TALIFIN NAZARI NA 14
WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu
“Ku Zaɓi Wanda Za Ku Bauta Masa”
“Da ni da gidana, Yahweh ne za mu bauta masa.”—YOSH. 24:15.
ABIN DA ZA MU KOYA
Talifin nan zai tuna mana dalilan da suka sa muka zaɓi mu bauta wa Jehobah.
1. Me muke bukata mu yi idan muna so mu yi farin ciki na gaske, kuma me ya sa? (Ishaya 48:17, 18)
UBANMU na sama yana ƙaunarmu sosai, kuma yana so mu ji daɗin rayuwa yanzu da kuma a nan gaba. (M. Wa. 3:12, 13) Allah ya halicce mu da baiwa iri-iri, amma bai ba mu ikon yi wa kanmu ja-goranci ko ikon zaɓa wa kanmu abin da ya dace da wanda bai dace ba. (M. Wa. 8:9; Irm. 10:23) Jehobah ya san cewa idan muna so mu yi farin ciki na gaske, muna bukata mu bauta masa kuma mu yi masa biyayya.—Karanta Ishaya 48:17, 18.
2. Mene ne Shaiɗan yake so mu gaskata da shi, kuma mene ne Jehobah ya yi?
2 Shaiɗan yana so mu gaskata cewa za mu iya yin farin ciki ba tare da mun bauta wa Jehobah ba, da kuma cewa ꞌyanꞌadam za su iya yi wa kansu ja-goranci kuma su yi nasara. (Far. 3:4, 5) Don Jehobah ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, ya ƙyale ꞌyanꞌadam su mallaki kansu na ɗan lokaci. A yanzu muna gani sarai cewa mulkin ɗanꞌadam bai yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da labaran maza da mata da suka yi farin ciki don sun bauta wa Jehobah. Wanda ya fi farin ciki a cikinsu, shi ne Yesu Kristi. Da farko, bari mu ga dalilan da suka sa Yesu ya zaɓi ya bauta wa Jehobah. Bayan haka, za mu ga dalilin da ya sa Ubanmu na sama ya cancanci mu bauta masa. A ƙarshe kuma, za mu ga wasu dalilan da suka sa muka zaɓi mu bauta wa Jehobah.
DALILAN DA SUKA SA YESU YA ZAƁI YA BAUTA WA JEHOBAH
3. Mene ne Shaiɗan ya ce zai ba wa Yesu, kuma wane zaɓi ne Yesu ya yi?
3 Saꞌad da Yesu yake duniya, ya sami damar zaɓan wanda zai bauta wa. Jim kaɗan bayan Yesu ya yi baftisma, Shaiɗan ya ce zai ba shi dukan mulkokin duniya idan ya yi masa sujada. Amma Yesu ya ce masa: “Tafi daga nan kai Shaiɗan! Gama a rubuce yake cewa, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa.’” (Mat. 4:8-10) Me ya sa Yesu ya zaɓi ya bauta wa Jehobah? Bari mu ga wasu dalilai.
4-5. Waɗanne dalilai ne suka sa Yesu ya zaɓi ya bauta wa Jehobah?
4 Ainihin abin da ya sa Yesu ya zaɓi ya bauta wa Jehobah shi ne domin yana ƙaunar sa sosai. (Yoh. 14:31) Ƙari ga haka, Yesu yana bauta wa Jehobah domin abin da ya kamata ya yi ke nan. (Yoh. 8:28, 29; R. Yar. 4:11) Ya san cewa Jehobah ne Mahaliccin kome da kome, shi ne ya ba mu rai, za mu iya dogara gare shi, kuma shi mai alheri ne sosai. (Zab. 33:4; 36:9; Yak. 1:17) Dukan abubuwan da Jehobah ya gaya wa Yesu gaskiya ne kuma shi ne ya ba shi dukan abubuwan da yake da su. (Yoh. 1:14) Amma ba haka Shaiɗan yake ba. Ya sa ꞌyanꞌadam sun zama masu zunubi kuma sun soma mutuwa. Shi maƙaryaci ne, mai haɗama, kuma mai son kai. (Yoh. 8:44) Da yake Yesu ya san Jehobah sosai kuma ya san Shaiɗan, bai so ya zama kamar Shaiɗan wanda ya yi wa Jehobah tawaye ba.—Filib. 2:5-8.
5 Wani dalili kuma da ya sa Yesu ya zaɓi ya bauta wa Jehobah shi ne don sakamako masu kyau da yin hakan zai jawo. (Ibran. 12:2) Yesu ya san cewa idan ya riƙe amincinsa, hakan zai tsarkake sunan Allah kuma zai sa a kawo ƙarshen zunubi da mutuwa.
DALILIN DA YA SA YA KAMATA MU BAUTA WA JEHOBAH
6-7. Me ya sa mutane da yawa a yau ba sa bauta wa Jehobah, amma me ya sa Jehobah ya cancanci mu bauta masa?
6 Mutane da yawa a yau ba sa bauta wa Jehobah domin ba su san game da halayensa masu kyau ba, kuma ba su san abubuwa da yawa da ya yi domin su ba. Manzo Bulus ya haɗu da irin mutanen a Atina kuma ya yi musu waꞌazi.—A. M. 17:19, 20, 30, 34.
7 Bulus ya gaya musu cewa akwai Allah na gaskiya wanda “shi ne yake ba dukan mutane rai, da numfashi da dukan abubuwan da suke bukata.” Ya kuma ƙara da cewa: “Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance.” Allah ne Mahalicci, wanda “ya halicci dukan alꞌumma daga mutum guda,” don haka wajibi ne mu bauta masa shi kaɗai.—A. M. 17:25, 26, 28.
8. Mene ne Jehobah ba zai taɓa yi ba? Ka bayyana.
8 Da yake Jehobah ne Mahalicci da kuma Mai Iko Duka bisan dukan duniya, da yana so, da zai iya tilasta wa mutane su bauta masa. Amma Jehobah ba zai taɓa yin hakan ba. A maimakon haka, yana ba mu abubuwa da dama da suka nuna cewa yana nan kuma yana ƙaunar kowannenmu. Idan zai yiwu, yana son dukan mutane su zama abokansa har abada. (1 Tim. 2:3, 4) Shi ya sa Jehobah yana koya mana yadda za mu koyar da mutane game da nufinsa da kuma abubuwan da zai yi wa ꞌyanꞌadam. (Mat. 10:11-13; 28:19, 20) Ƙari ga haka, ya sa mu kasance cikin ikilisiyoyin da za mu iya bauta masa kuma mu sami taimako daga wurin dattawa masu ƙauna.—A. M. 20:28.
9. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar dukan ꞌyanꞌadam?
9 Jehobah yana nuna cewa yana ƙaunar dukan ꞌyanꞌadam ta wajen ba su abubuwa masu kyau har da waɗanda ba su yi imani da shi ba. Alal misali, biliyoyin mutane sun yi duban shekaru suna yin abin da suka ga dama maimakon su yi wa Jehobah biyayya. Duk da haka, Jehobah ya ci gaba da ba su abin da suke bukata don su rayu kuma su ji daɗi. (Mat. 5:44, 45; A. M. 14:16, 17) Ya ba su damar ƙaunar mutane kuma su ƙulla dangantaka, da damar samu nasu iyali da haifan yara, da yin aiki, kuma su ji daɗin rayuwa. (Zab. 127:3; M. Wa. 2:24) Babu shakka, Jehobah yana ƙaunar dukan mutane. (Fit. 34:6) Yanzu bari mu ga wasu dalilan da suka sa muka zaɓi mu bauta wa Jehobah, da kuma yadda yake albarkar waɗanda suke bauta masa.
ABIN DA YA SA MUKE BAUTA WA JEHOBAH
10. (a) Wane muhimmin dalili ne ya sa muke bauta wa Jehobah? (Matiyu 22:37) (b) Ta yaya ka amfana don yadda Jehobah yake gafartawa? (Zabura 103:13, 14)
10 Kamar Yesu, mu ma muna bauta wa Jehobah domin muna ƙaunar sa da dukan zuciyarmu. (Karanta Matiyu 22:37.) Sanin halayen Jehobah masu kyau suna sa mu ƙara kusantar sa. Alal misali, Jehobah yana a shirye ya gafarta mana a koyaushe. A lokacin da Israꞌilawa suka yi masa rashin biyayya, ya roƙe su ya ce: “Sai kowa ya juya daga muguwar hanyarsa.” (Irm. 18:11) Jehobah ya san cewa mu ajizai ne. (Karanta Zabura 103:13, 14.) Idan ka yi tunani a kan yawan lokutan da Jehobah ya gafarta maka, hakan zai sa ka so bauta masa har abada. Ko ba haka ba?
