TALIFIN NAZARI NA 31
WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna
Ka Koyi Yadda Za Ka Zama da Gamsuwa?
“Na koyi yadda zan zauna da kwanciyar rai a kowane halin da nake ciki.”—FILIB. 4:11.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu kasance da gamsuwa ta wajen yin godiya, da kasancewa da sauƙin kai, da kuma yin tunani a kan alkawuran Jehobah.
1. Mene ne gamsuwa take nufi, kuma mene ne ba ta nufi?
KANA gamsuwa da abin da kake da shi? Waɗanda suke gamsuwa da abin da suke da shi, suna yin hakan ne domin suna godiya don abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi musu. Ba sa fushi don abubuwan da ba su da shi. A sakamakon haka, suna farin ciki kuma suna kasancewa da salama. Amma, kasancewa da gamsuwa ba ya nufin cewa ba za mu damu da abin da yake faruwa a rayuwarmu ba. Alal misali, ba laifi ba ne idan muna marmarin faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah. (Rom. 12:1; 1 Tim. 3:1) Amma, idan mun gamsu da abin da muke da shi, ba za mu daina farin ciki ko da ba mu samu wani aiki da muke marmarin samu ba.
2. Wace illa ce rashin gamsuwa zai iya kawo mana?
2 Rashin gamsuwa zai iya sa mu soma yanke shawarwarin da ba su dace ba. Alal misali, mutane da ba sa gamsuwa da abin da suke da shi, suna yin awoyi da yawa a wurin aiki don su samu kuɗi kuma su sayi wasu abubuwa da wataƙila ba sa bukata. Abin baƙin cikin shi ne, kaɗan daga cikin ꞌyanꞌuwanmu ma sun taɓa satan kuɗi ko wasu abubuwan da suke mammarin samu. Mai yiwuwa sun yi tunani cewa, abin ya kamata ya zama nasu, ko suna bukatarsa nan da nan, ko kuma za su yi amfani da kuɗin, daga baya su biya. Duk da haka, sata, sata ne, kuma ba wanda ba ya ɓata wa Jehobah rai. (K. Mag. 30:9) Wasu sun yi sanyin gwiwa don ba a ba su wani aikin da suke marmarin samu a ikilisiya ba, har hakan ya sa sun daina bauta wa Jehobah gabaki ɗaya. (Gal. 6:9) Me zai iya sa wanda yake bauta wa Jehobah ya yi irin wannan tunanin? Mai yiwuwa, mutumin ya daina gamsuwa da abubuwan da yake da su ne.
3. Wane darasi mai ban ƙarfafa ne za mu iya koya daga Filibiyawa 4:11, 12?
3 Dukanmu za mu iya kasancewa da gamsuwa. Manzo Bulus ya ce, ‘ya koyi yadda zai zauna da kwanciyar rai a kowane halin da yake ciki.’ (Karanta Filibiyawa 4:11, 12.) Ya rubuta waɗannan kalaman a lokacin da yake kurkuku. Duk da haka, bai daina farin ciki ba. Ya koyi yadda zai iya zama da gamsuwa. Idan yana mana wuya mu gamsu da abin da muke da shi, abin da manzo Bulus ya faɗa, da abin da ya faru da shi za su taimaka mana mu gamsu da abin da muke da shi ko da a wane hali muke ciki. Amma, kada mu ɗauka cewa zai yi mana sauƙi mu gamsu da abubuwan da muke da su a kowane lokaci. A maimakon haka, wajibi ne mu koyi yadda za mu zama masu gamsuwa. Ta yaya? Bari mu tattauna halayen da za su iya taimaka mana mu koyi yadda za mu zama masu gamsuwa.
MU RIƘA NUNA GODIYA
4. Me ya sa zama masu godiya zai taimaka mana mu zama masu gamsuwa? (1 Tasalonikawa 5:18)
4 Zai yi wa mutumin da yake nuna godiya sauƙi ya zama mai gamsuwa. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:18.) Idan muna godiya don abubuwan da muke da su, ba za mu yi tunani sosai a kan abubuwan da muke so, amma ba mu da su ba. Idan muna nuna godiya a kan aikin da muke yi a ikilisiya yanzu, za mu mai da hankali a kan yadda za mu yi aikin da ƙwazo sosai, maimakon mu riƙa yawan tunani a kan wanda muke so da ba a ba mu ba. Jehobah ya san yana da muhimmanci mu zama masu godiya. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi masa godiya saꞌad da muke adduꞌa! Idan mu masu godiya ne, za mu sami “salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.”—Filib. 4:6, 7.
5. Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya tanadar wa Israꞌilawa da ya kamata su yi godiya a kai? (Ka kuma duba hoton.)
5 Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da Israꞌilawa. Sun yi ta yin gunaguni don ba su samu abincin da suka saba ci a ƙasar Masar ba. (L. Ƙid. 11:4-6) Gaskiyar ita ce, rayuwarsu a dajin bai da sauƙi. Amma mene ne ya kamata su yi don su zama masu gamsuwa? Ya kamata su gode wa Jehobah don dukan abubuwa masu kyau da ya riga ya yi musu. Ya kamata su tuna cewa, lokacin da ake wulaƙanta su a ƙasar Masar, Jehobah ya kawo annoba goma a kan Masarawa kuma ya cece su. Bayan da Israꞌilawa suka sami ꞌyanci, sun “kwashi arzikin Masarawa” wato, azurfa, da zinariya, da kuma riguna. (Fit. 12:35, 36) Da Masarawa suka bi Israꞌilawa zuwa Jar Teku, Jehobah ya yi abin ban mamaki ta wajen raba tekun kashi biyu. Kuma saꞌad da suke daji, ya yi ta yi musu tanadin manna kowace rana. To, me ya sa Israꞌilawan suke gunaguni a kan abincin da Jehobah ya tanada musu? Domin ba su gamsu da abin da suke da shi ba. Duk da cewa suna da isasshen abincin da suke bukata, ba su nuna godiya don abubuwan da Jehobah ya yi musu ba.
Me ya sa Israꞌilawa ba su gamsu da abin da suke da shi ba? (Ka duba sakin layi na 5)
6. Ta yaya za mu zama masu godiya?
6 Ta yaya za mu zama masu godiya? Hanya ɗaya ita ce, neman zarafi kowace rana don yin tunani a kan abubuwan da muke jin daɗinsu a rayuwa. Kuma za mu iya rubuta biyu ko uku daga cikin abubuwan da muke so mu yi godiya a kai. (Mak. 3:22, 23) Na biyu, mu riƙa gode wa mutanen da suka yi mana alheri. Mafi muhimmanci kuma, mu gode wa Jehobah kowace rana. (Zab. 75:1) Na uku, mu zaɓi abokan da suke nuna godiya. Idan abokanmu ba sa nuna godiya, mu ma za mu iya zama marasa godiya. Amma idan abokanmu masu nuna godiya ne, halinsu mai kyau zai sa mu yi hakan. (M. Sha. 1:26-28; 2 Tim. 3:1, 2, 5) Idan muna neman zarafi kowane lokaci don mu yi godiya, hakan zai sa mu rage damuwa a kan abubuwan da ba sa tafiya sumul, da kuma abubuwan da muke so amma ba mu da su.
7. Mene ne ya taimaka wa Aci ta zama mai gamsuwa?
7 Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da Aci da take zama a ƙasar Indonesiya. Ta ce: “A lokacin annobar korona, na soma gwada yanayi na da na wasu ꞌyanꞌuwa. Hakan ya sa ban gamsu da abin da nake da shi ba.” (Gal. 6:4) Mene ne ya taimaka mata ta canja yadda take tunani? Ta ce, “Na soma tunani a kan abubuwa masu kyau da Jehobah yake ba ni kowace rana. Ƙari ga haka, na soma tunani a kan abubuwa masu kyau da nake samuwa domin ina ƙungiyar Jehobah. Sai na gode wa Jehobah domin dukan abubuwan nan. Hakan ya sa na zama mai gamsuwa.” Idan ba ma farin ciki domin yanayin da muke ciki, za mu iya yin abin da Aci ta yi.
MU ZAMA MASU SAUƘIN KAI
8. Mene ne ya faru da Baruch?
8 Akwai lokacin da sakataren annabi Irmiya mai suna Baruch, ya daina gamsuwa da abin da yake da shi domin yanayin da yake ciki. Aikinsa mai wuya ne. Kuma shi yake taimaka wa Irmiya su gaya wa Israꞌilawa marasa godiya abin da zai faru da su idan sun ci gaba da yi wa Jehobah rashin biyayya. Amma, maimakon ya mai da hankali a kan abin da Jehobah yake so ya yi, Baruch ya soma tunani sosai a kan abin da zai amfane shi kawai. Jehobah ya sa Irmiya ya gaya masa cewa: “Kana neman wa kanka manyan abubuwa ne? Kada ka neme su.” (Irm. 45:3-5) Abin da Jehobah yake ƙoƙarin ya gaya wa Baruch shi ne, “ya gamsu da abin da yake da shi, duk da yanayin da yake ciki.” Baruch ya saurari abin da Jehobah ya ce, kuma ya ci gaba da zama abokinsa na kud da kud.
9. Wane darasi ne muka koya daga 1 Korintiyawa 4:6, 7? (Ka kuma duba hotunan.)
9 A wasu lokuta, wani ɗanꞌuwa zai iya gani kamar ya kamata a ba shi damar yin wani aiki a ikilisiya. Zai iya yin wannan tunanin domin yana ganin yana da baiwa iri-iri, ko yana da ƙwazo, ko kuma ya yi shekaru yana bauta wa Jehobah. Mai yiwuwa, an ba wa wani wannan damar da yana ganin ya kamata a ba shi. Me zai taimaka masa kada ya yi fushi? Zai iya yin tunani a kan abin da manzo Bulus ya ce a 1 Korintiyawa 4:6, 7. (Karanta.) Duk wata damar da muka samu a ƙungiyar Jehobah, ko kuma muna da wata baiwa, Jehobah ne ya ba mu. Kuma ya ba mu ne ba don mun fi wasu ba, amma don yawan ƙauna da alherinsa ne.—Rom. 12:3, 6; Afis. 2:8, 9.
Jehobah ne ya ba mu duk wata baiwar da muke da ita (Ka duba sakin layi na 9)b
10. Ta yaya za mu zama masu sauƙin kai?
10 Za mu iya zama masu sauƙin kai idan muna tunani mai zurfi a kan irin misalin da Yesu ya kafa mana. Bari mu yi laꞌakari da abin da ya faru a daren da Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa. Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Yesu kuma ya san cewa Uban ya sa dukan kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma,” sai “ya fara wanke ƙafafun almajiran.” (Yoh. 13:3-5) Yesu zai iya ganin kamar, su ne ya kamata su wanke ƙafafunsa. Amma bai yi hakan ba. Bai ga kamar ya kamata ya zauna a gida mai kyau, ko ya zama mai arziki, ko kuma ya zama da abubuwan more rayuwa don shi ɗan Allah ne ba. (Luk. 9:58) Yesu mai sauƙin kai ne, kuma ya gamsu da abin da yake da shi. Ya bar mana misali mai kyau da za mu bi.—Yoh. 13:15.
11. Mene ne ya taimaka wa Dennis ya zama mai gamsuwa?
11 Wani Ɗanꞌuwa mai suna Dennis da ke zama a ƙasar Nezalan ya yi ƙoƙari ya kasance da sauƙin kai kamar Yesu, amma hakan bai yi masa sauƙi ba. Ya ce: “A wasu lokuta idan na ga wani ya sami damar yin aikin da nake so a ikilisiya, nakan yi fushi sosai. Sai in ga kamar ni ne ya kamata a ba wa aikin. Idan hakan ya faru, nakan yi nazari a kan batun sauƙin kai. Na maka wasu nassosi a manhajar JW Library® game da sauƙin kai don in iya samun su da sauƙi kuma in karanta su. Na kuma sauƙar da wasu jawabai a wayata don in riƙa saurarar su.a Na gane cewa duk wani aikin da muke yi, muna yin sa ne don mu ɗaukaka Jehobah, ba kanmu ba. Jehobah ya ba kowannenmu aikin yi, kuma shi ne yake sa mu yi nasara.” Idan ka soma yin baƙin ciki don ba ka sami aikin da kake so a ikilisiya ba, ka yi ƙoƙari ka daɗa kasancewa da sauƙin kai. Yin hakan zai ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, kuma zai sa ka zama mai gamsuwa.—Yak. 4:6, 8.
MU YI TUNANI A KAN ALKAWURAN JEHOBAH
12. Waɗanne alkawura ne Jehobah ya yi mana da za su taimaka mana mu zama masu gamsuwa? (Ishaya 65:21-25)
12 Za mu zama masu gamsuwa idan muna tunani sosai a kan alkawuran da Jehobah ya yi mana. A littafin Ishaya, Jehobah ya ce ya fahimci yadda muke fama da matsaloli, kuma ya yi alkawari cewa zai kawar da dukan matsalolin. (Karanta Ishaya 65:21-25.) Za mu kasance da gidaje masu kyau, da ayyukan yi, da kuma abinci masu gina jiki masu daɗi sosai. Ba za mu kasance da tsoro cewa wani mugun abu zai same mu ko yaranmu ba. (Isha. 32:17, 18; Ezek. 34:25) Muna da tabbaci cewa nan ba daɗewa ba, alkawuran nan za su cika.
13. Waɗanne irin yanayoyi ne muke fama da su a yau, kuma ta yaya yin tunani a kan begenmu zai taimaka mana?
13 Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tunani a kan alkawuran da Jehobah ya yi mana? Domin muna rayuwa ne a “kwanakin ƙarshe” kuma dukanmu muna da matsalolin da suke ci mana tuwo a ƙwarya. (2 Tim. 3:1) A kullum Jehobah yana taimaka mana mu jimre ta wajen, ba mu ƙarfi, da shawarwari, kuma yana tallafa mana. (Zab. 145:14) Ƙari ga haka, begenmu zai iya taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli. Wataƙila kana shan wuya sosai kafin ka iya biyan bukatun iyalinka. Hakan yana nufin cewa za ka ci gaba da zama talaka ne? Sam! Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu dukan abin da muke bukata har ma da ƙari a aljanna. (Zab. 9:18; 72:12-14) Ƙila kana fama da wata cuta ko baƙin ciki mai tsanani, ko kuma jikinka yana maka ciwo-ciwo kowace rana. Shin, haka za ka ci gaba da fama har abada, ba tare da samun sauƙi ba? Aꞌa. Cututtuka da mutuwa ba za su ƙara kasancewa ba. (R. Yar. 21:3, 4) Begen da muke da shi ne zai taimaka mana kada mu yi fushi don abubuwan da muke fama da su a yanzu. Ko da ana wulaƙanta mu, ko wani namu ya rasu, ko kuma wani abu marar kyau ya faru da mu, za mu iya kasancewa da farin ciki da kuma salama. Me ya sa? Domin mun san cewa “wannan ꞌyar wahalar da muke sha ba za ta daɗe ba,” kuma a sabuwar duniya ba za mu sake shan wahala ba har abada.—2 Kor. 4:17, 18.
