SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Yadda Za Ka Amfana Daga Rubutun da Ke Tsakiya
A juyin New World Translation of the Holy Scriptures na Turanci, an nuna inda za ka iya samun wasu Nassosin da suke ɗauke da ƙarin bayanai a kan wata aya da kake karantawa. Waɗannan bayyanen sun nuna cewa, ayoyin Littafi Mai Tsarki dabam-dabam sun jitu da juna. Idan kana so ka sami ƙarin bayyanen nan, ka duba haruffan da aka rubuta bayan wata kalma ko jimla. Idan kana amfani da juyin New World Translation da aka buga, za ka ga layi guda biyu da aka ja a tsakiyar littafin, wato Marginal References. A ciki, ka nemi haruffan da ya yi daidai da wanda ke bayan wata kalma ko jimla da ke ayar da kake karantawa. A jw.org ko kuma a manhajar JW Library,® ka danna haruffan da ke bayan kalmar ko jimlar.
Ayoyin da za ka gani a wurin suna ɗauke da abubuwan da aka ambata a gaba da dai sauransu:
Nassosin da suka yi kama: Wannan Nassin zai nuna maka wani Nassi dabam da ke ɗauke da labari iri ɗaya da wanda kake karantawa. Alal misali, ka duba 2 Samaꞌila 24:1 da 1 Tarihi 21:1.
Nassin da aka yi ƙaulin sa: Wannan Nassin zai nuna maka inda aka yi ƙauli, ko kuma inda aka ɗauko wani furuci da ke ayar da kake karantawa. Alal misali, ka duba Matiyu 4:4 da Maimaitawar Shariꞌa 8:3.
Cikar annabcin: Wannan Nassin zai nuna maka wani annabcin da aka yi, ko inda annabcin da aka yi a ayar da kake karantawa ya cika. Alal misali, ka duba Matiyu 21:5 da Zakariya 9:9.