11. Waɗanne dalilai ne kuma suke sa mu bauta wa Ubanmu na sama?
11 Wani dalili kuma da ya sa muke son bauta wa Jehobah shi ne domin abin da ya kamata mu yi ke nan. (Mat. 4:10) Ƙari ga haka, mun san cewa idan muka ci gaba da bauta wa Jehobah, hakan zai jawo sakamako masu kyau. Wato, za mu tsarkake sunan Jehobah, za mu nuna cewa Iblis maƙaryaci ne kuma mu sa Ubanmu farin ciki. Ban da haka ma, idan muka bauta wa Jehobah yanzu, hakan zai ba mu damar bauta masa har abada!—Yoh. 17:3.
12-13. Mene ne muka koya daga labarin Jane da Pamela?
12 Tun muna yara, za mu iya ƙaunar Jehobah sosai, kuma ƙaunar da muke masa zai iya ci gaba da ƙaruwa. Abin da ya faru da Jane da ꞌyarꞌuwarta Pamelaa ke nan. A lokacin da suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, Jane tana shekara 11, Pamela kuma 10. Ko da yake iyayensu ba sa nazari, sun amince Jane da Pamela su yi nazari da Shaidun Jehobah muddin za su riƙa zuwa coci tare da su a ƙarshen maƙo. Jane ta ce: “Abin da Shaidun Jehobah suka koya min daga Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka min in guji shan ƙwayoyi da yin lalata kamar yadda yawancin ꞌyan makarantarmu suke yi.”
13 Bayan ꞌyan shekaru, su biyun sun zama masu shela. Daga baya, sun soma hidimar majagaba kuma suna kula da iyayensu da suka tsufa. Jane ta bayyana yadda take ji game da abubuwan da Jehobah ya yi musu, ta ce: “Na koyi cewa Jehobah yana kula da abokansa a koyaushe, kuma kamar yadda 2 Timoti 2:19 ta ce, Jehobah ‘ya san waɗanda suke nasa.’” Babu shakka, Jehobah yana kula da waɗanda suke ƙaunar sa kuma suke bauta masa!
14. Ta yaya za mu kāre sunan Jehobah? (Ka kuma duba hotunan.)
14 Muna so mutane su san gaskiya game da Jehobah. Alal misali, a ce kana da wani aboki mai kirki, mai bayarwa hannu sake, da kuma mai gafartawa. Sai wata rana, ka ji wani yana cewa abokinka, mugu ne kuma shi maƙaryaci ne. Me za ka yi? Babu shakka za ka kāre shi. Haka ma, idan muka ji mutane suna maganganun karya game da Jehobah, mukan kāre sunansa ta wajen gaya musu gaskiya. (Zab. 34:1; Isha. 43:10) Muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu bauta masa ta wurin abubuwan da muke faɗa da kuma yi.
Za ka taimaka wajen kāre suna Jehobah kuwa? (Ka duba sakin layi na 14)b
15. Ta yaya manzo Bulus ya amfana don canje-canjen da ya yi a rayuwarsa? (Filibiyawa 3:7, 8)
15 Muna shirye mu yi canje-canje a rayuwarmu don mu faranta wa Jehobah rai, ko kuma don mu ƙara ƙwazo a hidimarmu. Alal misali, manzo Bulus yana da babban matsayi a addinin Yahudawa, amma ya bar kome don ya bi Kristi kuma ya bauta wa Jehobah. (Gal. 1:14) Hakan ya sa ya yi rayuwa mai kyau yayin da yake bauta wa Jehobah kuma zai yi mulki tare da Yesu a sama. Bai taɓa yin da na sani don ya bauta wa Jehobah ba. Mu ma idan muka bauta wa Jehobah, ba za mu taɓa yin da na sani ba.—Karanta Filibiyawa 3:7, 8.