14. Ta yaya za mu ƙarfafa begenmu?
14 Da yake begenmu yana taimaka mana mu kasance da gamsuwa, mene ne zai sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuransa? Abin da zai taimaka mana shi ne, mu riƙa gani kamar muna aljanna. Idan muna damuwa don ba ma samun isashen kuɗin da za mu biya bukatunmu, za mu iya yin tunani a kan yadda rayuwa za ta kasance a lokacin da ba za mu bukaci kuɗi ba, kuma babu matalauta. Idan kuma muna baƙin ciki don ba mu sami damar yin wani aiki a ikilisiya ba, za mu iya yin tunani a kan irin daɗin da za mu ji a aljanna inda babu zunubi. Wannan shi ne abin da ya fi muhimmanci, ba aikin da muke yi a yanzu ba. Ban da haka ma, za mu yi dubban shekaru muna yi wa Jehobah hidima. (1 Tim. 6:19) Akwai abubuwa da yawa da suke damunmu yanzu, shi ya sa zai yi mana wuya mu yi tunani a kan alkawuran da Jehobah ya yi mana. Amma, idan mun nace da yin tunani a kan abubuwa masu kyau da za mu mora a nan gaba, zai yi mana sauƙi mu mai da hankali a kansu, a maimakon matsalolin da muke fuskanta.
15. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Christa?
15 Za mu iya koyan darasi daga labarin Christa matar Dennis da muka ambata ɗazu. Ta ce: “Ina fama da wata cutar da take kashe min jiki sosai, ba na iya tafiya, ina amfani da keken guragu ne. Kuma a yawancin lokuta, a kwance nake a kan gado. Jikina gaba ɗaya yana min ciwo kullum. Kuma bai daɗe ba da likitana ya gaya min cewa zai yi wuya in sami sauƙi. A tāke sai na yi tunani cewa, ‘Bai san begen da nake da shi ba ne.’ Begen da nake da shi yana sa in sami kwanciyar hankali. A yau, ina jimrewa ne da azaba, amma a sabuwar duniya zan ji daɗin rayuwa sosai!”
“MASU TSORONSA BA SA RASA KOME”
16. Me ya sa Dauda ya rubuta cewa masu tsoron Jehobah “ba sa rasa kome”?
16 Ko da muna gamsuwa da abin da muke da shi, mukan yi fama da matsaloli. Ka yi laꞌakari da yanayin Sarki Dauda. Aƙalla, ya rasa yaransa guda uku. Wasu sun zarge shi da yin abubuwa marasa kyau, abokansa sun ci amanarsa, wani sarki ya yi shekaru yana ta neman sa don ya kashe shi. Duk da matsalolin da Dauda ya fuskanta, shi mai gamsuwa ne. Shi ya sa ya ce: “Masu tsoron [Jehobah] ba sa rasa kome.” (Zab. 34:9, 10) Me ya sa ya faɗi hakan? Ya faɗi hakan ne domin ya san cewa, ko da yake Jehobah ba ya hana matsaloli faruwa a duniya, zai tanadar wa bayinsa duk abin da suke bukata. (Zab. 145:16) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu jimre duk wata matsalar da muke fuskanta. A gaskiya, za mu iya zama masu gamsuwa da abin da muke da shi.
17. Me ya sa muke so mu zama masu gamsuwa?
17 Jehobah yana so mu zama masu gamsuwa. (Zab. 131:1, 2) Don haka, mu yi ƙoƙari mu zama masu gamsuwa. Idan mun zama masu godiya, mun kasance da sauƙin kai, kuma muna tunani a kan alkawuran Jehobah, hakan zai sa mu zama masu gamsuwa.
WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”
a Alal misali, ka kalli bidiyoyin nan Jehobah Yana Kula da Masu Saukin kai da kuma Girman Kai Yakan Kai ga Halaka a jw.org/ha.
b BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana gyare-gyare, ana ganawa da wata ꞌyarꞌuwa da ta koyi yaren kurame a taron daꞌira, wani ɗanꞌuwa yana ba da jawabi ga jamaꞌa.