammala da cewa: “Mutane da yawa suna ganin idan mutum ya sami aikin da ake biyan sa albashi mai tsoka, zai iya saɗaukar da kome, har da lokacin da yake kasancewa da iyalinsa da kuma na ibada. Amma ina farin ciki cewa na kāre dangantakata da Jehobah da iyayena da kuma ꞌyanꞌuwana. Bayan shekara ɗaya, Jehobah ya taimaka min in sami wani aiki da ke ba ni damar yin ayyukan ibada da kuma biyan bukatuna. Idan muka sa bautar Jehobah farko a rayuwarmu, mai yiwuwa, ba za mu zama da kuɗi da yawa ba amma Jehobah zai kula da mu.” A gaskiya, idan muka gaskata da alkawuran Jehobah kuma muka bi ja-gorancinsa, za mu ci-gaba da tsai da shawarwarin da za su nuna cewa muna da bangaskiya, kuma Jehobah zai albarkace mu.

SAꞌAD DA MUKE NEMAN WANDA ZA MU AURA

10. Saꞌad da muke neman wanda za mu aura, me zai nuna cewa muna yanke shawarwari bisa abin da muke gani?

10 Aure kyauta ce daga wurin Jehobah kuma ba laifi ba ne idan mutum yana so ya yi aure. A ce wata ꞌyarꞌuwa tana so ta auri wani ɗanꞌuwa, za ta yi tunani game da kyaunsa, da yadda yake yin abubuwa, da yadda mutane suke ɗaukan sa, da yadda yake bi da kuɗi, da yadda yake sa ta ji. Kuma za ta so ta san ko shi ne yake da hakkin kula da ꞌyan gidansu.b Sanin waɗannan abubuwan yana da muhimmanci. Amma, idan su ne kawai take tunani a kai, hakan na iya nuna cewa tana yanke shawarwari bisa abin da take gani ne.

11. Ta yaya za mu yi tafiya cikin bangaskiya idan muna neman wanda za mu aura? (1 Korintiyawa 7:39)

11 Jehobah yana alfahari da ꞌyanꞌuwa maza da mata da suke bin shawarwarin da ya bayar idan suna neman wanda za su aura! Alal misali, sukan bi shawarar da ta ce su jira har sai sun wuce “lokacin da shaꞌawar yin jimaꞌi yake da ƙarfi sosai” kafin su soma tunanin yin aure. (1 Kor. 7:​36, NWT) Sukan tabbatar cewa wanda suke so su aura yana da halayen da Jehobah yake so miji ko macen kirki ta kasance da su. (K. Mag. 31:​10-13, 26-28; Afis. 5:33; 1 Tim. 5:8) Ƙari ga haka, idan wani da ba ya bauta wa Jehobah ya ce yana son su, ba za su amince ba. Maimakon haka, za su bi shawarar da ke 1 Korintiyawa 7:39. (Karanta.) Wurin ya ce su auri “mai bin Ubangiji” kawai. Suna yin hakan ne domin suna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka musu.—Zab. 55:22.

12. Mene ne ka koya daga labarin ꞌYarꞌuwa Rosa?

12 Ka yi laꞌakari da labarin ꞌYarꞌuwa Rosa, da take hidimar majagaba a Kolombiya. Aikin da take yi ya sa tana yawan haɗuwa da wani mutum da ba Mashaidi ba, kuma mutumin ya soma nuna mata yana son ta. ꞌYarꞌuwa Rosa ma ta so mutumin. Ta ce: “A gani na shi mutumin kirki ne. Yana taimaka wa mutane a wurin da yake zama, ba ya shan taba ko ƙwaya kuma ba ya buguwa da giya. Ina jin daɗin yadda yake bi da ni. Yana da dukan halayen da nake so mijina ya kasance da su, sai dai shi ba Mashaidi ba ne.” Ta ci-gaba da cewa: “Ya yi mini wuya sosai in gaya masa cewa ba za mu iya yin soyayya ba. A lokacin na kaɗaita kuma na so in yi aure, amma ban sami ɗanꞌuwan da nake so in aura ba.” Duk da haka, Rosa ba ta mai da hankali ga abin da take gani kawai ba. Kuma ta yi tunani a kan yadda shawarar da za ta yanke zai shafi dangantakarta da Jehobah. Don haka, ta daina maꞌamala da mutumin kuma ta duƙufa a yin ayyukan ibada. Ba da daɗewa ba, an gayyace ta zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki, kuma yanzu ita majagaba na musamman ce. Rosa ta ce: “Jehobah ya albarkace ni sosai kuma hakan ya sa ni farin ciki ba kaɗan ba.” A wasu lokuta, bai da sauƙi mu yi abin da Jehobah yake so mu yi, musamman idan abu ne da muke so sosai. Amma za mu amfana idan mun bi shawarwarin da Jehobah yake ba mu.

SAꞌAD DA ƘUNGIYARMU TA BA MU UMURNI

13. A wasu lokuta, yaya za mu iya ji idan aka ba mu umurni a ƙungiyarmu?

13 Dattawa, da masu kula da daꞌira, da reshen ofishinmu, da kuma Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, suna yawan ba mu umurnan da za su taimaka mana mu bauta wa Jehobah. Amma a wasu lokuta, ba za mu fahimci dalilin da ya sa suka ba mu wani umurni ba. Ƙila ma mu ga kamar bin umurnin zai iya jawo mummunar sakamako. Ko kuma mu mai da hankali ga kurakuran ꞌyanꞌuwan da suka ba da umurnin.