16. Me muka koya daga labarin Julia? (Ka kuma duba hotunan.)
16 Idan muka mai da hankali ga bautar Jehobah da dukan zuciyarmu, zai albarkace mu yanzu da kuma a nan gaba. Bari mu bincika labarin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Julia. Saꞌad da Julia take ƙarama, takan rera waƙa a cocinsu. Ta iya waƙa sosai har ma aka soma koya mata yadda za ta zama mawaƙiyar da ta ƙware. Nan da nan Julia ta zama sananniya kuma ta soma rera waƙoƙi a manyan wurare. Saꞌad da take koyan waƙa a wani sanannen makarantar da ake koyar da waƙa, wani ɗan ajinsu ya soma gaya mata abubuwa game da Allah, kuma ya bayyana mata cewa sunansa Jehobah ne. Jim kaɗan bayan haka, Julia ta soma nazari sau biyu a mako. A kwana a tashi, ta yanke shawarar yin amfani da lokacinta da ƙarfinta wajen bauta wa Jehobah, maimakon ta zama mawaƙiyar da ta ƙware sosai. Yin hakan bai yi mata sauƙi ba. Ta ce: “Mutane da yawa sun gaya min cewa shawarar da na yanke wawanci ne. Amma na fi so in yi amfani da rayuwata in bauta wa Jehobah.” Duk da cewa shekaru 30 sun wuce, yaya take ji game da shawarar da ta yanke? Ta ce: “Ina da kwanciyar hankali, kuma na san cewa Jehobah zai biya dukan bukatuna a nan gaba.”—Zab. 145:16.
Idan bautar Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu, za mu ji daɗin rayuwa sosai (Ka duba sakin layi na 16)c
MU CI GABA DA BAUTA WA JEHOBAH
17. (a) Mene ne waɗanda ba su soma bauta wa Jehobah ba suke bukatar su yi, kuma me ya sa? (b) Mene ne waɗanda suka zaɓi su bauta wa Jehobah suka sani?
17 Muna rayuwa ne kusa da ƙarshen wannan zamanin. Manzo Bulus ya ce: “Gama ba da daɗewa ba, Mai zuwan nan zai zo, ba zai yi latti ba.” (Ibran. 10:37) Ta yaya hakan ya shafe mu? Lokacin da mutane suke da shi na zaɓan ko za su bauta wa Jehobah ya ragu sosai. (1 Kor. 7:29) Idan kuma mun riga mun zaɓi mu bauta wa Jehobah, mun san cewa dole ne mu jimre matsaloli, amma ƙarshensu zai zo nan “ba da daɗewa ba.”
18. Mene ne Jehobah da Yesu suke so mu yi?
18 Yesu ya ƙarfafa mutane su zama almajiransa kuma su ci gaba da zama mabiyansa. (Mat. 16:24) Saboda haka, idan mun daɗe muna bauta wa Jehobah, yanzu ba lokacin da za mu ja da baya ba ne. Wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da bauta wa Jehobah. Ko da yake ba zai zama da sauƙi ba, amma muna da tabbaci cewa za mu yi farin ciki kuma Jehobah zai albarkace mu!—Zab. 35:27.
19. Me muka koya daga labarin Gene?
19 Wasu mutane suna gani kamar idan suna bauta wa Jehobah, ba za su ji daɗin rayuwa ba. Idan kai matashi ne, kana ganin idan ka bauta wa Jehobah ba za ka ji daɗin rayuwa ba? Wani ɗanꞌuwa matashi mai suna Gene ya ce: “Na ji kamar ba zan taɓa jin daɗin rayuwata ba don ni Mashaidin Jehobah ne. Na ga kamar yawancin matasa da muka yi girma tare sukan yi abubuwa kamar, zuwa fati, da naman mata, da buga wasannin bidiyo da ake kashe-kashe. Amma ni kuma daga zuwa taro, sai waꞌazi kawai nake yi.” Ta yaya irin tunanin nan ya shafi Gene? Ya ce: “Na soma yin abubuwa marar kyau da na ga sauran matasan suna yi. Da farko na ɗan ji daɗi kam. Amma daga baya na daina farin ciki. Sai na soma tunani a kan yadda zan amfana idan na bi abin da ke Littafi Mai Tsarki, kuma na yanke shawarar bauta wa Jehobah da dukan zuciyata. Tun daga lokacin, Jehobah yana amsa adduꞌoꞌina.”
20. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi?
20 Wani marubucin zabura ya rera waƙa ga Jehobah, ya ce: “Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa, waɗanda ka jawo su kusa su kasance a filin Gidanka.” (Zab. 65:4) Bari dukanmu mu ƙudura niyyar ci gaba da bauta wa Jehobah. Kuma kamar Joshua mu ma mu ce: “Da ni da gidana, Yahweh ne za mu bauta masa.”—Yosh. 24:15.
WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah
a An canja wasu sunayen.
b BAYANI A KAN HOTUNA: Bayan da wata mata ta ji abin da maƙiyan Shaidun Jehobah suke faɗa a bakin wurin da suke taron yanki, sai ta je wurin da ake waꞌazi da amalanke don ta ji gaskiya.
c BAYANI A KAN HOTO: Ana kwaikwayon yadda Julia ta mai da hankalinta wajen bauta wa Jehobah.