14. Me zai taimaka mana mu bi umurnan da ƙungiyar Jehobah take ba mu? (Ibraniyawa 13:17)

14 Idan muna da bangaskiya, za mu gaskata cewa Jehobah ne yake yi wa ƙungiyarsa ja-goranci, kuma ya san duk yanayin da muke ciki. Hakan zai sa mu yi saurin yin biyayya, kuma mu yi hakan da zuciya ɗaya. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) Gaskiyar ita ce, idan mun bi umurnin da aka ba mu, ikilisiyarmu za ta kasance da haɗin kai. (Afis. 4:​2, 3) Duk da cewa ꞌyanꞌuwan da suke ba mu umurnai ajizai ne, mun san cewa idan mun amince da abin da suke faɗa, Jehobah zai albarkace mu. (1 Sam. 15:22) Mun kuma san cewa idan ana bukata a yi canje-canje, Jehobah zai sa a yi hakan a lokacin da ya dace.—Mik. 7:7.

15-16. Mene ne ya taimaka ma wani ɗanꞌuwa ya yi tafiya cikin bangaskiya duk da cewa yana shakkar umurnin da aka ba su? (Ka kuma duba hoton.)

15 Ga wani labarin da ya nuna amfanin da za mu samu idan muka kasance da bangaskiya kuma muka bi umurnin da ƙungiyarmu ta bayar. A ƙasar Peru, an fi yin Sifanisanci, amma yawancin mutanen suna da nasu yaren. Ɗaya daga cikin yaren shi ne Quechua. ꞌYanꞌuwa sun yi shekaru suna neman waɗanda suke yin yaren nan a yankinsu. Amma an yi wasu canje-canje a yadda za su riƙa yin waꞌazi don a bi umurnin gwamnati. (Rom. 13:1) A sakamakon haka, wasu ꞌyanꞌuwa sun ɗauka cewa ba za a sami ci-gaba ba. A ƙarshe, ꞌyanꞌuwan sun yi biyayya ga umurnin, kuma Jehobah ya albarkace su sun sami mutane da yawa da ke yaren Quechua.

16 Wani dattijo mai suna Kevin da ke ikilisiyar da ake yin yaren Quechua yana cikin waɗanda suka damu. Ya ce: “Na tambayi kaina cewa, ‘Ta yaya za mu sami mutanen da ke yaren Quechua?’” Mene ne ya taimaka wa Kevin? Ya ce: “Na yi tunani a kan abin da ke Karin Magana 3:5. Kuma hakan ya sa na tuna da labarin Musa. Jehobah ya ba shi umurnin da mutum zai iya gani kamar bai dace ba. Ya gaya masa cewa ya bi da Israꞌilawa ta Jar Teku, inda ya yi kamar ba za su iya kuɓuce wa Masarawan da ke bin su ba. Duk da haka, Musa ya yi biyayya kuma Jehobah ya albarkace shi ta wajen yin wani abin ban mamaki don ya cece su.” (Fit. 14:​1, 2, 9-11, 21, 22) Hakan ya sa Kevin ya bi umurnin da aka ba su. Wane sakamako ne ya samu? Ya ce: “Yadda Jehobah ya albarkace mu ya ba ni mamaki. A dā, muna tafiya sosai idan muna waꞌazi, kuma ƙarshenta sai mu sami mutum ɗaya ko biyu ne kawai da suke yaren Quechua. Amma yanzu muna zuwa wuraren da akwai masu yin yaren Quechua da yawa. A sakamakon haka, muna samun mutane da yawa da suke sauraran mu, da kuma waɗanda suke so mu dawo mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Ban da haka ma, mun sami ƙaruwa a yawan mutanen da suke zuwa taronmu.” Babu shakka, idan muna tafiya cikin bangaskiya, Jehobah zai albarkace mu.

Wani mutum da ke yaren Quechua yana magana da maꞌaurata da ke waꞌazi. Yana nuna musu inda wani yake zama.

Mutane da yawa sun gaya wa ꞌyanꞌuwan inda za su sami masu yin yaren Quechua a yankin (Ka duba sakin layi na 15-16)


17. Mene ne ka koya daga wannan talifin?

17 A talifin nan, mun ga yadda za mu yanke shawarwari bisa abin da Jehobah yake so a hanyoyi uku. Amma ba shi ke nan ba. Muna bukatar mu ci-gaba da yanke shawarwari bisa abin da Jehobah yake so a dukan fannonin rayuwa, kamar a lokacin da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi, ko yawan karatun boko da za mu yi da kuma yadda za mu reni ꞌyaꞌyanmu. A duk lokacin da muke so mu yanke wata shawara, bai kamata mu yi hakan bisa abin da muke gani kawai ba, amma ya kamata mu yi tunanin yadda hakan zai shafi dangantakarmu da Jehobah, mu bi shawarar da yake ba mu, mu kuma gaskata da alkawarin da ya yi cewa zai kula da mu. Idan mun yi hakan, za mu yi tafiya da “Yahweh Allahnmu har abada abadin.”—Mik. 4:5.

TA YAYA BANGASKIYA ZA TA TAIMAKA MANA MU YANKE SHAWARWARI MASU KYAU . . .

  • saꞌad da muke zaɓan aikin da za mu yi?

  • saꞌad da muke neman wanda za mu aura?

  • saꞌad da ƙungiyarmu ta ba mu umurni?

WAƘA TA 156 Mu Zama da Bangaskiya

a An canja wasu sunayen.

b Don bayanin ya zo da sauƙi a sakin layin nan, an yi magana ne game da ꞌyarꞌuwar da take neman wanda za ta aura. Amma ɗanꞌuwan da yake neman wadda zai aura ma zai amfana daga shawarar.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba